Tuesday, 12 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 23 "Ya'Marwan open the door please" tayi magana kaman tana kuka. Shiru yayi be kulata ba ta kuma kiran sunanshi a hankali "Ya'Marwan" still no respond ta dade a tsaye tana kiran sunanshi amma yaki amsawa kuma yana jikin kofan yana sauraronta. Daga baya ta wuce taje ta kwanta. Mikewa yayi ya shiga toilet yayo alwala ya shinfida dadduma ya fara gabatar da nafila cus ya gane shine kawai me sakashi natsuwa,shine kawai ke sashi mantawa da matsalolinshi,shine kawai ke bashi kwanciyan hankali kuma seyaji kaman yana kusa dasu Mammi, kaman sunajinshi a lokacin *** Ummu ce ta sauko kasa tana kiran sunan Maid din gidan. Amsawa tayi tazo ta durkusa a gabanta. "Samomin ruwa da tsinma" "Yes Ma'am" ta mike ta nufa kitchen Itama Ummu seta nufa parlo inda vase nata yake kawai setaga bashi bane a wajan na wajan stairs ne. Juyawa tayi ta kalla gun stairs din da sauri babu komai a wajan. "Jameelarh!! Jameelarh!!" Ta fara kwallawa maid din kira. "Yes Ma'am" tazo da sauri ta kuma durkusawa. "Were is my mothers flower vase?" Tayi magana har muryanta rawa yakeyi alaman ba karamin so takema Vase din nan ba. Durkusar da kanta kasa tayi "Ma'am i think you should talk to..." se tayi shiru ta kasa magana jikinta na rawa dan ta san halin Meelarh zata iya kuranta a yau din nan. Da Ummu ta gane wanda take nufi seta wuce tabar Maid din a durkushe. "Khameelarh!! Khameelarh!!" Ummu ke kwalla mata kira  sannanta fara hawa staircase din. Khameelarh kam tana dakinta a kan study table nata tana designing wani takalmi kawai taji Ummu na kiranta da 'Khameelarh' dumm! Gabanta ya fara fadi "Busted!" Ta gaya tana zare ido kuma ta kasa amsawa. "Khameelarh!" Ummu ta kuma kiranta da full name nata abunda batayi se idan tayi laifi. Mikewa tayi a guje ta nufa bathroom ta kulle kofa, se kuma ta fito ta shiga closet nata shima fitowa tayi. Balcony ta fita tana neman inda zata sauka ta gudu se taga babu hanya ta kuma dawowa. Ta haye gado ta fara baccin karya. Shima taga baze yuwu ba mikewa ta kuma yi ta sake shiga closet dinta ta fara hada kayanta wai zata gudu. Se Ummu ta banko kofa ta shigo se jikin Khameelarh ya fara rawa ta mike a guje cikin inda kayanta yake ta shiga ta durkusa kaman barawo tana wani zare ido. "Khameelarh!" Ta kuka kiranta. Seta nufa study table nata ta hango drawing din seta juyo ta nufa toilet tana kiran sunanta tana kuma knocking shima shiru seta leka balcony cus the door was open. Babu Khameelarh shima seta shiga closet nata, idonta ne yakai kayan data fara hadawa wajan zata gudu dashi. Karasawa gun kayan tayi seta kuma cewa "Khameelarh!" Shiru kaman ta sani seta nufa inda kayanta yake ta bude kofan a hankali tana matsar da kayan dayake a jikin hangers suke kawai se taga Khameelarh a kasa wai ita ta boye. "Are you serious? Kinajina ma kenan kika boye? Wait. Kinsan abunda kikayi kenan?" Fitowa Khameelarh tayi daga wajan kawai seta fashe da kuka "Ummu wlh it wasn't my fault!" "Then who's fault was it?" Ta tambayeta tana folding hannunta "Me. No El_Armeen" ta gyara da sauri "El_Armeen" Ummu ta tambayeta tana daga giranta daya sama. "Yes. You see lokacin kun kusa dawowa koh? Ina zaune a parlo dayake kullum yana zuwa yana keeping dina company, so se ina zaune akan kujera" and then she paused se ta sha majina kaman dagaske seta cigaba "To bansan yazo ba kawai seya ban tsoro ta baya na, na mike zan gudu kawai se na buje vase din ya tarwatse and mun kasa guming nashi" durkusawa tayi a kasa ta rike kafan Ummu "Ummu my baby my presious mother my one and only Ummu dan Allah kiyi hakuri kinji a promise to do the chores for a whole wee... day" kaman abun arziki. "Hadda wasan banza kuke da El_Armeen?" Zare ido Khameelarh tayi "Wlh a'a kima tambaya maids din gidan bana wasa dashi wlh ranan ne kawai ya ban tsoro shikenan" "Yanxin tashi! You know how important that vase was to me right?" "Yes" tayi magana a hankali tayi wani poppy face irin she's sorry aji tausayinta "It was your mothers" she added looking truely guilty "Good..." se tayi shiru se hawaye ya fara zubu mata "And you know how i love that vase it was the only thing she left" ta karashe magana muryanta yana rawa (Kunsan wasu idan sunada ciki they get really emotional) Kallonta Khameelarh tayi sosai "Ummu are you crying?" "No am not" tana share hawayan "Ummu am really so sorry" "Shikenan" ta fada tana san fita daga dakin Shan gabanta Khameelarh tayi "Ummu seriously you are pregnant you just won't admit it" '"I am okeyy? And i don't know what am doing" Hannunta ta rike kaman sa'anta "You can do it okey? (Kuji min yarinya) Daga mata kai Ummu tayi kaman wata karamar yarinya (Kunsan me akayi anan? Exchanging akayi. Khameelarh ta kuma Maman and Ummu ta dawo daughter. Lol) "Now you are all messy why not muje s-h-o-p-p-i-n-g?" Tayi spelling dinshi feeling all freaked out and excited "Omi! God. That will really help. But na dade banje shopping ba" "Thats no problem" ta gaya irin ba komai ba alhalin itama tunda take bata taba fita wai shopping ba sede ko online shopping ko kuma a tura maids din mansion din da driver. "Amma tsaya kayancan" se tayi pointing kayan da Khameelarh ta fara hadawa "Me