Tuesday, 8 August 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA -CHAPTER 4 INTRODUCTION TO THE MANSOOR FAMILY Alhaji Mansoor shine Asalin sunanshi auran saurayi da budurwa sukayi da Hajiya Mait Asalin Alhaji Mansoor buzu be haka ma Hajiya Mait duk iyayensu buzaye ni a garin Kano suka hadu sukayi aure se suka dawo Abuja da zama A NNPC yake aiki while ita kuma designer ce so sunada rufin asirinsu Allah ya basu yara biyu Marwan wanda shine babba se Maryam wanda sunan Mahaifiyar Alhaji Mansoor kenan amma ana mata inkiya da Manal(Moi babe😻) Marwan da Manal sun tashi cikin so da kauna da kuma tarbiya amma fa basa zama a roof daya su dade dan duk sunada tsokana kuma dukka baza'a tabasu a zauna lafiya ba tou dan haka kullum suna cikin fada da juna wani sa'in ma har danbe sunayi se Manal ta haye kan bayan Marwan Marwan yanada shekaru 26 yanxin haka while Manal na 17 yanxin MARWAN Saurayi ne me dan banzan fara'a dason mutane da kuma son babies dan duk inda yazo yaga tou seya dauka Allah yasa mashi son yara a rayuwanshi kuma kullum ka kalla fuskanshi akwai smile akai be rabuwa da murmushi haka Allah yayishi kuma ga tsabta ga kuma son kwalliya Marwan nada manyan idanuwa he has this bushy eyebrow ga kuma lips nashi are cute and reddish ba wani dugu bane sosai dan baza'a sakashi a list na dugaye ba kuma baza'a sakashi ana guntaye ba. Fari ne irin sosai ku hango kawai yadda yaran buzaye zasu kasance. Gashin kanshi kowa after every two weeks seya rage danshi be cika son gashi yayi yawa ba amma yana barin saura kuma ga gashin are curly #Damn Yanada gashin kafa though some girls find it disgusting but shi be damu ba cus sha'anin mata be dameshi ba amma yawancin abunda yakeyi yi yake saboda ya burgesu amma be shiga sabgansu Ga packs #IHaveFalling Manal kuma irin matan nan ne yan gayu tunda tasan tanada kyau so abunda ke rudanta kenan dan tanada dan banzan girman kai ba kaman yayanta ba da he's so simple and friendly THIS IS A BRIEF DESCRIPTION OF THE M FAMILY Dakinshi ya shiga yayi wanka shiga closet nashi yayi ya shafa lotion nashi da turare seya fito dagashi se dugan wando black da wata black top a hannunshi so babu riga a jikinshi (🏃♀i don see them) Gaban kofan closet din ya tsaya dayake akwai mirror a jiki seya tsaya yana brushing kanshi suka kwanta gasu kuma baki sosai Vest ya saka sannan ya saka rigan ya dauko wayanshi da keys nashi ya fito Yana fitowa yaci karo da Mammi "Ina zaka bakayi lunch ba?" "Zanje inda aka fi sona ne dan na gane gidan nan kaman adopting dina akayi" Befa son inda zashi ba Murmushi tayi sannan tace "a dawo lafiya" seta fara wucewa Kallonta yayi seyace "Kinga abunda nake gaya ko Mammi danni bakisona shiyasa kike min haka kamata fa yayi kice nayi hakuri amma kince in dawo lafiya, shikenan" Dariya ne ya kwace mata amma seta fuske tayi wucewanta danta lura shi Marwan ba girma yake ba Abun kular dashi yayi da yaga tayi wucewarta she did'nt even care to say a word seya fice shima Bude gate ya farayi seya fita da motanshi sannan ya dawo ya rufe seya kama hanyan gidan wani mate nashi a UNIVERSITY OF ABUJA sunanshi Faisal Cewa ma yayi shi'a nan ze kwana *** Abbu ne ya fito Ummu na biye dashi a baya tareda jaka a hannunta da alama na Abbu ne se Khameelarh ta fito daga bedroom nata ta kallesu "Abbu ina zaka?" "Kano zani gaisuwa" ya fadi yana karasa fitowa ita kuma ta matso kusa dashi sannan tace "Waya rasu Abbu" "Dan masanin Kano ya rasu jiya" "Allah sarki. Allah jikanshi though ban sanshi ba" Ta fadi tana dan yamutse fuska "Amiin" suka amsa dukka su biyun "Yanxin yaushe zaka dawo?" "Gobe insha Allah dan inada meeting" "Abbu kawai kayi masu waya mana kayi gaisuwa baseka jeba" Kallonta yayi sosai shida Ummu sannan yace "Ya zama dole naje ne shiyasa zani. Amma karki damu gobe 10am insha Allah ina nan gidan kinji princess?" ya gaya kaman yana ma karaman yarinya magana Zunbure baki tayi sannan tace "Ni wlh Abbu banson kaje" "Then zo muje tare" kallonshi tayi irin are you for real? "Nah aiint intrested" "Meyasa?" Ummu wanda tunda suka fara surutunsu batayi magana ba ta tambaya "Cus, the place is gonna be noicy and naji kace sunanshi whatever you call him probably his popular and so many people will be there so seka dawo" Tana gama fadin