Tuesday, 12 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 23 "Ya'Marwan open the door please" tayi magana kaman tana kuka. Shiru yayi be kulata ba ta kuma kiran sunanshi a hankali "Ya'Marwan" still no respond ta dade a tsaye tana kiran sunanshi amma yaki amsawa kuma yana jikin kofan yana sauraronta. Daga baya ta wuce taje ta kwanta. Mikewa yayi ya shiga toilet yayo alwala ya shinfida dadduma ya fara gabatar da nafila cus ya gane shine kawai me sakashi natsuwa,shine kawai ke sashi mantawa da matsalolinshi,shine kawai ke bashi kwanciyan hankali kuma seyaji kaman yana kusa dasu Mammi, kaman sunajinshi a lokacin *** Ummu ce ta sauko kasa tana kiran sunan Maid din gidan. Amsawa tayi tazo ta durkusa a gabanta. "Samomin ruwa da tsinma" "Yes Ma'am" ta mike ta nufa kitchen Itama Ummu seta nufa parlo inda vase nata yake kawai setaga bashi bane a wajan na wajan stairs ne. Juyawa tayi ta kalla gun stairs din da sauri babu komai a wajan. "Jameelarh!! Jameelarh!!" Ta fara kwallawa maid din kira. "Yes Ma'am" tazo da sauri ta kuma durkusawa. "Were is my mothers flower vase?" Tayi magana har muryanta rawa yakeyi alaman ba karamin so takema Vase din nan ba. Durkusar da kanta kasa tayi "Ma'am i think you should talk to..." se tayi shiru ta kasa magana jikinta na rawa dan ta san halin Meelarh zata iya kuranta a yau din nan. Da Ummu ta gane wanda take nufi seta wuce tabar Maid din a durkushe. "Khameelarh!! Khameelarh!!" Ummu ke kwalla mata kira  sannanta fara hawa staircase din. Khameelarh kam tana dakinta a kan study table nata tana designing wani takalmi kawai taji Ummu na kiranta da 'Khameelarh' dumm! Gabanta ya fara fadi "Busted!" Ta gaya tana zare ido kuma ta kasa amsawa. "Khameelarh!" Ummu ta kuma kiranta da full name nata abunda batayi se idan tayi laifi. Mikewa tayi a guje ta nufa bathroom ta kulle kofa, se kuma ta fito ta shiga closet nata shima fitowa tayi. Balcony ta fita tana neman inda zata sauka ta gudu se taga babu hanya ta kuma dawowa. Ta haye gado ta fara baccin karya. Shima taga baze yuwu ba mikewa ta kuma yi ta sake shiga closet dinta ta fara hada kayanta wai zata gudu. Se Ummu ta banko kofa ta shigo se jikin Khameelarh ya fara rawa ta mike a guje cikin inda kayanta yake ta shiga ta durkusa kaman barawo tana wani zare ido. "Khameelarh!" Ta kuka kiranta. Seta nufa study table nata ta hango drawing din seta juyo ta nufa toilet tana kiran sunanta tana kuma knocking shima shiru seta leka balcony cus the door was open. Babu Khameelarh shima seta shiga closet nata, idonta ne yakai kayan data fara hadawa wajan zata gudu dashi. Karasawa gun kayan tayi seta kuma cewa "Khameelarh!" Shiru kaman ta sani seta nufa inda kayanta yake ta bude kofan a hankali tana matsar da kayan dayake a jikin hangers suke kawai se taga Khameelarh a kasa wai ita ta boye. "Are you serious? Kinajina ma kenan kika boye? Wait. Kinsan abunda kikayi kenan?" Fitowa Khameelarh tayi daga wajan kawai seta fashe da kuka "Ummu wlh it wasn't my fault!" "Then who's fault was it?" Ta tambayeta tana folding hannunta "Me. No El_Armeen" ta gyara da sauri "El_Armeen" Ummu ta tambayeta tana daga giranta daya sama. "Yes. You see lokacin kun kusa dawowa koh? Ina zaune a parlo dayake kullum yana zuwa yana keeping dina company, so se ina zaune akan kujera" and then she paused se ta sha majina kaman dagaske seta cigaba "To bansan yazo ba kawai seya ban tsoro ta baya na, na mike zan gudu kawai se na buje vase din ya tarwatse and mun kasa guming nashi" durkusawa tayi a kasa ta rike kafan Ummu "Ummu my baby my presious mother my one and only Ummu dan Allah kiyi hakuri kinji a promise to do the chores for a whole wee... day" kaman abun arziki. "Hadda wasan banza kuke da El_Armeen?" Zare ido Khameelarh tayi "Wlh a'a kima tambaya maids din gidan bana wasa dashi wlh ranan ne kawai ya ban tsoro shikenan" "Yanxin tashi! You know how important that vase was to me right?" "Yes" tayi magana a hankali tayi wani poppy face irin she's sorry aji tausayinta "It was your mothers" she added looking truely guilty "Good..." se tayi shiru se hawaye ya fara zubu mata "And you know how i love that vase it was the only thing she left" ta karashe magana muryanta yana rawa (Kunsan wasu idan sunada ciki they get really emotional) Kallonta Khameelarh tayi sosai "Ummu are you crying?" "No am not" tana share hawayan "Ummu am really so sorry" "Shikenan" ta fada tana san fita daga dakin Shan gabanta Khameelarh tayi "Ummu seriously you are pregnant you just won't admit it" '"I am okeyy? And i don't know what am doing" Hannunta ta rike kaman sa'anta "You can do it okey? (Kuji min yarinya) Daga mata kai Ummu tayi kaman wata karamar yarinya (Kunsan me akayi anan? Exchanging akayi. Khameelarh ta kuma Maman and Ummu ta dawo daughter. Lol) "Now you are