zakiyi dashi" "Just forget it okey?" "Fine. Wait guduwa zakiyi da?" "Ummu!" Tayi ihu "Okeyy!! Okeyy!!" *** Ummu ta saka wata black duguwan riga kwata-kwata be matseta ba kuma be mata yawa ba. Ta daura wata black veil irin babban nan. Khameelarh kuma ta saka wata white duguwan riga da digon blue se blue veil da fari-farin flowers a jiki (So i wanted to post the picture i selected and yaki posting so please kindly check the photo that represent the whole page) Fitowa sukayi after all the selfies and shirme suka shiga wata arninyan black and red Range Rover 2015. Sega bodygyard din Abbu ya nufo su. Khameelarh na hangoshi tace "Ummu sauri ki tada motan mu tafi dan Allah" Juyowa tayi ta kalleta "Ummu kiyi sauri abeg" ta kuma maimaitawa "Meye wai haka?" "Wancan mayan yanxin zece seya rakamu" tayi magana tana pointing dinshi Juyawa tayi taga me take nunawa. Se ta ganshi. Itama sauri ta farayi tana saka sit belt dan batasan ya rakasu yayi kusa dasu sosai dayake Ummu ta rugada ta kunna motan kawai se Khameelarh ta tura giya. Se Ummu ta taka motan ya fara tafiya da karfi ta fuzga motan ya fara gudu. Se suka saki dariya da sukaga guard din ya tsaya suka nufa gun gate. Guard din kowa daya tsaya a hankali ya taba abun kunnenshi yace "Don't open the gate" Yake gayan ma security din Daga mai kai kawai yayi dan suna kallon juna Horn din motan suka ringa danna ma scurity ya bude gate amma ya tsaya yana kallon. Khameelarh ta saka hannunta akan abun taki cirewa kara kawai yakeyi. Ummu ta saka hannu a kunne se dariya suke. Guard din ya karasu gun yayi knocking window gefan Ummu suka tsoarat baki daga suka kalla gun "F*ck" sukace a tare da suka ganshi. Hannunta saka ta bude mai window seta juya tana kallon streaght "Ma'am you know you are not suppose to go out by yourself after what happened" Ya gaya in an respective tone. Shiru tayi bata kulashi ba dukda tasan gaskiyanshi. Khameelarh kam se hararanshi takeyi ya lura amma seya basar kawai dan zaman lafiya. Magana ya kumayi da abun kunneshi seyace "Can i?" Yana alaman bude kofan "No!!" Khameelarh ta fada da karfi, begeta Ummu tayi seta daga mai kai bude kofan yayi ta fito. Wani security yazo ya budema Khameelarh nata itama ta fito suka bude masu baya duk suka shiga. Suna hada ido da guard din Khameelarh ta mashi dakuwa shi kuwa murmushi yayi mata kawai ta kuma sakar mai harara. *** Range Rovers ne guda bakwai suka gero duk bakake sena tsakiya ne wanda su Ummu ke ciki Red and black Guard dinne ke driving nasu duk motocin sunsha tint. Selfies din hauka suka ringayi. Tayi posting a insta tace Mother and daughter day. Wata mool suka isa Ummu da Khameelarh duk suka saka shades dinsu suka fito daga motan already paparazzi suna giransu ko saboda posting dinda tayinne suka duba location din oho! Guards 5 suka fito suka kare mutanan wajan harsu Ummu suka iya shiga. Guards biyu suka tsaya waje bayan wanda ke cikin motan se uku suka shiga cikin mool din suna binsu a baya. Manager mool din yana ganin wanda suka shigo ciki ya saka a kura mutanan wajan (Idan mutum beda wani matsayi se ata wulakantashi. Allah ka azurtamu. Amiiiin ooo). Ummu data lura da abunda akeyi ma mutane a wajan se ta saka baki tace ya kyalesu mana mutumin yaki Tace idan kuwa be kyalesu ba suma zasu bar mashi mool dinshi. Da haka ya kyalesu wasu masu zuciya suka bar wajan baki daya wasu kuma wanda basusan mutuncin kansu ba suka tsaya. Guards biyu suka dauko masu basket guda biyu suna binsu 'side to side' (Ariana grande ft. Nicki Minaj) Dayan guard din Abbu kowa yana biye dasu a baya. Khameelarh kowa rabin hankalinta yana kan wayanta ta dago kanta taga wanda ke binta da basket dinta se taga wani daban juyawa tayi tana duban wancan Guard din se ta ganshi yana biye dasu kawai a baya. Wani evil smirk ta saki tace ma wanda ke binta da naya basket din "Ni bakai nakeso ba wancan nakeso" tayi magana kaman da shagwaba tana nuna Guard din Abbu. Kallon juna suka farayi. Ummu tace "Meelarh wancan is not like a normal gaurd shi..." "No Ma'am karki damu duk abunda yaro keso shi ake bashi" Yayi magana yana amsan basket din yana mata wani murmushi "What the f*ck! Nice yarinyan?" "Meelarh shut up will you?" Ummu tayi mata magana. "Amma Ummu kinji abunda yace min" kaman zatayi kuka tayi magana "Ke kika saya da kudinki tunda kikace shi kikeson ya amsan maki" shiru tayi tana kunbura fuska kaman zata fashe. *** Shirme suka ringayi a mool din nan kaman ba gobe kuma tayima Guard din Abbu me suna Aleeyu wukanci kaman ba gobe. Se taga abu tace shi takeso idan ya dauko se tace na can sama takeso haka ze dauka ladder yahau ya dauko mata seta amsa ta kalla seta yamutsa fuska tace "Ya tsufa" ta gaya abun nan yafi dau 10 shi kuma seya amsa ya maida. Sunyi siyayya sosai ga haukan da suka ringayi a mool din nan mutanan wajan se daukan hotonan su sukeyi. Wata Baby Ummu ta gani a hannun wata mata Baby girl gata kyakkyawa ta kalla Khameelarh "Meelarh kalla Baby nan" Meelarh da a rayuwanta zata iya kirga daukan Baby da tayi. Seda ta amsa Baby nan ta ringa yawo da ita a wajan dukda bata iya rikewa sosai ba ta ringa daukansu hotona kowa. Maman Baby baki har kunne ana son Baby. "Who's a good girl? Who's a cute baby? Ohh. Yes