Wednesday, 23 August 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 16 Janta yayi ya saman mata wajan zama ta zauna tana maida nunfashi abun tausayi. Juyawa yayi ya kalla gefe da gefe kawai seya hango wani shagon provision "Tsaya anan barin sayo maki ruwa" daga mai kai kawai tayi. Mikewa yayi ya nufa gun shagon da sallama, saurayin dake shagon ya amsa mashi "Akwai ruwa me sanyi?" Marwan ya tambayeshi yana kallon shagon dan beson ya kalle saurayi wata kila shima yaga poster da ake nemanshi. "A akwai, na gura?" Daga mai kai kawai yayi "Guda nawa?" Ya tambayeshi yana nufan gun freezer "Daya ma yayi" "Tohm" budewa yayi ya ciro ya saka mai a leda ya mika mai shi kuma ya mika mai kudin ya bashi chanji. Harze fito seya kalle me shagon "Dan Allah in tambayeka mana" Ajiye abunda yakeyi ya kalleshi "ina sauraranka Allah sa na sani" "Amiin. Daman tambayan shagon saida kaya nake idan akwai a kusa?" "A akwai wani. Muje waje na nuna maka" Fitowa sukayi Me shagon ya mai kwatance shi kowa Marwan yamai godiya ya nufo gun Manal ya bata ruwan bayan ya bude mata Amsa tayi ta kafa kai se sha takeyi shi kowa ido kawai ya zuba mata yana kallonta shi tausayinsu yake ji sosai. Seda tasha kusan rabi sanan ta kalleshi "Gashi" ta fada tana mika mai sauran Amsa yayi shima yasha. Ta mike suka cigaba da tafiya. Basuyi wani tafiya me nisa ba sukaga store din da me shagon ya masu kwatance. Ciro jakan bayanshi yayi ya bude, credit card dinshi ya ciro a ciki seya mika mata "Rike min ki zauna anan karki tashi" amsa tayi ta daga mai kai kawai Shi kuma ya shiga ciki *** Acting president ke zaune a office nashi yana tunanin yadda ze kamo yaron nan can ya kalla Dove dake tsaya a bakin kofan yace "Wai ya kukayi da gidansu" "Babu komai fa yana nan a bude" "A bude?" Ya maimaita "Amma wlh bakuda hankali" he added "Your Excellency ban gane ba" "Yanxin kuje ku nemo min abunda ze amfani mu a gidan bayan nan kusa ma gidan wuta ku tabbata ku an kashe wutan baza'a gane abunda akayi ba. Ka gane koh?" "Yes boss" ya amsa yana kokarin fita daga office din "One more thing ka turo min P.A dina idan ka fita" "Tohm" kawai yace ya fice shi ya fara gajiya da abunda Acting President ke masu ya maidasu kaman bayi Ba'a wani dade ba sega P.A din ta shigo "Sir you asked for me?" "Yeah. Inson ki nemo min the best hacker a garin nan yanxin nan na baki 10mins ina jiran zuwanshi" "Yes sir" ta fice da sauri Ankai kusan 30mins segata ta shigo da wani haddadan saurayi "Sir am so sorry it took me some minute to find him"ta gaya jikinta yana rawa dan tana tsoran Allah tana tsoran Vice President Seda ya mata wani irin kallo tukun yace "Don't be cus you are fired. And don't you dare say a word just get out!" Ya gaya a tsawace ya cigaba da kallon papers dinda ke kan table dinshi Hawaye kawai ya fara kwaranyo mata babu daman magana haka ta kama hanyan fita. Gayen da ta kawo kallonta yake kawai ta bashi tausayi "Sir is my fault tin dazin ta kiran.." "Shut the f*ck up!" Ya katseshi a tsawace "Sir please just listeing to tin dazin ta kirani wlh mahaifitace babu lafiya seda na kaita hospital kafin nazo nan please just give her a second chance please" ya karese maganan a hankali yana kallon Acting President. Itama P.A din tsayawa tayi tana jiran jina bunda zece Seda ya kare masu kallo dukka daga baya yace "One last chance" "Thank you sir. Thank you so much" tana gaya tana share hawaye tana murmushi dukka "Don't thank me thank him" ya sake gaya yana kara daure fuska Kallon saurayin tayi me suna Mustapha tace "Thank you so much" Daga mata kai.kawai yayi yana mata smiling. A haka ta fice tanata gode mai. Kallonshi Acting President yayi fuskan nan a daure kaman ass din jaki yace "Inason kamin hacking wani phone ne hope kazo da Computer ka?" "Yes Sir" ya amsa shi yana ciro jakanshi a kafadashi. Waje ya samu ya zauna ya ciro laptop dinshi Acting President ya mika mai Wayan Marwan dana Abbah "Gashi inason duk yadda zakayi ka gano yadda suke ko yayane ka ganu yadda me Iphone din yake ka gane?" "Na gane" Hada wayan yayi da USB zuwa laptop dinshi ya fara wasu danna-danne ya kusan 20mins can yace "Sir yanxin akayi amfani da Credit card dinshi koh 2min ba'ayi ba" Mikewa yayi da sauri ya nufo inda yake zaune "Zaka gane location dinsu?" "Why not" cigaba da danna-dannenshi yayi seya dago yagayan mai inda suke da kuma sunan store dinda yayi using credit card dinshi Wayanshi ya ciro ya fara dialing wani number seya saka a kunnenshi "Yes. Kuxo yanxin.na gano indan suke zan maka sendin location nasu nima ina hanya. Ka taho ta Mens naka Ashap abeg cus zasu iya barin wajan" se yayi hangin up ya kalla Mustapha A.K.A computer