Tuesday, 12 September 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 23 "Ya'Marwan open the door please" tayi magana kaman tana kuka. Shiru yayi be kulata ba ta kuma kiran sunanshi a hankali "Ya'Marwan" still no respond ta dade a tsaye tana kiran sunanshi amma yaki amsawa kuma yana jikin kofan yana sauraronta. Daga baya ta wuce taje ta kwanta. Mikewa yayi ya shiga toilet yayo alwala ya shinfida dadduma ya fara gabatar da nafila cus ya gane shine kawai me sakashi natsuwa,shine kawai ke sashi mantawa da matsalolinshi,shine kawai ke bashi kwanciyan hankali kuma seyaji kaman yana kusa dasu Mammi, kaman sunajinshi a lokacin *** Ummu ce ta sauko kasa tana kiran sunan Maid din gidan. Amsawa tayi tazo ta durkusa a gabanta. "Samomin ruwa da tsinma" "Yes Ma'am" ta mike ta nufa kitchen Itama Ummu seta nufa parlo inda vase nata yake kawai setaga bashi bane a wajan na wajan stairs ne. Juyawa tayi ta kalla gun stairs din da sauri babu komai a wajan. "Jameelarh!! Jameelarh!!" Ta fara kwallawa maid din kira. "Yes Ma'am" tazo da sauri ta kuma durkusawa. "Were is my mothers flower vase?" Tayi magana har muryanta rawa yakeyi alaman ba karamin so takema Vase din nan ba. Durkusar da kanta kasa tayi "Ma'am i think you should talk to..." se tayi shiru ta kasa magana jikinta na rawa dan ta san halin Meelarh zata iya kuranta a yau din nan. Da Ummu ta gane wanda take nufi seta wuce tabar Maid din a durkushe. "Khameelarh!! Khameelarh!!" Ummu ke kwalla mata kira sannanta fara hawa staircase din. Khameelarh kam tana dakinta a kan study table nata tana designing wani takalmi kawai taji Ummu na kiranta da 'Khameelarh' dumm! Gabanta ya fara fadi "Busted!" Ta gaya tana zare ido kuma ta kasa amsawa. "Khameelarh!" Ummu ta kuma kiranta da full name nata abunda batayi se idan tayi laifi. Mikewa tayi a guje ta nufa bathroom ta kulle kofa, se kuma ta fito ta shiga closet nata shima fitowa tayi. Balcony ta fita tana neman inda zata sauka ta gudu se taga babu hanya ta kuma dawowa. Ta haye gado ta fara baccin karya. Shima taga baze yuwu ba mikewa ta kuma yi ta sake shiga closet dinta ta fara hada kayanta wai zata gudu. Se Ummu ta banko kofa ta shigo se jikin Khameelarh ya fara rawa ta mike a guje cikin inda kayanta yake ta shiga ta durkusa kaman barawo tana wani zare ido. "Khameelarh!" Ta kuka kiranta. Seta nufa study table nata ta hango drawing din seta juyo ta nufa toilet tana kiran sunanta tana kuma knocking shima shiru seta leka balcony cus the door was open. Babu Khameelarh shima seta shiga closet nata, idonta ne yakai kayan data fara hadawa wajan zata gudu dashi. Karasawa gun kayan tayi seta kuma cewa "Khameelarh!" Shiru kaman ta sani seta nufa inda kayanta yake ta bude kofan a hankali tana matsar da kayan dayake a jikin hangers suke kawai se taga Khameelarh a kasa wai ita ta boye. "Are you serious? Kinajina ma kenan kika boye? Wait. Kinsan abunda kikayi kenan?" Fitowa Khameelarh tayi daga wajan kawai seta fashe da kuka "Ummu wlh it wasn't my fault!" "Then who's fault was it?" Ta tambayeta tana folding hannunta "Me. No El_Armeen" ta gyara da sauri "El_Armeen" Ummu ta tambayeta tana daga giranta daya sama. "Yes. You see lokacin kun kusa dawowa koh? Ina zaune a parlo dayake kullum yana zuwa yana keeping dina company, so se ina zaune akan kujera" and then she paused se ta sha majina kaman dagaske seta cigaba "To bansan yazo ba kawai seya ban tsoro ta baya na, na mike zan gudu kawai se na buje vase din ya tarwatse and mun kasa guming nashi" durkusawa tayi a kasa ta rike kafan Ummu "Ummu my baby my presious mother my one and only Ummu dan Allah kiyi hakuri kinji a promise to do the chores for a whole wee... day" kaman abun arziki. "Hadda wasan banza kuke da El_Armeen?" Zare ido Khameelarh tayi "Wlh a'a kima tambaya maids din gidan bana wasa dashi wlh ranan ne kawai ya ban tsoro shikenan" "Yanxin tashi! You know how important that vase was to me right?" "Yes" tayi magana a hankali tayi