you are. Yes you are" Khameelarh ce da Baby ita kowa yarinya se dariya takeyi. Check book Ummu ta ciro ta rubutama Matan check din 20,000 ta bata wai ta sayan ma Baby diapers se godiya take. Khameelarh kaman karta bata yarinyan taji itama Baby seda tayi ihu. Sunfi 3hrs a mool din nan se shirme sukeyi Ummu kowa ta bada kyautan kudi yafi 70,000. Daga bisani suka nufa inda ake biyan kudin shima nan sun dade ana shirme suka biya kudin aka kai masu kayan har mota suka shiga. Aleeyu kowa wato personal guard din Abbu yasha dakuwa a wajan Khameelarh yafi sau goma shi kuma seya basar. (Yarinta) A news kowa ko ina se labarin abun ake da kyautan da Ummu tayi. --Two weeks later-- R ayuwa ta kuma daidai a Lawiza family kowa ya kuma bakin aikinshi Khameelarh itama ta kuma makaranta itada El_Armeen dan shima tunda ta bari be kuma zuwa ba se suka kuma tare everything was back to normal for this family. Abbu kowa jiki yayi daidai babu wata matsala. Amma su Vice president (sunan daya tsana kenan) kullum sake planing yadda ze hallaka President yake. Abbu bawan Allah shi kowa ya yarda dashi tsakani da Allah be taba kawo negetive thought a zuciyanshi ba. *** Momy El_Armeen se ramewa take yaronta ya tambayeta meke damunta taki gayan mai ita abun duniya duk yabi ya isheta gashi sonda take mai bazata iya rabuwa dashi ba. Wani sa'in ma be kwana a gida yana wajan karuwanshi (Kugi tsohon banza). ♥♥♥

Share:

Saturday, 9 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 22 Sake rikota yayi ta kuma fizgewa da karfi ta cigaba da kukanta. "Manal am sorry okey?" Tayi banza dashi tana rike da cikinta har'a lokacin be dena mata radadi ba besan sanda ya rungumota ba seta kasa kwacewa tayi lamo a jikinshi tana cigaba da kukanta. "Am very sorry" He apologized again. "I had no idea" He added. "I just want my brother back" Ta furta a hankali *** --The nxt day-- Ranan ya kaman ran saturday karfe 6am Khameelarh tana dakinta tana daura wani jacket a waist nata se aka fara knockimg kofanta. Budewa tayi se taga Abbu tsaye da kayan sport a jikinshi kallonshi ta tsayayi na kusan 10secs se kawai ta tuntsire da wata dariya hadda rike ciki se dariya take mai. "You can laugh whatever you want i knw i look hurt" ya gaya yana gyara rigan jikinshi yana wani feeling kanshi. Sake tuntsewa da dariya tayi. "Ummu tasan kasa kayan nan kuwa?" She asked in between laughter. "A mana ta sani. Ni yanxin ma morning exceise zani na dade banje ba" "Kaidawa zaka?" "Dake mana" he answerd immidiately "Dabani ba wlh. Ka sume min a hanya na rasa inda zanyi dakai" tayi magana cikin zulaya "Amma kin rainani seriously" yayi magana yana juyawa. Da sauri ta fito daga dakin "Am joking okey? But seka cema guards dinka bazasu bimu ba dan asali saboda su na dena zuwa" "Naji" Kumawa dakin tayi ta dauko wayanta da earpiece ta saka suka sauko kasa. Guards din se gaidashu suke yana amsawa da fara'a a fuskanshi Har sunzo kofa zasu fita se wasu guards kusan biyar suna biye a bayansu. Juyawa yayi ya kallesu. "No kuyi zamanku" "Your Excellency am so sorry but i can't do that" Wannan bodyguard dinshi da always yana gaban mota idan zasu fita yake tare dashi yayi magana. Alama yayi mashi dakai dayazo. "Abbu" Khameelarh ta kira sunanshi da shagwaba. "Meelarh he is morethan a guard to me babu komai idan munje dashi" "I don't even exist" Personal Guard din Abbu added. Murmushi Abbu yayi ita kuwa Khameelarh sakarmai harara tayi seya mata murmushi a haka suka fito suna tafiya kawai suna hira. Sunkai har karshen layin kowa se daga masu hannu ake banda masu karasowa suna gaidashi har kasa shi kowa seya kai masu hannu su gaisa. Abun harya fara ba Khameelarh haushi. Dawowa sukayi Guard din yanacan baya yana biye dasu a baya da black shades dinshi da suit su kowa se hiransu suke. Khameelarh tayi masu selfie yafi 20 tun a lokacin tayi adding a story ta na Snapchat tayi posting kuma a Insta. "Abbu. Ummu ta gayan maka? Khameelarh ta tambayeshi tana cire earpiece din kunnenta. "Ta gayan min mene" ya tambaya kaman besan me take nufi ba. "Tana da ciki mana. You are acting as if you have no idea what am talking about" Seda yayi murmushi sannan yace "She is" Da sauri ta riko hannunshi tana zare ido "Da gaske?" "A mana" "God! Am freaking happy. Nima zan sama baby sister in ringa gyara mata gashi da pulishing nails nata" tayi magana kaman tana dreaming "Har kin san mace ce?" Ya katseta yana mata murmushi. "Ohh yess! Mace ce ma. But hw many month ne in fara shiri?" "Nima ban sani ba taki yarda na kira doctor. Tsaya wai bakijin kunya ko kadan am your father fah" "Kunyan me......." se kuma kunya yazo mata se tayi murmushi kawai. A haka suka iso gida suna dan hiransu gwanin sha'awa kaman ba Baba da Yarinya ba Suna isowa gida da ruwa aka fara masu sallama tun a gate. Suka shiga ciki gidan. Abbu ya wuce dakinshi itama ta wuce nata. Wanka tayi da saka shorts da tag top tayi ponytail da gashinta seta kuma ta kwanta abunta. *** Marwan yana zaune a bakin gadon Manal tana bata magana ta amsa tasha ya mika mata ruwa a glass cup shima ta amsa tasha seta mika mai a hankali tace "Thank you" Daga mata kai yayi yace "Rest a little ze dina ciwo" yayi magana a hankali gyada mai kai kawai tayi