Monday, 4 September 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 20 Sorry not sorry- Demi lovato Manal na kwance a dakinta idon nan ya kunbura yayi kato kaman zasu fadu se kuka take. Dashi take kwana dashi take tashi har muryanta ya dashi gashi rana daya kawai ta wani rame Marwan yayi-yayi tace abinci take se kuka kawai takeyi. Shima ba'a barshi a baya ba ku yaushe yana kan sallaya yana mata addu'a yana kuka duk sun rame se hanci da idanuwa daya rage. Wajajan karfe 3pm duk suna dakunansu kowa na kan gado ba bacci suke ba. Manal na sana'arta shi kowa rabi bacci yake rabi kowa idonshi biyu. Yanata tunanin Mammi. Akwai ranan da take bacci a dakin ta yazo wucewa ya hangota seya shiga ya dauko wani cream dinta ya shafa mata a hannu seya dauka tsinken tsintsiya ya shafa mata a kunne seta saka hannun cream din zata bige abunda ke wajan se kawai ta bata fuskanta da cream din ya ringa mata dariya, ita kuwa mikewa tayi da sauri ta rankwashe kanshi ya mike a guje ya bar dakin. Besan sanda wani hawaye ya fara zubu mashi ba kawai seya fashe da wani irin kuka zuciyanshi wani irin abu take mai kawai seya fara ajiyan zuciya a hankali. Kaman cikin mafarki se yaji wani irin kara a parlo a birkice ya mike zaune yana sake jin abun ya tabbatar daga parlo ne a tare suka shiga parlo shida Manal seda suka hada ido dukkansu idonsu yayi jajir. Se suka maida hankalinsu inda suke jin karan. Wajan T.v ne yana kawo red seya dauke. Motsowa Marwan yayi kusa dashi ya taba remote din kawai se fuskan matan ya fito. Kana ganin fuskanta kasan bad news ta kawo masu "Hey Manal. Marwan ya kafanka?" A hankali take magana. Shiru yayi be kulata ba can seya ce "Ina Abbah?" Seda ta kalla Manal sannan ta kalla Marwan a hankali ta fara "Kullu nafsi za'ikatul maut....." Rike kai Manal tayi ta kurma wani uban kara na kusan 50secs se kawai ta saki wani dariya ta zube a wajan. Kafin kace me shima Marwan ya sume! Babu me taimakawo kowa gashi su kadai ne a gidan. Hawaye kawai matan ke zubarwa cus ba karamin tausayinsu takeji ba ace yara dasu su rasa iyayensu dukka a lokaci daya an maidasu marayu karfi da yaji. da sauri ta kashe video call din. Befi 30mins ba se gata tazo har'a lokacin suna sume dukka, tazo itada wannan doctor da Acting president ke aiki dashi wanda ya duba sanda Abbah ya rasu ashe shima aikin su daya da matan da take taimakawa su Marwan wato Secret Agents Of Nigeria (SAON). (I just made it up) suna aiki ne a boye bana Government bane wanda ko President himself be sani ba aikinsu akan mutane da suke neman taimako ne shine suke taimaka masu. A gadon da aka kwantar dasu anan aka maidasu. Doctor ya duba Manal batada wani damage akai cus dariyan da tayi se matan tayi tunanin ta sama matsala ne. Marwan kowa kaman ze tashi se wani nunfashi yake sama-sama kaman za'a cire mai rai (dukda bansan yadda ake ba). Dan haka aka dubashi aka gano ciwon zuciya yanason ya kamashi yama fara kamshi and he is too yoing to have it. Seda aka mai dressing kafanshi sannan ta rubuta mai wani note kusa da gadonshi akan idan ya tashi yasha magongunan data bar mashi a wajan shida Manal sannan suka wuce. Bayan ta masu alluran samun hutu. *** Acting president ke zaune sojojin daya aiki suka dawo suke cemai sun kashe Marwan da Manal tunda shi wawa ne seya yarda harda murnan shi. Wai ya gama da family su shikenan. Abbu yanxin ya samu sauki sosai yana iya tafiya yana komai dakanshi cus jininshi baki daya aka