all messy why not muje s-h-o-p-p-i-n-g?" Tayi spelling dinshi feeling all freaked out and excited "Omi! God. That will really help. But na dade banje shopping ba" "Thats no problem" ta gaya irin ba komai ba alhalin itama tunda take bata taba fita wai shopping ba sede ko online shopping ko kuma a tura maids din mansion din da driver. "Amma tsaya kayancan" se tayi pointing kayan da Khameelarh ta fara hadawa "Me zakiyi dashi" "Just forget it okey?" "Fine. Wait guduwa zakiyi da?" "Ummu!" Tayi ihu "Okeyy!! Okeyy!!" *** Ummu ta saka wata black duguwan riga kwata-kwata be matseta ba kuma be mata yawa ba. Ta daura wata black veil irin babban nan. Khameelarh kuma ta saka wata white duguwan riga da digon blue se blue veil da fari-farin flowers a jiki (So i wanted to post the picture i selected and yaki posting so please kindly check the photo that represent the whole page) Fitowa sukayi after all the selfies and shirme suka shiga wata arninyan black and red Range Rover 2015. Sega bodygyard din Abbu ya nufo su. Khameelarh na hangoshi tace "Ummu sauri ki tada motan mu tafi dan Allah" Juyowa tayi ta kalleta "Ummu kiyi sauri abeg" ta kuma maimaitawa "Meye wai haka?" "Wancan mayan yanxin zece seya rakamu" tayi magana tana pointing dinshi Juyawa tayi taga me take nunawa. Se ta ganshi. Itama sauri ta farayi tana saka sit belt dan batasan ya rakasu yayi kusa dasu sosai dayake Ummu ta rugada ta kunna motan kawai se Khameelarh ta tura giya. Se Ummu ta taka motan ya fara tafiya da karfi ta fuzga motan ya fara gudu. Se suka saki dariya da sukaga guard din ya tsaya suka nufa gun gate. Guard din kowa daya tsaya a hankali ya taba abun kunnenshi yace "Don't open the gate" Yake gayan ma security din Daga mai kai kawai yayi dan suna kallon juna Horn din motan suka ringa danna ma scurity ya bude gate amma ya tsaya yana kallon. Khameelarh ta saka hannunta akan abun taki cirewa kara kawai yakeyi. Ummu ta saka hannu a kunne se dariya suke. Guard din ya karasu gun yayi knocking window gefan Ummu suka tsoarat baki daga suka kalla gun "F*ck" sukace a tare da suka ganshi. Hannunta saka ta bude mai window seta juya tana kallon streaght "Ma'am you know you are not suppose to go out by yourself after what happened" Ya gaya in an respective tone. Shiru tayi bata kulashi ba dukda tasan gaskiyanshi. Khameelarh kam se hararanshi takeyi ya lura amma seya basar kawai dan zaman lafiya. Magana ya kumayi da abun kunneshi seyace "Can i?" Yana alaman bude kofan "No!!" Khameelarh ta fada da karfi, begeta Ummu tayi seta daga mai kai bude kofan yayi ta fito. Wani security yazo ya budema Khameelarh nata itama ta fito suka bude masu baya duk suka shiga. Suna hada ido da guard din Khameelarh ta mashi dakuwa shi kuwa murmushi yayi mata kawai ta kuma sakar mai harara. *** Range Rovers ne guda bakwai suka gero duk bakake sena tsakiya ne wanda su Ummu ke ciki Red and black Guard dinne ke driving nasu duk motocin sunsha tint. Selfies din hauka suka ringayi. Tayi posting a insta tace Mother and daughter day. Wata mool suka isa Ummu da Khameelarh duk suka saka shades dinsu suka fito daga motan already paparazzi suna giransu ko saboda posting dinda tayinne suka duba location din oho! Guards 5 suka fito suka kare mutanan wajan harsu Ummu suka iya shiga. Guards biyu suka tsaya waje bayan wanda ke cikin motan se uku suka shiga cikin mool din suna binsu a baya. Manager mool din yana ganin wanda suka shigo ciki ya saka a kura mutanan wajan (Idan mutum beda wani matsayi se ata wulakantashi. Allah ka azurtamu. Amiiiin ooo). Ummu data lura da abunda akeyi ma mutane a wajan se ta saka baki tace ya kyalesu mana mutumin yaki Tace idan kuwa be kyalesu ba suma zasu bar mashi mool dinshi. Da haka ya kyalesu wasu masu zuciya suka bar wajan baki daya wasu kuma wanda basusan mutuncin kansu ba suka tsaya. Guards biyu suka dauko masu basket guda biyu suna binsu 'side to side' (Ariana grande ft. Nicki Minaj) Dayan guard din Abbu kowa yana biye dasu a baya. Khameelarh kowa rabin hankalinta yana kan wayanta ta dago kanta taga wanda ke binta da basket dinta se taga wani daban juyawa tayi tana duban wancan Guard din se ta ganshi yana biye dasu kawai a baya. Wani evil smirk ta saki tace ma wanda ke binta da naya basket din "Ni bakai nakeso ba wancan nakeso" tayi magana kaman da shagwaba tana nuna Guard din Abbu. Kallon juna suka farayi. Ummu tace "Meelarh wancan is not like a normal gaurd shi..." "No Ma'am karki damu duk abunda yaro keso shi ake bashi" Yayi magana yana amsan basket din yana mata wani murmushi "What the f*ck! Nice yarinyan?" "Meelarh shut up will you?" Ummu tayi mata magana. "Amma Ummu kinji abunda yace min" kaman zatayi kuka tayi magana "Ke kika saya da kudinki tunda kikace shi kikeson ya amsan maki" shiru tayi tana kunbura fuska