ta kwantar da kanta a kan pillo tana kallon celin din a hankali tace "I missed Abbah da Mammi so much" Dumm!! Kirjinshi ya buga se jikinshi ya fara rawa ya kuma kasa mata magana "I don't wanna imagine our future. I missed them so mch already. Bazan taba yafema wanda ya rabamu dasu ba" ta karashe maganan a hankali hawaye na zubu mata. He can't take it anymore. Kawai seya mike ya fita daga dakin, binshi tayi da kallo kawai. Yana shiga dakinshi buga kofan yayi da karfin gaske kawai seya zauna a jikin kofan yana jingine a jiki ya fashe da wani irin kuka kaman ba namiji ba. He is doing he's best to be strong but he don't think he can do it. Kanshi ya saka cikin gwiwanshi kawai yana cigaba da kukanshi. Allah kana ganin halinda aka sakamu a ciki karfi da yaji. Allah kana ganin abunda aka mana an maidamu marayu karfi da yaji. Allah make me someone so that i can Avenge for my parents death Ya Allah! Don't make them get away with what they did to my parent. Mammi, Abbah life sucks without you guyx! This life is nothing without your parent Allah make me strong so that i can support my sister. Ya Allah ka tayani rike alkawarin danama su Abbah. Hannunshi yabdaga ya kalla inda ya dinke M-card din wajan kawai ya shafa har'a lokacin yana zafi wajan. Hawayan idonshi ya share kawai se yayi wani murmushi I know am stronger than this. Mammi, Abbah am so sorry all this is my fault. It all started frm my mistake am so sorry. Am so sorry Se kawai ya kuma fashewa da wani kukan Mammi i can't do this i need you guyx by my side. I missed everything about you. I missed seeing your smile. I missed kallon fuskanki when you are freaked out about the president. I missed your face idan na gayan maki banada lafiya ko Manal batada lafiya. I want you guyx back. Abbah am trying to be the strong person you made me but i don't think i can make it. Haka ya ringa sambatu shi kadai yanayi yana kuka. Idan ya tuna happy moments they shared with his family se yayi murmushi can kuma seya kuma fashewa da kuka duk kuma yana jikin kofan ta cikin dakin. Can se yaji Manal tana knocking dakin a hankali tana "Ya'Marwan open up please" ***

Share:

Wednesday, 6 September 2017

RASHIN MAHIFA- CHAPTER 21 An kawo gawan driver daya rasu Abbu ya kalla gawan sedaya durkusa yayi mashi addu'a sannan ya saka a kira iyalishi a gayan masu bayan ya saka a tura masu kudade masu dinbin yawa kenan. "Ummu" Khameelarh ta kira sunanta a hankali cus tun sanda suka shigo batayi magana ba. Kallonta tayi idonta cike da hawaye amma batayi magana ba. Karasawa tayi gunta tace "Ummu meyafaru?" Kallonta kawai take se Khameelarh tayi huging dinta itama tayi huging nata back sun dade a haka daga bisani suka rabu. *** Vice president dake kallon abunda yake faruwa live a office nashi ji yayi kaman yayi ihu ya rungumo T.v dan har'an fara rabawa a news cewa president was attacked and an kashesu da first lady. El_Armeen yana ganin abunda akeyi a news dan haka ya dauka wayanshi ya fara masu video sanda ake hugs din nan se kuka Khameelarh take yayi posting a account dinshi na Instagram yayi adding a storyshi na snapchat sannan yayi posting a youtube inless dan 20mins it was brodcast that The President is alife wanda suka fara kuka already seya kuma murna. Vice president da yaga abunda danshi yayi posting he was very shocked ya kira numbershi be dade ba ya daga yake tambayanshi yana ina "Ina gidansu Khameelarh" ya amsa da murna a fuskanshi "And president da first lady are alife?" He asked in a low tone "Yess" ya amsashi a hankali. Kawai se yayi cutting line din. El_Armeen be damu ba ya cigaba da shirman video da yakeyi. Se dadi yakeji kaman Familyshi. --1hr later-- Gidan ya kayaye da hayaniyan mutane yan sannu da zuwa su Hawwatie suma sun iso dukkansu da Babbanta da Mammanta se yan mutanan da ba'a rasa ba abokan arziki. Su Vice President kowa ko lekowa ba'ayi ba. Brother Abbu wato Baban Hawwatiee wannan karan ma seda ya sake kuka na dadi cus shi ya rigada ya cire hope din sake haduwa da danuwanshi se gashi ya dawo. 8pm lokacin kowa ya watse harda El_Armeen shima ya tafi gida suna zaune a dining suna dinner Khameelarh se murmushi take tana kallon fuskokinsu Abbu as usual tana kusa dashi tanacin abinci. Rabonda taci abinci me nauyi tun randa suna lunch Abbu ya fadin nan seyau se murmushi kawai takeyi duk suka lura da ita se Abbu ya saki murmushi shima yace "Kewai meke damunki kaman tababbiya se murmushi kike ke daya" "Am freaking happy you guyx are back safe!" Ta gaya tana daga hannunta sama. Girgiza kai Ummu tayi tana dariya itama tana kallon abincin se jagwal-gwalawa take ko spoon daya ta kasayi. "Ummu abincin babu dadi ne" Khameelarh ta tambaya tana kallonta. Dagowa tayi tace "Banjin cin komai ne idan naci amai zanyi" kaman da shagwaba tayi magana kaman wata yarinya Ajiye spoon din hannunta Khameelarh tayi tana bude baki tace "Omi! God. Are you pregnant!" She asked very surprise and freaking happy. Da sauri Abbu ya dago ya kalleta shima da tambaya a fuskanshi. Vegetables din plate dinda ke gaban Ummu ta dauka ta watsama Khameelarh tace "You silly girl" kare fuskanta tayi "Seriously. Ummu are you pregnant?" Ta kuma tambayanta shide Abbu kallo kawai yake binta