chanja mai in-case idan akwai guban a jikinshi. An yanke masu nan da two days zasu kuma gida amma Ummu tace kar Doctors din su gayan ma kuwa sede kawai a gansu a Abuja. Hatta Khameelarh itama batasan da zancan ba. *** Rayuwansu Marwan ya jagule ya chanza shide ta nashi gefan jira kawai yake mutuwa tazo mashi dan kusan sau uku yana kukarin kashe kanshi Manal na hanashi na farko wuka ya dauka ya daura a hannunshi ze yanka jijiyanshi ta ringa kuka tana ihu wai idan ya mutu ita kadai zata rage haka ya fasa. Rayuwansu de ta kuma wani iri abu kaman a film ya riga ya daukan ma kanshi alkawari se yayi avanging death din iyayenshi koba yanzin bane seyabi duk wanda keda hannu shima ya kasheshi sede shima azo a kasheshi. His heart is now full of darkness, His cute smile is nomore ya tsana kuwa a duniya ya tsana family President cus yana ganin hadda laifinshi. And the very man he will never forget in his life, mutumin daya fara sakashi a halin dayake ciki, mutumin dayayi sanadiyan rabuwansu, mutumin daya kashe iyayenshi. Kullum seya dauka M-card din ya kalla. Hatta Manal bema magana kullum yana cikin dakinshi be damu da halinda take ciki ba. He now don't care about anyone he hate the freaking world he hate all the people that are living in it. T.v dake dakinshi tuni ya fasashi wayan ma tuni ya tarwatsashi. Yanzin haka zaune yake a bakin gadonshi a kasa da scissors a hannunshi ya hudeshi kawai seya daura a hannunshi ya yanka ku alaman jin zafi beyiba. M-card din ya dauko a saka a cikin wani dan karamin abu kaman paper amma ba paper bani kawai seya tura cikin naman hannunshi (O. M. G) allura ya saka ya dinke wajan. Wajan yayi jajir banda jinin dake zuba, idonshi yayi jajir kana kallonshi kasan yanajin zafi. Goge jinin yayi ya zama M-card din yana cikin naman jikinshi kenan (God!). Marwan ya chanja sosai kaman bashi bane idan yaji ciwo Mammi tazo goge mai ake kokowa dashi yana ihu amma shine ke yanka naman jikinshi yau kuma yana nunawa ko a jikinshi. Fuskan nan a murtike kaman bashi bane wanda duk sanda ka daga kanka zakaga yana maka murmushi ko yaushe akwai murmushi dauke a fuskan nan. Gashin nan is a mess kaman bashi bane kullum yake brushing gashinshi sau uku ko biyu a rana. A yanxin be tausayin kowa besan kowa ko matan datake taimaka masu idan ta masu requesting video chat se yayi disconnecting sede idan Manal na wajan ta dauka. Manal kam yanzin tayi tawakkali ta fauwalawa Allah komai. Kullum tana cikin ma iyayenta addu'a, kullum tana masu addu'a baki daya Allah yasa su hadu baki dayansu a cikin gidan Aljanna (Allah sa baki dayan mu mu hadu acan. Amiiiin) Dukda ramewan da tayi kaman wanda ta shekara tana ciwo be hanata boye damuwanta ba saboda Marwan. Cus taga alaman he's more affective than her, ta fara damuwa da yadda Marwan ya kuma tashin farko. Wani sa'in zata girka masu abinci takaimai har daki ko kallonta bayayi se bayan ta fita ze fito da plate din ya ajiye mata akan dining. Rabonda taji muryanshi tun randa yace 'Ina Abbah' Randa matan nan ta kirasu kenan take gayan masu shima Abbah ya rasu. Tou tun ranan bata sake jin muryanshi ba. Kota mai magana sede ya bita da ido kawai ya kuma so silent ko abinci bayaci. Haka zata shiga daki tayi kuka-tayi kuka se tanajin mutuwan iyayenta yazo mata sabo tal. RASHIN MAHAIFA sucks! Kullum abunda take fada kenan. Gashi an kullesu a gida babu daman fita kuma babu waya. T.v ne kawai abokin hiranta ita kam. Babu ranan da