haka ta shige dakinta Murmushi Abbu yayi sannan suka fito da Ummu. Suna fitowa compound din gidan wani guard yazo aguje ze amsa jakan hannunta dakatar dashi tayi seta hanashi jakan Sallama sukayi akan Monday da safe ze dawo(gobe kenan) Seda taga motan ya fita daga gidan sannan ta dena daga hannu ta juya. Ashe Khameelarh na kallonsu daga dakinta --The nxt day-- Ta gama shirinta ta fito setaga Ummu tana ajiye plate akan dining Karasawa tayi gunta tayi pecking nata. Ummu tace "bazakiyi breakfast ba?" "Yah na kushi" "Meyasa? haka zaki with an empty stomach?" "Ni Ummu bazan iya breakfast ba tareda Abbu bah" ta fadi da alaman shagwabe Ummu ta bude baki zatayi magana kenan se wayanta ya fara buzzing tana dubawa se taga number dan haka ta maida ta ajiye Har seda yayi sau uku sannan ta dauka tareda sallama Banji abunda sukace ba nadaji sun gaisa se Ummu tace "toh shikenan" se tayi hanging up Kallon Khameelarh tayi tace "principal naku ta kira wai tanason gani na muje tare dake. Me kikayi Khameelarh?" Ta mata wannan tambayan da alaman tuhuma "Ummu daga kiranki se kice nayi wani abu kika san ko grades dina ne sukayi high or something amma harkin fara zargina? I just wish one day you will be proud of me" "Meelarh honey,that's not what i meant. Yanxin de tunda bazakiyi break-fast dinba tasu muje" Ta fadi tana mikewa hannun Khameelarh ta rike suka fito tare. Bude masu kofa akayi suka shiga Ummu na driving cus ita baki daya batason ta zauna driver na driving nata she finds it disturbing (weird). Suna isa gate din school din a bude yake dan haka suka shiga. A lokacin iyaye se ajiye yaransu sukeyi so anata hayaniya Tana gama parking daga kan da zatayi kawai taga inda school din ya kuma dumm!! Gabanta ya yanke ya fadi seta juya ta kalla Khameelarh ita selfie ma takeyi Amshe wayan tayi a hannunta ta kalleta "Meelarh tell me you didn't do this!" Kallan compoud din school tayi seta maida view nata gun Ummu "I wasn't the one that did this" Kallonta tayi alaman bata yarda ba. Abun ya kullar da ita se tace "Why don't you guyx believe me? God!! Am fucking tired of this!!" Seta bude kofan zata fice riketa Ummu tayi tace "If i found out you did this seriously you are gonna here it from me!" Saketa tayi ta fito Khameelarh itama ta fito fuskanta has turn to red cus ita duk abunda zatayi idan tasan itace tayi she can take the blame amma she hates it ayi accussing nata akan something she didn't do. Se gaida first lady ake tayi yara da manya Khameelarh kowa da tuni ta wuce amma Ummu ta rike mata hannunta so babu daman tafiya dole ta tsaya se zunbure-zunbure takeyi. Suna shiga office din principal baki bude Ummu ta tsaya tana kallon office din yadda akayi mai Khameelarh kowa murmushi taketa yi Mikowa Principal din tayi ta gaida Ummu amma kasa amsawa tayi ta tsaya tanata kallon office din Murmushi principal din tayi sannan tace "You see how my student did to my office" kallonta Ummu tayi sannan ta maida kallonta zuwa Khameelarh seta sake kallon office din kasa magana ma tayi kawai ta sake hannun Khameelarh ta nufa kujeran dake kusa da table ta zauna tareda dafe kanta Ta kusa 10mins a haka se Khameelarh tazo ta zauna a daya kujera na kusa da ita,Principal itama tazo ta zauna a nata kujeran amma da alama tana dingishi(😹Khameelarh is a wicked bitch) Dagowa Ummu tayi with her red face ta sauke akan Khameelarh "Tell me you didn't do this!" Ta sake maimaitawa "Uh..mm....well....." ta fara kame-kame tana gyara barret nata "So this part is your job right?" Ta katseta duk ta gama chanjawa "Well yeah but....." Ji kake tawwww!! Ummu ta gaurama Khameelarh wata mari seta fuskanta ya juya gefe guda tana kallon daya side din kuma bata juyo ba she just can't believe ace yau ita aka mara wai kuma Ummu ta mareta da hannunta nan da nan hawaye ya fara zubo mata a idonta kaman ruwa and she was still looking at the other view kuma ta kasa rike wajan Ko ita Principal din ta mugun tsorata mikewa tayi da sauri se kuma ta kasa magana "Khameelarh me kikeson ki zama a garin nan? me kikeson ki maida rayuwanki? Kince ba kice kikayi wancan ba and hadda fushi ashe naki is worst... Juyo ki kalleni in this instant!!" Ta fadi da karfi Khameelrh kam ta kuma kaman frozen chiken danko motse bata sake ba se hawayen