dashi. Mikewa tayi tana murmushi tazo tayi pecking Khameelarh tace "Goodnyt" bata jira abunda zatace ba ta haye sama. Juyowa Khameelarh tayi tana kallon Abbu "Abbu seriously is she pregnant?" "Wait. Ho... how will i know?" Ya mike shima ya gudu. Dariya kawai take masu ta maidasu kaman kakanninta ba iyayenta ba. Itama mikewa tayi ta shige dakinta. Abbu na shiga dakinsu ya tarar da Ummu a gaban mirror tana kallon cikinta. Murmushi ya saki sannan ya karasa gunta ya saka hannunshi a waist nata duk suna kallon mirror (basu girma su). Hannunshi ta rike yace "Is it true?" Kallon fuskanshi tayi ta gaban mirror se tace "I think so?" Tayi magana more like tana tambayanshi. Juyo da ita yayi suna kallon fuskan juna yace "Kinyi test ne?" "Nop" Seya saketa ya nufa inda wayanshi yake yace "Lemmi call the doctor yazo ya dubaki. I hope it's true" ya karashe maganan yana wani murmushi. Karasowa tayi gunshi da sauri ta amshe wayan daga hannunshi. "Abeg karka kirashi. Nasan am pregnant all it matter now is watanni nawane" ta karshe maganan kaman dadan kunya. Murmushi yayi se yayi huging nata yanajin dadi. "Allah ya raya mana twins" yayi magana yana shafa cikin. Murmushi tayi tace "Amiiin" a hankali. *** Marwan yana kwance a dakinshi wuraran 9:30pm yana kallon celin din dakinshi wani radadi zuciyanshi keyi kaman ya cire ya ajige a gefe guda. Manal kowa itama tana dakinta tanata kuka cikinta yana mata ciwo daga baya ta mike tana rike da cikin ta nufo dakin Marwan ta fara knocking mai kofanshi. "What!" Ya buga mata tsawa. Batayi magana ba seta bude kofan ta shigo tana kuka tace "Ya'Marwan cikina yana ciwo kaman ze fashe" a hankali take magana tana kuma rike cikin da dukka hannayanta. Ko juyowa ya kalleta beyiba yace "Do i look like i care?" (Omi! God i seriously hate the present Marwan i want our Marwan back) Kallonshi ta tsaya yi da mamaki na kusan 2mins shi bema san tanayi ba kawai seta juya ta hango wani flower vase akan side-drawer wurgi tayi dashi gefe guda seya fadi ya tarwashe ta kuma sakin kuka ta fice a guje dakinta ta kuma ta fada kan gadon ta cigaba da rera kukanta. Da sauri ya dago ya kalle abunda tayi se yaji ta bashi tausayi He knows he is giving her a had time but he don't freaking care 'Amma kasan you are all she got! And you made a promise to your parent you will keep her safe. Then why are you doing this? All that is happing is not her fault. She is affected to it also you know' Wani gefe a zuciyanshi kemai wannan magana shiru kawai yayi. Kukanta kawai takeyi kawai zuciyanta seya fara raya maga wani abu. Mikewa tayi ta nufa gun labulan kofa. Ina irin abun nan da yake rike labule? Tou shi ta zaro dukka biyun na gefan ta dauresu dukka seta dauka kujeran mirror ta ajiye a tsakiya dakin wurin fan. Tahau ta fara kulle igiyan a jikin celin fan din tanayi tana kuka. Kawai se Marwan ya shigo dakin. He was very shock daya gane abunda takeda niyanyi, ita batamasan ya shigo ba se share hawaye takeyi tana kulle igiyan. "Manal!!" Ya kwalla mata kira da karfi. A firgice ta juyo ta kalleshi. Kawai seta kuma fashewa da kuka ta cigaba da abunda take. A zuciye ya nufa inda take da karfin gaske ya fizgota dagakan kujeran ta fadu akan hannunshi ya dauketa da wani wawan mari. Kurma ihu tayi. "Tou ka barni na kashe kaina mana tunda kai ka tsaneni. I regreat living them in the first place. I wish you were the one that is dead. I freaking hate you, mena maka da kakemin haka? I hate you!" Ta durkusa a wajan tana wani irin kuka abun tausayi ga shedan hannunshi a fuskanta. Wani irin tausayinta ne ya kamashi seya durkusa shima ya rungumeta "Am so sorry" ya furta a hankali "Let go of me!!" Ta gaya a tsawace tana janye jikinta daga gunshi. ***

Share:

Monday, 4 September 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 20 Sorry not sorry- Demi lovato Manal na kwance a dakinta idon nan ya kunbura yayi kato kaman zasu fadu se kuka take. Dashi take kwana dashi take tashi har muryanta ya dashi gashi rana daya kawai ta wani rame Marwan yayi-yayi tace abinci take se kuka kawai takeyi. Shima ba'a barshi a baya ba ku yaushe yana kan sallaya yana mata addu'a yana kuka duk sun rame se hanci da idanuwa daya rage. Wajajan karfe 3pm duk suna dakunansu kowa na kan gado ba bacci suke ba. Manal na sana'arta shi kowa rabi bacci yake rabi kowa idonshi biyu. Yanata tunanin Mammi. Akwai ranan da take bacci a dakin ta yazo wucewa ya hangota seya shiga ya dauko wani cream dinta ya shafa mata a hannu seya dauka tsinken tsintsiya ya shafa mata a kunne seta saka hannun cream din zata bige abunda ke wajan se kawai ta bata fuskanta da cream din ya ringa mata dariya, ita kuwa mikewa tayi da sauri ta rankwashe kanshi ya mike a guje ya bar dakin. Besan sanda wani hawaye ya fara zubu mashi ba kawai seya fashe da wani irin kuka zuciyanshi wani irin abu take mai kawai seya fara ajiyan zuciya a hankali. Kaman cikin mafarki se yaji wani irin kara a parlo a birkice ya mike zaune yana sake jin abun ya tabbatar daga parlo ne a tare suka shiga parlo shida Manal seda suka hada ido dukkansu idonsu yayi jajir. Se suka maida hankalinsu inda suke jin karan. Wajan T.v ne yana kawo red seya dauke. Motsowa Marwan yayi kusa dashi ya taba remote