baxatayi kuka ba, babu shi. Ya rigada ya zaman mata jiki, tayi sau uku sau hudu a rana se taji dadi a ranta. A duk lokacin da tayi wani abu daze tuna mata da Abbah da Mammi ana wajan zata kwanta tayita kuka harse ta gaji dan kanta ta tashi cus babu me bata hakuri. Gashi matan nan bata taba zuwa su hadu ba! *** Yau karfe 2pm Allah ya saukar dasu Abbu a Nigeria. Suna sauka Airport din were very surprised da suka ganshi. Benx guda goma aka kawo masu suka shiga dayake an saba nashi yana tsakiya yau se Ummu tace su shiga muta na biyu cus babu wanda zeyi tsammanin yana ciki! Acting president yana zaune se wani ya kirashi yake gayan mai Presisent ya dawo. Kafin yayi magana se yaga ana nunawa a news. Wani irin wulli yayi da wayan hannunshi ta tarwatse, ya zubar da dukka takardun table nashi mikewa yayi ya nufa wajan T.v shi, kujera ya dauka irin me karfe a wajan kafan nan kawai ya buga a babban T.v nan yana ihu seya fashe. Ya dade yana hauka shi kadai a office dinshi. P.A shi tana jinshi babu daman ta leko se'a koreta bata shirya rasa aikinta ba shiyasa ta shareshi idan ya gama tasa a gyara wajan. Wani shawara ne yazo mai kawai ya dauka Telephone din office dinshi yayi dailing wani number seya saka a kunne. Befi ringing uku ba aka daga. "Yes. Inason ka saka snipers uku a yanxin nan su tarwatsa min motan da President ke ciki, kasan wanne ne koh? Tou na tsakiyan ne yake zama a ciki. A ta harbinshi harse motan ya kama da wuta one more thing idan aka kamaku if any of you dare to mention my name y'all dead!" yana kaiwa nan ya kashe call din yana ajiyan zuciya kaman zaki se'a lokacin yadan ji dadi a zuciyanshi. *** El_Armeen da Khameelarh as always suna zaune a parlo shi tun sanda su Abbu suka bar garin gidan ya zaman mashi wajan yini wani sa'in se 9pm yake tafiya gida har Mommynshi ta sabama. Kowa na danna wayanshi cus har Khameelarh tayi sabon waya (aikin kudi) se El_Armeen yayi saurin dagowa yace "Ina remote yake?" Ko kallonshi batayi ba tace "Jirani na naimo maka dan rainin hankali kawai" tsaki yaja ya mike ya dauka yakai news ae kowa seyaga motansu Abbu an hada convoy dukka motan baki kuma ko wanne akwai karamin flag din Nigeria a gaban motan. Ihu ya saki yace cewa "His Excellency is back!" Wani irin dagowa Khameelarh tayi ta kalla T.v ta tabbatar motocin Abbu ne wani ihu ta saki itama batasan sanda tayi wulli da wayanta gefe guda ba ta rungume El_Armeen sunata ihu basu ma san sunyi ba. Kawai se Khameelarh ta fashe da kuka, a rude ya rike mata kafadanta ya fara tambayanta "Meyafaru kuma?" Batayi magana ba se hawayen dake kwaranyo mata tanayi tana murmushi "This the happiest day of my freaking life!" Ta gaya da karfi hawaye na zubuwa amma tana murmushi. Dariya yayi shima ya kuma rungumeta. Haka suka zauna suna kallon yadda motocin ke tafiya a hankali yan garin se ihu ake ana dagama motocin hannu. Samari da yara bin motocin suke aguje suna ihu *** Suna cikin motan Ummu na rike da hannun Abbu se kallon titin suke inda mutane ke kallon motan tsakiyan anata daga mata hannu cus dukkan motocin akwai tint and is very dark so baza asan wanne ne yake ciki ba. Se murmushi kawai sukeyi. Dayake su hudu ne a motan da suke ciki. Da driver se personal bodyguard din Abbu wanda Abbu ya yarda dashi sosai cus shi sau dayawa idan suna tare da Abbu idan aka kawo mashi hari yana sacrificing kanshi ya daukan ma Abbu bullet shiyasa ya yarda dashi sosai. Ko sanda suke hospital din