kaman zata fashe. *** Shirme suka ringayi a mool din nan kaman ba gobe kuma tayima Guard din Abbu me suna Aleeyu wukanci kaman ba gobe. Se taga abu tace shi takeso idan ya dauko se tace na can sama takeso haka ze dauka ladder yahau ya dauko mata seta amsa ta kalla seta yamutsa fuska tace "Ya tsufa" ta gaya abun nan yafi dau 10 shi kuma seya amsa ya maida. Sunyi siyayya sosai ga haukan da suka ringayi a mool din nan mutanan wajan se daukan hotonan su sukeyi. Wata Baby Ummu ta gani a hannun wata mata Baby girl gata kyakkyawa ta kalla Khameelarh "Meelarh kalla Baby nan" Meelarh da a rayuwanta zata iya kirga daukan Baby da tayi. Seda ta amsa Baby nan ta ringa yawo da ita a wajan dukda bata iya rikewa sosai ba ta ringa daukansu hotona kowa. Maman Baby baki har kunne ana son Baby. "Who's a good girl? Who's a cute baby? Ohh. Yes you are. Yes you are" Khameelarh ce da Baby ita kowa yarinya se dariya takeyi. Check book Ummu ta ciro ta rubutama Matan check din 20,000 ta bata wai ta sayan ma Baby diapers se godiya take. Khameelarh kaman karta bata yarinyan taji itama Baby seda tayi ihu. Sunfi 3hrs a mool din nan se shirme sukeyi Ummu kowa ta bada kyautan kudi yafi 70,000. Daga bisani suka nufa inda ake biyan kudin shima nan sun dade ana shirme suka biya kudin aka kai masu kayan har mota suka shiga. Aleeyu kowa wato personal guard din Abbu yasha dakuwa a wajan Khameelarh yafi sau goma shi kuma seya basar. (Yarinta) A news kowa ko ina se labarin abun ake da kyautan da Ummu tayi. --Two weeks later-- R ayuwa ta kuma daidai a Lawiza family kowa ya kuma bakin aikinshi Khameelarh itama ta kuma makaranta itada El_Armeen dan shima tunda ta bari be kuma zuwa ba se suka kuma tare everything was back to normal for this family. Abbu kowa jiki yayi daidai babu wata matsala. Amma su Vice president (sunan daya tsana kenan) kullum sake planing yadda ze hallaka President yake. Abbu bawan Allah shi kowa ya yarda dashi tsakani da Allah be taba kawo negetive thought a zuciyanshi ba. *** Momy El_Armeen se ramewa take yaronta ya tambayeta meke damunta taki gayan mai ita abun duniya duk yabi ya isheta gashi sonda take mai bazata iya rabuwa dashi ba. Wani sa'in ma be kwana a gida yana wajan karuwanshi (Kugi tsohon banza). ♥♥♥

Share:

Saturday, 9 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 22 Sake rikota yayi ta kuma fizgewa da karfi ta cigaba da kukanta. "Manal am sorry okey?" Tayi banza dashi tana rike da cikinta har'a lokacin be dena mata radadi ba besan sanda ya rungumota ba seta kasa kwacewa tayi lamo a jikinshi tana cigaba da kukanta. "Am very sorry" He apologized again. "I had no idea" He added. "I just want my brother back" Ta furta a hankali *** --The nxt day-- Ranan ya kaman ran saturday karfe 6am Khameelarh tana dakinta tana daura wani jacket a waist nata se aka fara knockimg kofanta. Budewa tayi se taga Abbu tsaye da kayan sport a jikinshi kallonshi ta tsayayi na kusan 10secs se kawai ta tuntsire da wata dariya hadda rike ciki se dariya take mai. "You can laugh whatever you want i knw i look hurt" ya gaya yana gyara rigan jikinshi yana wani feeling kanshi. Sake tuntsewa da dariya tayi. "Ummu tasan kasa kayan nan kuwa?" She asked in between laughter. "A mana ta sani. Ni yanxin ma morning exceise zani na dade banje ba" "Kaidawa zaka?" "Dake mana" he answerd immidiately "Dabani ba wlh. Ka sume min a hanya na rasa inda zanyi dakai" tayi magana cikin zulaya "Amma kin rainani seriously" yayi magana yana juyawa. Da sauri ta fito daga dakin "Am joking okey? But seka cema guards dinka bazasu bimu ba dan asali saboda su na dena zuwa" "Naji" Kumawa dakin tayi ta dauko wayanta da earpiece ta saka suka sauko kasa. Guards din se gaidashu suke yana amsawa da fara'a a fuskanshi Har sunzo kofa zasu fita se wasu guards kusan biyar suna biye a bayansu. Juyawa yayi ya kallesu. "No kuyi zamanku" "Your Excellency am so sorry but i can't do that" Wannan bodyguard dinshi da always yana gaban mota idan zasu fita yake tare dashi yayi magana. Alama yayi mashi dakai dayazo. "Abbu" Khameelarh ta kira sunanshi da shagwaba. "Meelarh he is morethan a guard to me babu komai idan munje dashi" "I don't even exist" Personal Guard din Abbu added. Murmushi Abbu yayi ita kuwa Khameelarh sakarmai harara tayi seya mata murmushi a haka suka fito suna tafiya kawai suna hira. Sunkai har karshen layin kowa se daga masu hannu ake banda masu karasowa suna gaidashi har kasa shi kowa seya kai masu hannu su gaisa. Abun harya fara ba Khameelarh haushi. Dawowa sukayi Guard din yanacan baya yana biye dasu a baya da black shades dinshi da suit su kowa se hiransu suke. Khameelarh tayi masu selfie yafi 20 tun a lokacin tayi adding a story ta na Snapchat tayi posting kuma a Insta. "Abbu. Ummu ta gayan maka? Khameelarh ta tambayeshi