din kawai se fuskan matan ya fito. Kana ganin fuskanta kasan bad news ta kawo masu "Hey Manal. Marwan ya kafanka?" A hankali take magana. Shiru yayi be kulata ba can seya ce "Ina Abbah?" Seda ta kalla Manal sannan ta kalla Marwan a hankali ta fara "Kullu nafsi za'ikatul maut....." Rike kai Manal tayi ta kurma wani uban kara na kusan 50secs se kawai ta saki wani dariya ta zube a wajan. Kafin kace me shima Marwan ya sume! Babu me taimakawo kowa gashi su kadai ne a gidan. Hawaye kawai matan ke zubarwa cus ba karamin tausayinsu takeji ba ace yara dasu su rasa iyayensu dukka a lokaci daya an maidasu marayu karfi da yaji. da sauri ta kashe video call din. Befi 30mins ba se gata tazo har'a lokacin suna sume dukka, tazo itada wannan doctor da Acting president ke aiki dashi wanda ya duba sanda Abbah ya rasu ashe shima aikin su daya da matan da take taimakawa su Marwan wato Secret Agents Of Nigeria (SAON). (I just made it up) suna aiki ne a boye bana Government bane wanda ko President himself be sani ba aikinsu akan mutane da suke neman taimako ne shine suke taimaka masu. A gadon da aka kwantar dasu anan aka maidasu. Doctor ya duba Manal batada wani damage akai cus dariyan da tayi se matan tayi tunanin ta sama matsala ne. Marwan kowa kaman ze tashi se wani nunfashi yake sama-sama kaman za'a cire mai rai (dukda bansan yadda ake ba). Dan haka aka dubashi aka gano ciwon zuciya yanason ya kamashi yama fara kamshi and he is too yoing to have it. Seda aka mai dressing kafanshi sannan ta rubuta mai wani note kusa da gadonshi akan idan ya tashi yasha magongunan data bar mashi a wajan shida Manal sannan suka wuce. Bayan ta masu alluran samun hutu. *** Acting president ke zaune sojojin daya aiki suka dawo suke cemai sun kashe Marwan da Manal tunda shi wawa ne seya yarda harda murnan shi. Wai ya gama da family su shikenan. Abbu yanxin ya samu sauki sosai yana iya tafiya yana komai dakanshi cus jininshi baki daya aka chanja mai in-case idan akwai guban a jikinshi. An yanke masu nan da two days zasu kuma gida amma Ummu tace kar Doctors din su gayan ma kuwa sede kawai a gansu a Abuja. Hatta Khameelarh itama batasan da zancan ba. *** Rayuwansu Marwan ya jagule ya chanza shide ta nashi gefan jira kawai yake mutuwa tazo mashi dan kusan sau uku yana kukarin kashe kanshi Manal na hanashi na farko wuka ya dauka ya daura a hannunshi ze yanka jijiyanshi ta ringa kuka tana ihu wai idan ya mutu ita kadai zata rage haka ya fasa. Rayuwansu de ta kuma wani iri abu kaman a film ya riga ya daukan ma kanshi alkawari se yayi avanging death din iyayenshi koba yanzin bane seyabi duk wanda keda hannu shima ya kasheshi sede shima azo a kasheshi. His heart is now full of darkness, His cute smile is nomore ya tsana kuwa a duniya ya tsana family President cus yana ganin hadda laifinshi. And the very man he will never forget in his life, mutumin daya fara sakashi a halin dayake ciki, mutumin dayayi sanadiyan rabuwansu, mutumin daya kashe iyayenshi. Kullum seya dauka M-card din ya kalla. Hatta Manal bema magana kullum yana cikin dakinshi be damu da halinda take ciki ba. He now don't care about anyone he hate the freaking world he hate all the people that are living in it. T.v dake dakinshi tuni ya fasashi wayan ma tuni ya tarwatsashi. Yanzin haka zaune yake a bakin gadonshi a kasa da scissors a hannunshi ya hudeshi kawai seya daura a hannunshi ya yanka ku alaman jin zafi beyiba. M-card din ya dauko a saka a cikin wani dan karamin abu kaman paper amma ba paper bani kawai seya tura cikin naman hannunshi (O. M. G) allura ya saka ya dinke wajan. Wajan yayi jajir banda jinin dake zuba, idonshi yayi jajir kana kallonshi kasan yanajin zafi. Goge jinin yayi ya zama M-card din yana cikin naman jikinshi kenan (God!). Marwan ya chanja sosai kaman bashi bane idan yaji ciwo Mammi tazo goge mai ake kokowa dashi yana ihu amma shine ke yanka naman jikinshi yau kuma yana nunawa ko a jikinshi. Fuskan nan a murtike kaman bashi bane wanda duk sanda ka daga kanka zakaga yana maka murmushi ko yaushe akwai murmushi dauke a fuskan nan. Gashin nan is a mess kaman bashi bane kullum yake brushing gashinshi sau uku ko biyu a rana. A yanxin be tausayin kowa besan kowa ko matan datake taimaka masu idan ta masu requesting video chat se yayi disconnecting sede idan Manal na wajan ta dauka. Manal kam yanzin tayi tawakkali ta fauwalawa Allah komai. Kullum tana cikin ma iyayenta addu'a, kullum tana masu addu'a baki daya Allah yasa su hadu baki dayansu a cikin gidan Aljanna (Allah sa baki dayan mu mu hadu acan. Amiiiin) Dukda ramewan da tayi kaman wanda ta shekara tana ciwo be hanata boye damuwanta ba saboda Marwan. Cus taga alaman he's more affective than her, ta fara damuwa da yadda Marwan ya kuma tashin farko. Wani sa'in zata girka masu abinci takaimai har daki ko kallonta bayayi se bayan ta fita ze fito da plate din ya ajiye mata akan dining. Rabonda taji muryanshi tun randa yace 'Ina Abbah' Randa matan nan ta kirasu kenan take gayan masu shima Abbah ya rasu. Tou tun ranan bata sake jin muryanshi ba. Kota mai magana sede ya bita da ido kawai ya kuma so silent ko abinci bayaci. Haka zata shiga daki tayi kuka-tayi kuka se tanajin mutuwan iyayenta yazo