shinema yake tsayawa a bakin kofan dakin ko yaushe duk wanda ze shiga dakin seya nuna mai ID-card dinshi na doctor kafin ya shiga. Se Ummu da Abbu Wasu snipers uku na hango akan wani building suna labe kowa da bindiganshi suna pointing motan tsakiyan seda gabana ya fadi cus i don't want to witness this moment. Harban motan tsakiyan suka fara ta ko'ina mutanan wajan aka fara tsarwatsewa anata ihu. Salati Ummu da Abbu suka farayi ta sake kankame hannunshi shi kowa yayi saurin dukar da kan Ummu. Dukka motocin suka tsaya wanda ke bayan suka fara juyawa na gaban kuma suna tsaye se Bodyguard din Abbu ya fito. Abbu nata cemai ya dawo amma be saurareshi ba ya kalla driver "Make sure you take them home save!" Yana gaya yana gyara bindiganshi Daga mai kai driver yayi kawai ya tada motan suka fara tafiya yayima na bayan alamana suma su tafi suka fara tafiya shi kowa daga bindiganshi yayi ya seto sniper daya aekowa cikin sa'a ya samoshi. Tuni motan ya faraci da wuta Allah ya taimaka ma mutum dayane a ciki amma ya rigada ya kune. Kafin dayan ya ankara har'an samoshi shima sauran guda daya seya mike ze gudu, bodyguard din ya fara binshi. Khameelarh suna kallon T.v suka fara ganin yadda ake harbin motan da suka tabbatar Abbu na ciki. Mikewa tayi da sauri hannunta a baki gama kasa komai tana tsaye a haka kawai shima El_Armeen ya tsaya yama kasa yin komai kawai yana tsaye. Bodyguard din ya tare sniper dayaga there is noway out kawai seya daga bindigan ya harba akanshi a cikin 2secs da sauri ya karasa gunshi amma har rai yayi halinshi. Chaje jikin sniper Bodyguard din ya farayi dan kuze sama wani abu a ciki. Amma be sama komai ba dan ko ID-card dinshi babu a jikinshi. Hakama sauran babu komai a jikinsu. Tuni an kira taimako harsun iso an fara kashe wutan an dauko gawan driver dukda ya kune anyi gidan President dashi cus ya ganshi. Snipers din kuma an debesu dan ayi bincike ko su waye and waya aikosu. Khameelarh kowa har'a lokacin tana tsaye da hannunta dukka a baki cause bata masan me zatayi ba. Driving din became so quite Ummu was in shock cus tunani take da sune a cikin motan Abbu shima haka. Dukka sauran motoci taran suka isa gidan a tare. Kawai se su Khameelarh sukaji hayaniya a waje ana shigowa da motoci. El_Armeen ne yayi kokarin lekawai kawai ya hango Abbu an bude masu kofa yana rike da hannun Ummu duk ya rame. "Khamee......larh!! Kha....." seya kasa karasawa yanata pointing window kawai. Ita tama kasa juyowa seya sake cewa "Ab...bu!! Kham..eelarh!" Da sauri ta juyo tana kallonshi yana pointing window idonta jajir. "Abbu!! Da Ummu!!" Ya gaya daidai wannan karan" A guje taje wajan window kawai ta hangosu sun fito anata masu sannu da zuwa Ummu se hawaye take. Fitowa tayi a guje tana ihu "Abbu!! Ummu!!" Da karfin gaske tanayi tana gudu tana kuka. A tare suka dago suka kalleta, gudu kawai take harta iso inda suke seta tsaya a hankali tace "You guyx are alife" kaman tana magana da kanta kawai ta fashe da wani irin kuka ta fada jikinshu a tare ta rungumesu. Huging nata back sukayi amma har'a lokacin Ummu was in shock, sun dade a haka seta sakesu. Abbu yajasu suka shiga cikin gidan baki daya. Khameelarh ta kalleshi tace "I thought you guyx....." se tayi shiru kawai "C'mon my baby i missed you" Abbu ya fada yana yana bude hannunshi dukka. Fadawa tayi a guje ta sake rungumeshi. Duk abun nan El_Armeen yana kallonsu yana murmushi kawai. 💋💋💋






0 comments:
Post a Comment