tana cire earpiece din kunnenta. "Ta gayan min mene" ya tambaya kaman besan me take nufi ba. "Tana da ciki mana. You are acting as if you have no idea what am talking about" Seda yayi murmushi sannan yace "She is" Da sauri ta riko hannunshi tana zare ido "Da gaske?" "A mana" "God! Am freaking happy. Nima zan sama baby sister in ringa gyara mata gashi da pulishing nails nata" tayi magana kaman tana dreaming "Har kin san mace ce?" Ya katseta yana mata murmushi. "Ohh yess! Mace ce ma. But hw many month ne in fara shiri?" "Nima ban sani ba taki yarda na kira doctor. Tsaya wai bakijin kunya ko kadan am your father fah" "Kunyan me......." se kuma kunya yazo mata se tayi murmushi kawai. A haka suka iso gida suna dan hiransu gwanin sha'awa kaman ba Baba da Yarinya ba Suna isowa gida da ruwa aka fara masu sallama tun a gate. Suka shiga ciki gidan. Abbu ya wuce dakinshi itama ta wuce nata. Wanka tayi da saka shorts da tag top tayi ponytail da gashinta seta kuma ta kwanta abunta. *** Marwan yana zaune a bakin gadon Manal tana bata magana ta amsa tasha ya mika mata ruwa a glass cup shima ta amsa tasha seta mika mai a hankali tace "Thank you" Daga mata kai yayi yace "Rest a little ze dina ciwo" yayi magana a hankali gyada mai kai kawai tayi ta kwantar da kanta a kan pillo tana kallon celin din a hankali tace "I missed Abbah da Mammi so much" Dumm!! Kirjinshi ya buga se jikinshi ya fara rawa ya kuma kasa mata magana "I don't wanna imagine our future. I missed them so mch already. Bazan taba yafema wanda ya rabamu dasu ba" ta karashe maganan a hankali hawaye na zubu mata. He can't take it anymore. Kawai seya mike ya fita daga dakin, binshi tayi da kallo kawai. Yana shiga dakinshi buga kofan yayi da karfin gaske kawai seya zauna a jikin kofan yana jingine a jiki ya fashe da wani irin kuka kaman ba namiji ba. He is doing he's best to be strong but he don't think he can do it. Kanshi ya saka cikin gwiwanshi kawai yana cigaba da kukanshi. Allah kana ganin halinda aka sakamu a ciki karfi da yaji. Allah kana ganin abunda aka mana an maidamu marayu karfi da yaji. Allah make me someone so that i can Avenge for my parents death Ya Allah! Don't make them get away with what they did to my parent. Mammi, Abbah life sucks without you guyx! This life is nothing without your parent Allah make me strong so that i can support my sister. Ya Allah ka tayani rike alkawarin danama su Abbah. Hannunshi yabdaga ya kalla inda ya dinke M-card din wajan kawai ya shafa har'a lokacin yana zafi wajan. Hawayan idonshi ya share kawai se yayi wani murmushi I know am stronger than this. Mammi, Abbah am so sorry all this is my fault. It all started frm my mistake am so sorry. Am so sorry Se kawai ya kuma fashewa da wani kukan Mammi i can't do this i need you guyx by my side. I missed everything about you. I missed seeing your smile. I missed kallon fuskanki when you are freaked out about the president. I missed your face idan na gayan maki banada lafiya ko Manal batada lafiya. I want you guyx back. Abbah am trying to be the strong person you made me but i don't think i can make it. Haka ya ringa sambatu shi kadai yanayi yana kuka. Idan ya tuna happy moments they shared with his family se yayi murmushi can kuma seya kuma fashewa da kuka duk kuma yana jikin kofan ta cikin dakin. Can se yaji Manal tana knocking dakin a hankali tana "Ya'Marwan open up please" ***

Share:

Wednesday, 6 September 2017

RASHIN MAHIFA- CHAPTER 21 An kawo gawan driver daya rasu Abbu ya kalla gawan sedaya durkusa yayi mashi addu'a sannan ya saka a kira iyalishi a gayan masu bayan ya saka a tura masu kudade masu dinbin yawa kenan. "Ummu" Khameelarh ta kira sunanta a hankali cus tun sanda suka shigo batayi magana ba. Kallonta tayi idonta cike da hawaye amma batayi magana ba. Karasawa tayi gunta tace "Ummu meyafaru?" Kallonta kawai take se Khameelarh tayi huging dinta itama tayi huging nata back sun dade a haka daga bisani suka rabu. *** Vice president dake kallon abunda yake faruwa live a office nashi ji yayi kaman yayi ihu ya rungumo T.v dan har'an fara rabawa a news cewa president was attacked and an kashesu da first lady. El_Armeen yana ganin abunda akeyi a news dan haka ya dauka wayanshi ya fara masu video sanda ake hugs din nan se kuka Khameelarh take yayi posting a account dinshi na Instagram yayi adding a storyshi na snapchat sannan yayi posting a youtube inless dan 20mins it was brodcast that The President is alife wanda suka fara kuka already seya kuma murna. Vice president da yaga abunda danshi yayi posting he was very shocked ya kira numbershi be dade ba ya daga yake tambayanshi yana ina "Ina gidansu Khameelarh" ya amsa da murna a fuskanshi "And president da first lady are alife?" He asked in a low tone "Yess" ya amsashi a