freak yace "Ka tsaya anan am still gonna need your help" be jira abunda zece ba yayi ficewanshi ya gayan ma P.A nashi tayi cancelling meetings dinshi cus ze fita ya fice waje. Tama kasa amsa mai dan tsoro take tayi wani magana ya sake firing dinta dan ko 2weeks batayi ba da fara aikin. Motanshi ya shiga drivershi ya tada mota suka kama hanyan gunsu Marwan. *** Bayan ya shiga store din ya sayo wani rigan sanyi irin me hulan nan a hade guda biyu duk bakake da wanduna shida Manal se shades da spray(which bansan mezeyi da wannan ba) shima guda biyu se wasu boats suma biyu size dinshi dana Manal suma bakake ya biya kudin ya fito ya tambaya me shagon idan yasan wani hotel nan kusa ae kowa akayi sa'a akwai wani Motel a kusa yamai godiya ya fita ya amsa jakan a hannun Manal suka kaman hanyan Motel din. Suna shiga ya sama daki daya ne kawai available a lokacin dare harya fara cus 7pm lokacin Ya amsa key din dakin ya biya matan kudin kwana daya da credit card din ya sake using Manal na rike da kayan daya sayo suka shiga dakin wanda yake number 304. Bude dakin yayi suka shiga ya kira a kawo masu abinci dan yadda yakejin cikinshi kaman an kwashe kayan ciki dan yunwa, shi kenan balle Manal. Tana zaune akan bakin gadon abun duniya ya isheta yazo ya zauna kusa da ita "Manal" ya kira sunanta a sanyaye Bata amsa ba sede kallonshi da tayi kawai. "Ki tashi kiyi wanka kafin a kawo abinci" daga mai kai kawai tayi ya mike seya dakatar da ita. "Gashi" ya gaya yana mika mata riga da wandon Amsa tayi ta shige toilet din. Fashewa kawai tayi da wani kuka mara sauti ta dade a haka daga baya ta saki shower akanta tana cigaba da kukanta. Rice and stew aka kawo plate biyu se nama akai da drink. Zama yayi ya ringa cin abincin nan kaman an aikoshi seda ya cinye plate din guda ya kura da drink din yayi katt sanan yaji dadi. Jakan ya dauko ya bude sega bindigan daya amshe na sojan rikeshi yayi yana kallonshi can ya ajiye ya ciro wayan daya sama a cikin motan daya SATA seya ajiye a gefe kawai sega Manal ta fito idon nan yayi jajir ya kunbura ta saka kayan ga kuma kayan data cire a hannunta. Kallonta kawai yayi yasan kuka tayi amma seya basar. Kayan daya fito dashi daga jakan ya maida sannan ya dauka abuncin da drink din yakai mata ta amsa seta dauka dadduma data gani a jikin kujera ta shunfuda ta dauka veil dinta dan karami ta yafa ta fara sallolin da tayi missing. Marwan kayan shima ya dauka ya nufa toilet yayi wanka ya saka kayan a ciki ya dauro alwala ya fito ya tarar da Manal tana cin abincin kaman tanacin guba girgiza kai kawai yayi ya dauka dadduma ya fara sallolin wanda yayi missing yana gamawa ya ringa gero nafiloli Manal itama ta shinfida riganta taba binshi haka suka ringa nafila suna rokan Allah ya kubutar dasu daga halinda suke ciki. *** Mustapha ke zaune kawai se yaga sun kara amfani da credit card din. Da sauri ya kira Acting president ya gayan mai location dinsu dan haka can suka nufa daman sun kusa wajan. Motan sojojin na gaba while nashi yana biye dasu a baya. Sun dade suna gera sallolin se suka sallamar bayan sunyi addu'oi kenan suka mike Marwan yace mata ta kwanta akan gadon shi kuma ze kwanta akan couch din gyada mai kai kawai tayi dan da alama ta fara zama kurma. Ta haye gado shi kuma yayi kwanciyanshi akan couch din dakin. --30mins later-- Sunyi nisa a baccin wanda dakyar ya kwashesu se Marwan yaji tsayuwan mota kusa da window dakin dayake su suna sama ne, da sauri ya mike ya leka kawai kaman a mafarki se yaga motan sojoji guda biyu ga kuma wata Benz baka a baya. Gun Manal ya nufa ya tasheta da sauri ta mike tana susa hannu "Tashi they find us" yayi magana jikinshi na rawa dan tsoro yanxin there is no way out of this. A birkice ta tashi tana tambayanshi abunda zasuyi. Dauko mata takalmin da ya sayo masu yayi ya bata ta amsa ta zauna tana sakawa da sauri shima ya saka nashi. Shades din kowa ya saka cikin jakan ya saka spray dinma a ciki ya dauko bindigan daya amsa gun sojan ya mikama Manal bata amsa ba seta tsaya tana mai wani irin kallo alaman tambaya "Just take it" amsa tayi irin a juye yadda ta amsa kana kallon fuskanta kasan akwai tsoro a ciki Shi kowa ya ciro bindigan da Abbah ya bashi ya rike a hannu. Wata lighter ya hango akan fridge din dakin dauka yayi ya zira a aljihunshi sannan ya goya jakan a bayanshi *** Acting President ya shiga ciki yaga receiptionist din suka gaisa kaman dagaske se ya nuna mata hotan Marwan yace taganshi ya shigo nan Daga kai tayi da sauri tace ta gansu shida kanwarshi "Ohh then are they still in here?" "Yes sir they are" ta gayan mashi room number suka nufo saman dukkansu πππ






0 comments:
Post a Comment