wani poppy face irin she's sorry aji tausayinta "It was your mothers" she added looking truely guilty "Good..." se tayi shiru se hawaye ya fara zubu mata "And you know how i love that vase it was the only thing she left" ta karashe magana muryanta yana rawa (Kunsan wasu idan sunada ciki they get really emotional) Kallonta Khameelarh tayi sosai "Ummu are you crying?" "No am not" tana share hawayan "Ummu am really so sorry" "Shikenan" ta fada tana san fita daga dakin Shan gabanta Khameelarh tayi "Ummu seriously you are pregnant you just won't admit it" '"I am okeyy? And i don't know what am doing" Hannunta ta rike kaman sa'anta "You can do it okey? (Kuji min yarinya) Daga mata kai Ummu tayi kaman wata karamar yarinya (Kunsan me akayi anan? Exchanging akayi. Khameelarh ta kuma Maman and Ummu ta dawo daughter. Lol) "Now you are all messy why not muje s-h-o-p-p-i-n-g?" Tayi spelling dinshi feeling all freaked out and excited "Omi! God. That will really help. But na dade banje shopping ba" "Thats no problem" ta gaya irin ba komai ba alhalin itama tunda take bata taba fita wai shopping ba sede ko online shopping ko kuma a tura maids din mansion din da driver. "Amma tsaya kayancan" se tayi pointing kayan da Khameelarh ta fara hadawa "Me zakiyi dashi" "Just forget it okey?" "Fine. Wait guduwa zakiyi da?" "Ummu!" Tayi ihu "Okeyy!! Okeyy!!" *** Ummu ta saka wata black duguwan riga kwata-kwata be matseta ba kuma be mata yawa ba. Ta daura wata black veil irin babban nan. Khameelarh kuma ta saka wata white duguwan riga da digon blue se blue veil da fari-farin flowers a jiki (So i wanted to post the picture i selected and yaki posting so please kindly check the photo that represent the whole page) Fitowa sukayi after all the selfies and shirme suka shiga wata arninyan black and red Range Rover 2015. Sega bodygyard din Abbu ya nufo su. Khameelarh na hangoshi tace "Ummu sauri ki tada motan mu tafi dan Allah" Juyowa tayi ta kalleta "Ummu kiyi sauri abeg" ta kuma maimaitawa "Meye wai haka?" "Wancan mayan yanxin zece seya rakamu" tayi magana tana pointing dinshi Juyawa tayi taga me take nunawa. Se ta ganshi. Itama sauri ta farayi tana saka sit belt dan batasan ya rakasu yayi kusa dasu sosai dayake Ummu ta rugada ta kunna motan kawai se Khameelarh ta tura giya. Se Ummu ta taka motan ya fara tafiya da karfi ta fuzga motan ya fara gudu. Se suka saki dariya da sukaga guard din ya tsaya suka nufa gun gate. Guard din kowa daya tsaya a hankali ya taba abun kunnenshi yace "Don't open the gate" Yake gayan ma security din Daga mai kai kawai yayi dan suna kallon juna Horn din motan suka ringa danna ma scurity ya bude gate amma ya tsaya yana kallon. Khameelarh ta saka hannunta akan abun taki cirewa kara kawai yakeyi. Ummu ta saka hannu a kunne se dariya suke. Guard din ya karasu gun yayi knocking window gefan Ummu suka tsoarat baki daga suka kalla gun "F*ck" sukace a tare da suka ganshi. Hannunta saka ta bude mai window seta juya tana kallon streaght "Ma'am you know you are not suppose to go out by yourself after what happened" Ya gaya in an respective tone. Shiru tayi bata kulashi ba dukda tasan gaskiyanshi. Khameelarh kam se hararanshi takeyi ya lura amma seya basar kawai dan zaman lafiya. Magana ya kumayi da abun kunneshi seyace "Can i?" Yana alaman bude kofan "No!!" Khameelarh ta fada da karfi, begeta Ummu tayi seta daga mai kai bude kofan yayi ta fito. Wani security yazo ya budema Khameelarh nata itama ta fito suka bude masu baya duk suka shiga. Suna hada ido da guard din Khameelarh ta mashi dakuwa shi kuwa murmushi yayi mata kawai ta kuma sakar mai harara. *** Range Rovers ne guda bakwai suka gero duk bakake sena tsakiya ne wanda su Ummu ke ciki Red and black Guard dinne ke driving nasu duk motocin sunsha tint. Selfies din hauka suka ringayi. Tayi posting a insta tace Mother and daughter day. Wata mool suka isa Ummu da Khameelarh duk suka saka shades dinsu suka fito daga motan