hankali. Kawai se yayi cutting line din. El_Armeen be damu ba ya cigaba da shirman video da yakeyi. Se dadi yakeji kaman Familyshi. --1hr later-- Gidan ya kayaye da hayaniyan mutane yan sannu da zuwa su Hawwatie suma sun iso dukkansu da Babbanta da Mammanta se yan mutanan da ba'a rasa ba abokan arziki. Su Vice President kowa ko lekowa ba'ayi ba. Brother Abbu wato Baban Hawwatiee wannan karan ma seda ya sake kuka na dadi cus shi ya rigada ya cire hope din sake haduwa da danuwanshi se gashi ya dawo. 8pm lokacin kowa ya watse harda El_Armeen shima ya tafi gida suna zaune a dining suna dinner Khameelarh se murmushi take tana kallon fuskokinsu Abbu as usual tana kusa dashi tanacin abinci. Rabonda taci abinci me nauyi tun randa suna lunch Abbu ya fadin nan seyau se murmushi kawai takeyi duk suka lura da ita se Abbu ya saki murmushi shima yace "Kewai meke damunki kaman tababbiya se murmushi kike ke daya" "Am freaking happy you guyx are back safe!" Ta gaya tana daga hannunta sama. Girgiza kai Ummu tayi tana dariya itama tana kallon abincin se jagwal-gwalawa take ko spoon daya ta kasayi. "Ummu abincin babu dadi ne" Khameelarh ta tambaya tana kallonta. Dagowa tayi tace "Banjin cin komai ne idan naci amai zanyi" kaman da shagwaba tayi magana kaman wata yarinya Ajiye spoon din hannunta Khameelarh tayi tana bude baki tace "Omi! God. Are you pregnant!" She asked very surprise and freaking happy. Da sauri Abbu ya dago ya kalleta shima da tambaya a fuskanshi. Vegetables din plate dinda ke gaban Ummu ta dauka ta watsama Khameelarh tace "You silly girl" kare fuskanta tayi "Seriously. Ummu are you pregnant?" Ta kuma tambayanta shide Abbu kallo kawai yake binta dashi. Mikewa tayi tana murmushi tazo tayi pecking Khameelarh tace "Goodnyt" bata jira abunda zatace ba ta haye sama. Juyowa Khameelarh tayi tana kallon Abbu "Abbu seriously is she pregnant?" "Wait. Ho... how will i know?" Ya mike shima ya gudu. Dariya kawai take masu ta maidasu kaman kakanninta ba iyayenta ba. Itama mikewa tayi ta shige dakinta. Abbu na shiga dakinsu ya tarar da Ummu a gaban mirror tana kallon cikinta. Murmushi ya saki sannan ya karasa gunta ya saka hannunshi a waist nata duk suna kallon mirror (basu girma su). Hannunshi ta rike yace "Is it true?" Kallon fuskanshi tayi ta gaban mirror se tace "I think so?" Tayi magana more like tana tambayanshi. Juyo da ita yayi suna kallon fuskan juna yace "Kinyi test ne?" "Nop" Seya saketa ya nufa inda wayanshi yake yace "Lemmi call the doctor yazo ya dubaki. I hope it's true" ya karashe maganan yana wani murmushi. Karasowa tayi gunshi da sauri ta amshe wayan daga hannunshi. "Abeg karka kirashi. Nasan am pregnant all it matter now is watanni nawane" ta karshe maganan kaman dadan kunya. Murmushi yayi se yayi huging nata yanajin dadi. "Allah ya raya mana twins" yayi magana yana shafa cikin. Murmushi tayi tace "Amiiin" a hankali. *** Marwan yana kwance a dakinshi wuraran 9:30pm yana kallon celin din dakinshi wani radadi zuciyanshi keyi kaman ya cire ya ajige a gefe guda. Manal kowa itama tana dakinta tanata kuka cikinta yana mata ciwo daga baya ta mike tana rike da cikin ta nufo dakin Marwan ta fara knocking mai kofanshi. "What!" Ya buga mata tsawa. Batayi magana ba seta bude kofan ta shigo tana kuka tace "Ya'Marwan cikina yana ciwo kaman ze fashe" a hankali take magana tana kuma rike cikin da dukka hannayanta. Ko juyowa ya kalleta beyiba yace "Do i look like i care?" (Omi! God i seriously hate the present Marwan i want our Marwan back) Kallonshi ta tsaya yi da mamaki na kusan 2mins shi bema san tanayi ba kawai seta juya ta hango wani flower vase akan side-drawer wurgi tayi dashi gefe guda seya fadi ya tarwashe ta kuma sakin kuka ta fice a guje dakinta ta kuma ta fada kan gadon ta cigaba da rera kukanta. Da sauri ya dago ya kalle abunda tayi se yaji ta bashi tausayi He knows he is giving her a had time but he don't freaking care 'Amma kasan you are all she got! And you made a promise to your parent you will keep her safe. Then why are you doing this? All that is happing is not her fault. She is affected to it also you know' Wani gefe a zuciyanshi kemai wannan magana shiru kawai yayi. Kukanta kawai takeyi kawai zuciyanta seya fara raya maga wani abu. Mikewa tayi ta nufa gun labulan kofa. Ina irin abun nan da yake rike labule? Tou shi ta zaro dukka biyun na gefan ta dauresu dukka seta dauka kujeran mirror ta ajiye a tsakiya dakin wurin fan. Tahau ta fara kulle igiyan a jikin celin fan din tanayi tana kuka. Kawai se Marwan ya shigo dakin. He was very shock daya gane abunda takeda niyanyi, ita batamasan ya shigo ba se share hawaye takeyi tana kulle igiyan. "Manal!!" Ya kwalla mata kira da karfi. A firgice ta juyo ta kalleshi. Kawai seta kuma fashewa da kuka ta cigaba da abunda take. A zuciye ya nufa inda take da karfin gaske ya fizgota dagakan kujeran ta fadu akan hannunshi ya dauketa da wani wawan mari. Kurma ihu tayi. "Tou ka barni na kashe kaina mana tunda kai ka tsaneni. I regreat living them in the first place. I wish you were the one that is dead. I freaking hate you, mena maka da kakemin haka? I hate you!" Ta durkusa a wajan tana wani irin kuka abun tausayi ga shedan hannunshi a fuskanta. Wani irin tausayinta ne ya kamashi seya durkusa shima ya rungumeta "Am so sorry" ya furta a hankali "Let go of me!!" Ta gaya a tsawace tana janye jikinta daga gunshi. ***