dake kwaranyo mata "Khameelarh am talking to you look at me!!!" Ta fadi da karfin gaske Amma ko alaman juyawa batayi ba "Mrs. Lawwan this....." "Stay out of this!!!" Ta guga mata tsawa Shiru tayi ta kuma ta zauna "Tashi kije mota ki jirani!!" Shima shiru "Khameelarh i won't repeat myself......" Bata karasa ba Khameelarh ta mike a zuciye tabar office din bag-pack nata ma anan ta barshi Nunfashinta wani sama-sama yake hawayen kuma be bar zubuwa ba #AnTaboYanmata Kanta akasa take tafiya dan karma ta hadu da wani aga tana hawaye Ji tayi ta binjige mutum tana dago kai kawai se taga Shopia Durkusawa Shopia tayi ta deba books nata daya zube dagowan da zatayi se taga idon Khameelarh jajir sakin books din tayi seta mike tsaye tareda wani murmushi folding hannunta tayi sannan tace "Now i understand why you say *Payback is a bitch*, i really do enjoy telling her all what you guyx did" Wtf! So she's the bitch that told them Khameelarh tayi maganan zuci amma seta rasa me zata ce mata "So now i hope zaki bar school din mara tarbiya kaw...." bata kai aya ba Khameelarh tayi ihu ta dira akanta Fadi kasa sukayi dukka biyun amma Khameelarh ce akanta Se yakusan mata fuska take da long nails nata ita kuma ta rike gashin Khameelarh se ihu suke zan iya cewa ihu yafi yawa *** Bayan fitan Khameelarh daga office din Principal ta fara kwantar ma Ummu hankali sannan ta juya mata laptop din kan table nata yadda Ummu zata gani Guess what? Khameelarh ce take kunce kujeran Principal din ashe akwai camera a office dinta "Innalillahi Allah nagode maka da ka bani wannan yarinyan Allah ka cigaba da shirya min ita" Shine kawai Ummu ta iya fadi dan batama san ta inda zata fara bata hakuri ba Katse mata tunaninta tayi da cewa "Mrs. Lawwan am so sorry na yanke shawara and i know it gonna be best for all of us. Tunda daman Khameelarh home schooling nata aka fara kawai a cigaba da mata tunda naga tafi sabawa dashi idan yaso in za'a fara Waec da Neco se tayi registiration a school din nan" Shiru Ummu tayi can se tace "Tou shikenan idan Abbunta ya dawo zan fadan mai, yadda akayi sena maki magana" Ta fadi da kyar "Okey tou shikenan Allah dawo dashi lafiya Allah kuma ya gyara mana zuri'a" "Amiin" Principal ta mika mata wasu papers tana budewa kawai taga anyi expelling Khameelarh ne a school din baki daya Wani murmushin takaici kawai ta saki Hayaniya sukaji a waje a tare suka mike principal din na gaba Plausing Ummu tayi da taga abunda ke faruwa ga Mustiee yana kokatin rabasu amma sunki sakin juna "Khameelarh!!" Gabadaya kowa na wajan seda ya juyo danjin muryan kawai se sukaga first lady A cikin 5secs kowa ya ware hadda Shopia da fuskanta ya zama kaman tayi fada da thousands kittes dan yasha yakushi Mikewa Khameelarh tayi gun motan ta wuce da birgiceccen gashinta ko kallon Ummu batayi ba Girgiza kai Ummu tayi tana rike da bag-pack na Khameelarh seta kalla Principal tace mata ta nuna mata locker Khameelarh danta cire kayanta "Ae baza'ayi haka ba barinje na debo mata" "Ohk thank you" "My pleasure" A tare suka bar wajan Umma ta nufa mota while Principal ta kuma office dinta Wani bunch of keys ta ciro a drawer seta dauko kwali ta fito Gun locker taje ta duba key na locker 199 sannan ta bude Komai na ciki sedata juyo mata a ciki sannan ta fito waje Trunk din motan Ummu ta bude suka saka kayan a ciki sannan Ummu ta ciro bandir na 500 ta mika mata godiya ta ringa mata seta shige motan ko kallon Khameelarh batayi ba ta tada motan suka fita daga school din Ita kowa kallon titi kawai take tana share hawaye Allah ya taimaketa akwai tint ajiki Wayanta taji yana ringing ta juyo danta dauka bag-pack nata se a lokacin Ummu taga yadda fuskanta yayi pink alaman marin data mata Dakewa tayi kuma seta juya ta cigaba da driving dinta daukan wayan Khameelarh tayi tana duba me kiranta number ta gani dan haka seta maida jakan ta juya tana cigaba da kallon window Suna isa gida kafin ta gama parking har Khameelarh ta fito a guje ta shige cikin gidan Tsayawa Ummu tayi tana kallonta se taji abunda ta mata bata kyauta mata bah.. amma kuma haka yafi da wannan tunanin ta gama parking aka bude mata kofa ta fito sannan ta bada key din motan dan a shigo da kayan Khameelarh na trunk nata.






0 comments:
Post a Comment