mata sabo tal. RASHIN MAHAIFA sucks! Kullum abunda take fada kenan. Gashi an kullesu a gida babu daman fita kuma babu waya. T.v ne kawai abokin hiranta ita kam. Babu ranan da baxatayi kuka ba, babu shi. Ya rigada ya zaman mata jiki, tayi sau uku sau hudu a rana se taji dadi a ranta. A duk lokacin da tayi wani abu daze tuna mata da Abbah da Mammi ana wajan zata kwanta tayita kuka harse ta gaji dan kanta ta tashi cus babu me bata hakuri. Gashi matan nan bata taba zuwa su hadu ba! *** Yau karfe 2pm Allah ya saukar dasu Abbu a Nigeria. Suna sauka Airport din were very surprised da suka ganshi. Benx guda goma aka kawo masu suka shiga dayake an saba nashi yana tsakiya yau se Ummu tace su shiga muta na biyu cus babu wanda zeyi tsammanin yana ciki! Acting president yana zaune se wani ya kirashi yake gayan mai Presisent ya dawo. Kafin yayi magana se yaga ana nunawa a news. Wani irin wulli yayi da wayan hannunshi ta tarwatse, ya zubar da dukka takardun table nashi mikewa yayi ya nufa wajan T.v shi, kujera ya dauka irin me karfe a wajan kafan nan kawai ya buga a babban T.v nan yana ihu seya fashe. Ya dade yana hauka shi kadai a office dinshi. P.A shi tana jinshi babu daman ta leko se'a koreta bata shirya rasa aikinta ba shiyasa ta shareshi idan ya gama tasa a gyara wajan. Wani shawara ne yazo mai kawai ya dauka Telephone din office dinshi yayi dailing wani number seya saka a kunne. Befi ringing uku ba aka daga. "Yes. Inason ka saka snipers uku a yanxin nan su tarwatsa min motan da President ke ciki, kasan wanne ne koh? Tou na tsakiyan ne yake zama a ciki. A ta harbinshi harse motan ya kama da wuta one more thing idan aka kamaku if any of you dare to mention my name y'all dead!" yana kaiwa nan ya kashe call din yana ajiyan zuciya kaman zaki se'a lokacin yadan ji dadi a zuciyanshi. *** El_Armeen da Khameelarh as always suna zaune a parlo shi tun sanda su Abbu suka bar garin gidan ya zaman mashi wajan yini wani sa'in se 9pm yake tafiya gida har Mommynshi ta sabama. Kowa na danna wayanshi cus har Khameelarh tayi sabon waya (aikin kudi) se El_Armeen yayi saurin dagowa yace "Ina remote yake?" Ko kallonshi batayi ba tace "Jirani na naimo maka dan rainin hankali kawai" tsaki yaja ya mike ya dauka yakai news ae kowa seyaga motansu Abbu an hada convoy dukka motan baki kuma ko wanne akwai karamin flag din Nigeria a gaban motan. Ihu ya saki yace cewa "His Excellency is back!" Wani irin dagowa Khameelarh tayi ta kalla T.v ta tabbatar motocin Abbu ne wani ihu ta saki itama batasan sanda tayi wulli da wayanta gefe guda ba ta rungume El_Armeen sunata ihu basu ma san sunyi ba. Kawai se Khameelarh ta fashe da kuka, a rude ya rike mata kafadanta ya fara tambayanta "Meyafaru kuma?" Batayi magana ba se hawayen dake kwaranyo mata tanayi tana murmushi "This the happiest day of my freaking life!"  Ta gaya da karfi hawaye na zubuwa amma tana murmushi. Dariya yayi shima ya kuma rungumeta. Haka suka zauna suna kallon yadda motocin ke tafiya a hankali yan garin se ihu ake ana dagama motocin hannu. Samari da yara bin motocin suke aguje suna ihu *** Suna cikin motan Ummu na rike da hannun Abbu se kallon titin suke inda mutane ke kallon motan tsakiyan anata daga mata hannu cus dukkan motocin akwai tint and is very dark so baza asan wanne ne yake ciki ba. Se murmushi kawai sukeyi. Dayake  su hudu ne a motan da suke ciki. Da driver se personal bodyguard din Abbu wanda Abbu ya yarda dashi sosai cus shi sau dayawa idan suna tare da Abbu idan aka kawo mashi hari yana sacrificing kanshi ya daukan ma Abbu bullet shiyasa ya yarda dashi sosai. Ko sanda suke hospital din shinema yake tsayawa a bakin kofan dakin ko yaushe duk wanda ze shiga dakin seya nuna mai ID-card dinshi na doctor kafin ya shiga. Se Ummu da Abbu Wasu snipers uku na hango akan wani building suna labe kowa da bindiganshi suna pointing motan tsakiyan seda gabana ya fadi cus i don't want to witness this moment. Harban motan tsakiyan suka fara ta ko'ina mutanan wajan aka fara tsarwatsewa anata ihu. Salati Ummu da Abbu suka farayi ta sake kankame hannunshi shi kowa yayi saurin dukar da kan Ummu. Dukka motocin suka tsaya wanda ke bayan suka fara juyawa na gaban kuma suna tsaye se Bodyguard din Abbu ya fito. Abbu nata cemai ya dawo amma be saurareshi ba ya kalla driver "Make sure you take them home save!" Yana gaya yana gyara bindiganshi Daga mai kai driver yayi kawai ya tada motan suka fara tafiya yayima na bayan alamana suma su tafi suka fara tafiya shi kowa daga bindiganshi yayi ya seto sniper daya aekowa cikin sa'a ya samoshi. Tuni motan ya faraci da wuta Allah ya taimaka ma mutum dayane a ciki amma ya rigada ya kune. Kafin dayan ya ankara har'an samoshi shima sauran guda daya seya mike ze gudu, bodyguard din ya fara binshi. Khameelarh suna kallon T.v suka fara ganin yadda ake harbin motan da suka tabbatar Abbu na ciki. Mikewa tayi da sauri hannunta a baki gama kasa komai tana tsaye a haka kawai shima El_Armeen ya tsaya yama kasa yin komai kawai yana tsaye. Bodyguard din ya tare sniper dayaga there is noway out kawai seya daga bindigan ya harba akanshi a cikin 2secs da sauri ya karasa gunshi amma har rai yayi halinshi. Chaje jikin sniper Bodyguard din ya