Share:

Monday, 4 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 20 Sorry not sorry- Demi lovato Manal na kwance a dakinta idon nan ya kunbura yayi kato kaman zasu fadu se kuka take. Dashi take kwana dashi take tashi har muryanta ya dashi gashi rana daya kawai ta wani rame Marwan yayi-yayi tace abinci take se kuka kawai takeyi. Shima ba'a barshi a baya ba ku yaushe yana kan sallaya yana mata addu'a yana kuka duk sun rame se hanci da idanuwa daya rage. Wajajan karfe 3pm duk suna dakunansu kowa na kan gado ba bacci suke ba. Manal na sana'arta shi kowa rabi bacci yake rabi kowa idonshi biyu. Yanata tunanin Mammi. Akwai ranan da take bacci a dakin ta yazo wucewa ya hangota seya shiga ya dauko wani cream dinta ya shafa mata a hannu seya dauka tsinken tsintsiya ya shafa mata a kunne seta saka hannun cream din zata bige abunda ke wajan se kawai ta bata fuskanta da cream din ya ringa mata dariya, ita kuwa mikewa tayi da sauri ta rankwashe kanshi ya mike a guje ya bar dakin. Besan sanda wani hawaye ya fara zubu mashi ba kawai seya fashe da wani irin kuka zuciyanshi wani irin abu take mai kawai seya fara ajiyan zuciya a hankali. Kaman cikin mafarki se yaji wani irin kara a parlo a birkice ya mike zaune yana sake jin abun ya tabbatar daga parlo ne a tare suka shiga parlo shida Manal seda suka hada ido dukkansu idonsu yayi jajir. Se suka maida hankalinsu inda suke jin karan. Wajan T.v ne yana kawo red seya dauke. Motsowa Marwan yayi kusa dashi ya taba remote din kawai se fuskan matan ya fito. Kana ganin fuskanta kasan bad news ta kawo masu "Hey Manal. Marwan ya kafanka?" A hankali take magana. Shiru yayi be kulata ba can seya ce "Ina Abbah?" Seda ta kalla Manal sannan ta kalla Marwan a hankali ta fara "Kullu nafsi za'ikatul maut....." Rike kai Manal tayi ta kurma wani uban kara na kusan 50secs se kawai ta saki wani dariya ta zube a wajan. Kafin kace me shima Marwan ya sume! Babu me taimakawo kowa gashi su kadai ne a gidan. Hawaye kawai matan ke zubarwa cus ba karamin tausayinsu takeji ba ace yara dasu su rasa iyayensu dukka a lokaci daya an maidasu marayu karfi da yaji. da sauri ta kashe video call din. Befi 30mins ba se gata tazo har'a lokacin suna sume dukka, tazo itada wannan doctor da Acting president ke aiki dashi wanda ya duba sanda Abbah ya rasu ashe shima aikin su daya da matan da take taimakawa su Marwan wato Secret Agents Of Nigeria (SAON). (I just made it up) suna aiki ne a boye bana Government bane wanda ko President himself be sani ba aikinsu akan mutane da suke neman taimako ne shine suke taimaka masu. A gadon da aka kwantar dasu anan aka maidasu. Doctor ya duba Manal batada wani damage akai cus dariyan da tayi se matan tayi tunanin ta sama matsala ne. Marwan kowa kaman ze tashi se wani nunfashi yake sama-sama kaman za'a cire mai rai (dukda bansan yadda ake ba). Dan haka aka dubashi aka gano ciwon zuciya yanason ya kamashi yama fara kamshi and he is too yoing to have it. Seda aka mai dressing kafanshi sannan ta rubuta mai wani note kusa da gadonshi akan idan ya tashi yasha magongunan data bar mashi a wajan shida Manal sannan suka wuce. Bayan ta masu alluran samun hutu. *** Acting president ke zaune sojojin daya aiki suka dawo suke cemai sun kashe Marwan da Manal tunda shi wawa ne seya yarda harda murnan shi. Wai ya gama da family su shikenan. Abbu yanxin ya samu sauki sosai yana iya tafiya yana komai dakanshi cus jininshi baki daya aka chanja mai in-case idan akwai guban a jikinshi. An yanke masu nan da two days zasu kuma gida amma Ummu tace kar Doctors din su gayan ma kuwa sede kawai a gansu a Abuja. Hatta Khameelarh itama batasan da zancan ba. *** Rayuwansu Marwan ya jagule ya chanza shide ta nashi gefan jira kawai yake mutuwa tazo mashi dan kusan sau uku yana kukarin kashe kanshi Manal na hanashi na farko wuka ya dauka ya daura a hannunshi ze yanka jijiyanshi ta ringa kuka tana ihu wai idan ya mutu ita kadai zata rage haka ya fasa. Rayuwansu de ta kuma wani iri abu kaman a film ya riga ya daukan ma kanshi alkawari se yayi avanging death din iyayenshi koba yanzin bane seyabi duk wanda keda hannu shima ya kasheshi sede shima azo a kasheshi. His heart is now full of