already paparazzi suna giransu ko saboda posting dinda tayinne suka duba location din oho! Guards 5 suka fito suka kare mutanan wajan harsu Ummu suka iya shiga. Guards biyu suka tsaya waje bayan wanda ke cikin motan se uku suka shiga cikin mool din suna binsu a baya. Manager mool din yana ganin wanda suka shigo ciki ya saka a kura mutanan wajan (Idan mutum beda wani matsayi se ata wulakantashi. Allah ka azurtamu. Amiiiin ooo). Ummu data lura da abunda akeyi ma mutane a wajan se ta saka baki tace ya kyalesu mana mutumin yaki Tace idan kuwa be kyalesu ba suma zasu bar mashi mool dinshi. Da haka ya kyalesu wasu masu zuciya suka bar wajan baki daya wasu kuma wanda basusan mutuncin kansu ba suka tsaya. Guards biyu suka dauko masu basket guda biyu suna binsu 'side to side' (Ariana grande ft. Nicki Minaj) Dayan guard din Abbu kowa yana biye dasu a baya. Khameelarh kowa rabin hankalinta yana kan wayanta ta dago kanta taga wanda ke binta da basket dinta se taga wani daban juyawa tayi tana duban wancan Guard din se ta ganshi yana biye dasu kawai a baya. Wani evil smirk ta saki tace ma wanda ke binta da naya basket din "Ni bakai nakeso ba wancan nakeso" tayi magana kaman da shagwaba tana nuna Guard din Abbu. Kallon juna suka farayi. Ummu tace "Meelarh wancan is not like a normal gaurd shi..." "No Ma'am karki damu duk abunda yaro keso shi ake bashi" Yayi magana yana amsan basket din yana mata wani murmushi "What the f*ck! Nice yarinyan?" "Meelarh shut up will you?" Ummu tayi mata magana. "Amma Ummu kinji abunda yace min" kaman zatayi kuka tayi magana "Ke kika saya da kudinki tunda kikace shi kikeson ya amsan maki" shiru tayi tana kunbura fuska kaman zata fashe. *** Shirme suka ringayi a mool din nan kaman ba gobe kuma tayima Guard din Abbu me suna Aleeyu wukanci kaman ba gobe. Se taga abu tace shi takeso idan ya dauko se tace na can sama takeso haka ze dauka ladder yahau ya dauko mata seta amsa ta kalla seta yamutsa fuska tace "Ya tsufa" ta gaya abun nan yafi dau 10 shi kuma seya amsa ya maida. Sunyi siyayya sosai ga haukan da suka ringayi a mool din nan mutanan wajan se daukan hotonan su sukeyi. Wata Baby Ummu ta gani a hannun wata mata Baby girl gata kyakkyawa ta kalla Khameelarh "Meelarh kalla Baby nan" Meelarh da a rayuwanta zata iya kirga daukan Baby da tayi. Seda ta amsa Baby nan ta ringa yawo da ita a wajan dukda bata iya rikewa sosai ba ta ringa daukansu hotona kowa. Maman Baby baki har kunne ana son Baby. "Who's a good girl? Who's a cute baby? Ohh. Yes you are. Yes you are" Khameelarh ce da Baby ita kowa yarinya se dariya takeyi. Check book Ummu ta ciro ta rubutama Matan check din 20,000 ta bata wai ta sayan ma Baby diapers se godiya take. Khameelarh kaman karta bata yarinyan taji itama Baby seda tayi ihu. Sunfi 3hrs a mool din nan se shirme sukeyi Ummu kowa ta bada kyautan kudi yafi 70,000. Daga bisani suka nufa inda ake biyan kudin shima nan sun dade ana shirme suka biya kudin aka kai masu kayan har mota suka shiga. Aleeyu kowa wato personal guard din Abbu yasha dakuwa a wajan Khameelarh yafi sau goma shi kuma seya basar. (Yarinta) A news kowa ko ina se labarin abun ake da kyautan da Ummu tayi. --Two weeks later-- R ayuwa ta kuma daidai a Lawiza family kowa ya kuma bakin aikinshi Khameelarh itama ta kuma makaranta itada El_Armeen dan shima tunda ta bari be kuma zuwa ba se suka kuma tare everything was back to normal for this family. Abbu kowa jiki yayi daidai babu wata matsala. Amma su Vice president (sunan daya tsana kenan) kullum sake planing yadda ze hallaka President yake. Abbu bawan Allah shi kowa ya yarda dashi tsakani da Allah be taba kawo negetive thought a zuciyanshi ba. *** Momy El_Armeen se ramewa take yaronta ya tambayeta meke damunta taki gayan mai ita abun duniya duk yabi ya isheta gashi sonda take mai bazata iya rabuwa dashi ba. Wani sa'in ma be kwana a gida yana wajan karuwanshi (Kugi tsohon banza). ♥♥♥






0 comments:
Post a Comment