darkness, His cute smile is nomore ya tsana kuwa a duniya ya tsana family President cus yana ganin hadda laifinshi. And the very man he will never forget in his life, mutumin daya fara sakashi a halin dayake ciki, mutumin dayayi sanadiyan rabuwansu, mutumin daya kashe iyayenshi. Kullum seya dauka M-card din ya kalla. Hatta Manal bema magana kullum yana cikin dakinshi be damu da halinda take ciki ba. He now don't care about anyone he hate the freaking world he hate all the people that are living in it. T.v dake dakinshi tuni ya fasashi wayan ma tuni ya tarwatsashi. Yanzin haka zaune yake a bakin gadonshi a kasa da scissors a hannunshi ya hudeshi kawai seya daura a hannunshi ya yanka ku alaman jin zafi beyiba. M-card din ya dauko a saka a cikin wani dan karamin abu kaman paper amma ba paper bani kawai seya tura cikin naman hannunshi (O. M. G) allura ya saka ya dinke wajan. Wajan yayi jajir banda jinin dake zuba, idonshi yayi jajir kana kallonshi kasan yanajin zafi. Goge jinin yayi ya zama M-card din yana cikin naman jikinshi kenan (God!). Marwan ya chanja sosai kaman bashi bane idan yaji ciwo Mammi tazo goge mai ake kokowa dashi yana ihu amma shine ke yanka naman jikinshi yau kuma yana nunawa ko a jikinshi. Fuskan nan a murtike kaman bashi bane wanda duk sanda ka daga kanka zakaga yana maka murmushi ko yaushe akwai murmushi dauke a fuskan nan. Gashin nan is a mess kaman bashi bane kullum yake brushing gashinshi sau uku ko biyu a rana. A yanxin be tausayin kowa besan kowa ko matan datake taimaka masu idan ta masu requesting video chat se yayi disconnecting sede idan Manal na wajan ta dauka. Manal kam yanzin tayi tawakkali ta fauwalawa Allah komai. Kullum tana cikin ma iyayenta addu'a, kullum tana masu addu'a baki daya Allah yasa su hadu baki dayansu a cikin gidan Aljanna (Allah sa baki dayan mu mu hadu acan. Amiiiin) Dukda ramewan da tayi kaman wanda ta shekara tana ciwo be hanata boye damuwanta ba saboda Marwan. Cus taga alaman he's more affective than her, ta fara damuwa da yadda Marwan ya kuma tashin farko. Wani sa'in zata girka masu abinci takaimai har daki ko kallonta bayayi se bayan ta fita ze fito da plate din ya ajiye mata akan dining. Rabonda taji muryanshi tun randa yace 'Ina Abbah' Randa matan nan ta kirasu kenan take gayan masu shima Abbah ya rasu. Tou tun ranan bata sake jin muryanshi ba. Kota mai magana sede ya bita da ido kawai ya kuma so silent ko abinci bayaci. Haka zata shiga daki tayi kuka-tayi kuka se tanajin mutuwan iyayenta yazo mata sabo tal. RASHIN MAHAIFA sucks! Kullum abunda take fada kenan. Gashi an kullesu a gida babu daman fita kuma babu waya. T.v ne kawai abokin hiranta ita kam. Babu ranan da baxatayi kuka ba, babu shi. Ya rigada ya zaman mata jiki, tayi sau uku sau hudu a rana se taji dadi a ranta. A duk lokacin da tayi wani abu daze tuna mata da Abbah da Mammi ana wajan zata kwanta tayita kuka harse ta gaji dan kanta ta tashi cus babu me bata hakuri. Gashi matan nan bata taba zuwa su hadu ba! *** Yau karfe 2pm Allah ya saukar dasu Abbu a Nigeria. Suna sauka Airport din were very surprised da suka ganshi. Benx guda goma aka kawo masu suka shiga dayake an saba nashi yana tsakiya yau se Ummu tace su shiga muta na biyu cus babu wanda zeyi tsammanin yana ciki! Acting president yana zaune se wani ya kirashi yake gayan mai Presisent ya dawo. Kafin yayi magana se yaga ana nunawa a news. Wani irin wulli yayi da wayan hannunshi ta tarwatse, ya zubar da dukka takardun table nashi mikewa yayi ya nufa wajan T.v shi, kujera ya dauka irin me karfe a wajan kafan nan kawai ya buga a babban T.v nan yana ihu seya fashe. Ya dade yana hauka shi kadai a office dinshi. P.A shi tana jinshi babu daman ta leko se'a koreta bata shirya rasa aikinta ba shiyasa ta shareshi idan ya gama tasa a gyara wajan. Wani shawara ne yazo mai kawai ya dauka Telephone din office dinshi yayi dailing wani number seya saka a kunne. Befi ringing uku ba aka daga. "Yes. Inason ka saka snipers uku a yanxin nan su tarwatsa min motan da President ke ciki, kasan wanne ne koh? Tou na tsakiyan ne yake zama a ciki. A ta harbinshi harse motan ya kama da wuta one more thing idan aka kamaku if any of you dare to mention my name y'all dead!" yana kaiwa nan ya kashe call din yana ajiyan zuciya kaman zaki se'a lokacin yadan ji dadi a zuciyanshi. *** El_Armeen da Khameelarh as always suna zaune a parlo shi tun sanda su Abbu suka bar garin gidan ya zaman mashi wajan yini wani sa'in se 9pm yake tafiya gida har Mommynshi ta sabama. Kowa na danna wayanshi cus har Khameelarh tayi sabon waya (aikin kudi) se El_Armeen yayi saurin dagowa yace "Ina remote yake?" Ko kallonshi batayi ba tace "Jirani na naimo maka dan rainin hankali kawai" tsaki yaja ya mike ya dauka yakai news ae kowa seyaga motansu Abbu an hada convoy dukka motan baki kuma ko wanne akwai karamin flag din Nigeria a gaban motan. Ihu ya saki yace cewa "His Excellency is back!" Wani irin dagowa Khameelarh tayi ta kalla T.v ta tabbatar motocin Abbu ne wani ihu ta saki itama batasan sanda tayi wulli da wayanta gefe guda ba ta rungume El_Armeen sunata ihu basu ma san sunyi ba. Kawai se Khameelarh ta fashe da kuka, a rude ya rike mata kafadanta ya fara tambayanta "Meyafaru kuma?" Batayi magana ba se hawayen dake kwaranyo mata tanayi tana murmushi "This the happiest day of my freaking life!"  Ta gaya da karfi hawaye na zubuwa amma tana murmushi. Dariya yayi shima ya kuma rungumeta. Haka suka zauna suna kallon yadda motocin ke tafiya a hankali yan garin se ihu ake ana dagama motocin hannu. Samari da yara bin motocin suke aguje suna ihu *** Suna cikin motan Ummu na rike da hannun Abbu se kallon titin suke inda mutane ke kallon motan tsakiyan anata daga mata hannu cus dukkan motocin akwai tint and is very dark so baza asan wanne ne yake ciki ba. Se murmushi kawai sukeyi. Dayake  su hudu ne a motan da suke ciki. Da driver se personal bodyguard din Abbu wanda Abbu ya yarda dashi sosai cus shi sau dayawa idan suna tare da Abbu idan aka kawo mashi hari yana sacrificing kanshi ya daukan ma Abbu bullet shiyasa ya yarda dashi sosai. Ko sanda suke hospital din shinema yake tsayawa a bakin kofan dakin ko yaushe duk wanda ze shiga dakin seya nuna mai ID-card dinshi na doctor kafin ya shiga. Se Ummu da Abbu Wasu snipers uku na hango akan wani building suna labe kowa da bindiganshi suna pointing motan tsakiyan seda gabana ya fadi cus i don't want to witness this moment. Harban motan tsakiyan suka fara ta ko'ina mutanan wajan aka fara tsarwatsewa anata ihu. Salati Ummu da Abbu suka farayi ta sake kankame hannunshi shi kowa yayi saurin dukar da kan Ummu. Dukka motocin suka tsaya wanda ke bayan suka fara juyawa na gaban kuma suna tsaye se Bodyguard din Abbu ya fito. Abbu nata cemai ya dawo amma be saurareshi ba ya kalla driver "Make sure you take them home save!" Yana gaya yana gyara bindiganshi Daga mai kai driver yayi kawai ya tada motan suka fara tafiya yayima na bayan alamana suma su tafi suka fara tafiya shi kowa daga bindiganshi yayi ya seto sniper daya aekowa cikin sa'a ya samoshi. Tuni motan ya faraci da wuta Allah ya taimaka ma mutum dayane a ciki amma ya rigada ya kune. Kafin dayan ya ankara har'an samoshi shima sauran guda daya seya mike ze gudu, bodyguard din ya fara binshi. Khameelarh suna kallon T.v suka fara ganin yadda ake harbin motan da suka tabbatar Abbu na ciki. Mikewa tayi da sauri hannunta a baki gama kasa komai tana tsaye a haka kawai shima El_Armeen ya tsaya yama kasa yin komai kawai yana tsaye. Bodyguard din ya tare sniper dayaga there is noway out kawai seya daga bindigan ya harba akanshi a cikin 2secs da sauri ya karasa gunshi amma har rai yayi halinshi. Chaje jikin sniper Bodyguard din ya farayi dan kuze sama wani abu a ciki. Amma be sama komai ba dan ko ID-card dinshi babu a jikinshi. Hakama sauran babu komai a jikinsu. Tuni an kira taimako harsun iso an fara kashe wutan an dauko gawan driver dukda ya kune anyi gidan President dashi cus ya ganshi. Snipers din kuma an debesu dan ayi bincike ko su waye and waya aikosu. Khameelarh kowa har'a lokacin tana tsaye da hannunta dukka a baki cause bata masan me zatayi ba. Driving din became so quite Ummu was in shock cus tunani take da sune a cikin motan Abbu shima haka. Dukka sauran motoci taran suka isa gidan a tare. Kawai se su Khameelarh sukaji hayaniya a waje ana shigowa da motoci. El_Armeen ne yayi kokarin lekawai kawai ya hango Abbu an bude masu kofa yana rike da hannun Ummu duk ya rame. "Khamee......larh!! Kha....." seya kasa karasawa yanata pointing window kawai. Ita tama kasa juyowa seya sake cewa "Ab...bu!! Kham..eelarh!" Da sauri ta juyo tana kallonshi yana pointing window idonta jajir. "Abbu!! Da Ummu!!" Ya gaya daidai wannan karan" A guje taje wajan window kawai ta hangosu sun fito anata masu sannu da zuwa Ummu se hawaye take. Fitowa tayi a guje tana ihu "Abbu!! Ummu!!" Da karfin gaske tanayi tana gudu tana kuka. A tare suka dago suka kalleta, gudu kawai take harta iso inda suke seta tsaya a hankali tace "You guyx are alife" kaman tana magana da kanta kawai ta fashe da wani irin kuka ta fada jikinshu a tare ta rungumesu. Huging nata back sukayi amma har'a lokacin Ummu was in shock, sun dade a haka seta sakesu. Abbu yajasu suka shiga cikin gidan baki daya. Khameelarh ta kalleshi tace "I thought you guyx....." se tayi shiru kawai "C'mon my baby i missed you" Abbu ya fada yana yana bude hannunshi dukka. Fadawa tayi a guje ta sake rungumeshi. Duk abun nan El_Armeen yana kallonsu yana murmushi kawai. 💋💋💋

Share:

Contact Form

Name

Email *

Message *