farayi dan kuze sama wani abu a ciki. Amma be sama komai ba dan ko ID-card dinshi babu a jikinshi. Hakama sauran babu komai a jikinsu. Tuni an kira taimako harsun iso an fara kashe wutan an dauko gawan driver dukda ya kune anyi gidan President dashi cus ya ganshi. Snipers din kuma an debesu dan ayi bincike ko su waye and waya aikosu. Khameelarh kowa har'a lokacin tana tsaye da hannunta dukka a baki cause bata masan me zatayi ba. Driving din became so quite Ummu was in shock cus tunani take da sune a cikin motan Abbu shima haka. Dukka sauran motoci taran suka isa gidan a tare. Kawai se su Khameelarh sukaji hayaniya a waje ana shigowa da motoci. El_Armeen ne yayi kokarin lekawai kawai ya hango Abbu an bude masu kofa yana rike da hannun Ummu duk ya rame. "Khamee......larh!! Kha....." seya kasa karasawa yanata pointing window kawai. Ita tama kasa juyowa seya sake cewa "Ab...bu!! Kham..eelarh!" Da sauri ta juyo tana kallonshi yana pointing window idonta jajir. "Abbu!! Da Ummu!!" Ya gaya daidai wannan karan" A guje taje wajan window kawai ta hangosu sun fito anata masu sannu da zuwa Ummu se hawaye take. Fitowa tayi a guje tana ihu "Abbu!! Ummu!!" Da karfin gaske tanayi tana gudu tana kuka. A tare suka dago suka kalleta, gudu kawai take harta iso inda suke seta tsaya a hankali tace "You guyx are alife" kaman tana magana da kanta kawai ta fashe da wani irin kuka ta fada jikinshu a tare ta rungumesu. Huging nata back sukayi amma har'a lokacin Ummu was in shock, sun dade a haka seta sakesu. Abbu yajasu suka shiga cikin gidan baki daya. Khameelarh ta kalleshi tace "I thought you guyx....." se tayi shiru kawai "C'mon my baby i missed you" Abbu ya fada yana yana bude hannunshi dukka. Fadawa tayi a guje ta sake rungumeshi. Duk abun nan El_Armeen yana kallonsu yana murmushi kawai. 💋💋💋

Share:

Thursday, 31 August 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 19 Look what you made me do - Taylor swift Ashe video call dinda sukeyi da Marwan ashe Mustie yana tracing location nasu ne. Aekowa ya gano inda suke. Tou bayan Acting President ya kashe call din seya kira sojojin wanda ya tabbatar suna area ne ya gayan masu 'kawai su kashe su' Saboda tsananin firgitan da tsoran da yayi tsayawa kawai yayi a wajan a cikin seconds dinda yake tsaye besan yadda kanshi yake ba yana tsaye ne kawai kaman statue in that very moment he felt kaman be duniya besan ku kuka zeyiba ko ihu besan ku daukan Manal zeyiba ku yaje ya nemo Mammi he just felt kaman soul nashi has left his body he felt the world has turn into something else. At that moment he just wishes be taba zuwa duniya ba to even witness the worst minutes of his life. He felt he hated the whole world he hated his life he hated everything. Se bayan kusan 20mins yana tsaye a wajan se'a lokacin wani irin ihu yazo mai. Ihun dabe taba tsammanin ya iyashi ba, ihu kawai yake kurmawa cus besan abunda zeyi ba idan bashi ba. Ga kanwarshi a kwance a titi gashi an kashe mahaifiyarshi a idonshi kuma bema san koh Abbah nada rai ba. Yana tsaye a wajan kawai seyaji harbin bindiga a area da suke in that moment all he wanted was a kasheshi shima dan haka bemayi yunkurin guduwa ba ko wani motsi hannunshi de yana kanshi ya rike yana durkushe a gaban Manal. Harbin bindiga ake ta ku ina besan sanda yaji wani azaba ba a right leg nashi kurma ihu kawai yayi (sun sama kafanshi) a cikin 3secs ya fice daga hayyacinshi kawai shima seya sume. Motan sojoji ne guda daya keta harbinsu wanda ke dauke da mutane hudu daya na driving so uku ne masu bindiga a hannunsu. Kawai daga sama sega wasu black mota sun iso wajan, se wasu mutane kusan su goma suka fito daga ciki kowa dauke da bindiganshi kuma fuskansu a kulle dukkansu se suka fara harban motan sojojin ta ku ina har suka sama wani soja anan take ya mutu. Sojojin suna ganin haka suka fuzga motansu suka gudu (kunsan halin sojan 9ja Lol) Daya gada cikin wanda sukazo masu black din yayo gunsu Marwan se naga ya yaye abun fuskan ashe na mace ce. Ta saka dan yatsanta gudu biyu a wiyan Manal seta cire ta saka ana Marwan. Kawai seta kalla raguwan mutanan se suka fito da gado guda biyu aka sakasu a kai suka lodasu a cikin motan suka bar wajan. Har'a lokacin bag-pack din Marwan yana bayanshi be cire ba. *** --Hours later-- Marwan ya bude idonshi a hankali se kawai yaga ko ina haske fari tal ko digon baki babu maida idonshi yayi ya kulle. Cus shi a tsammaninshi ya mutu ne yanama aljanna. Kusan 3mins seya sake bude idon yana kallon saman celin din ya dade a haka seya kalla gefe kawai ya hango Manal a kwance akan gado, yunkurin mikewa yayi kawai seyaji wani azaba a kafanshi kaman an yanketa kumawa yayi ya kwanta yana damke ido dan zafi. Yaye zanin dake jikinshi yayi se yaga irin an gyara mashi kafan ne an nannade da farin bandage, hannunshi ya dago ze taba kafan se yaji abu na rikeshi ashe karin jini ake mai cus yayi loosing jini dayawa furze abun yayi niyanyi se yaji wata muryan mace daga samanshi tace "I won't do that if i were you" abunda ya daukan mai hankali kenan ya daga kai yana neman ta inda yaji murya se aka sake cewa "Up here!" Ya kuma daga kanshi ashe a T.v take a gefan jikin bango kura mata ido yayi kawai beyi magana ba ita kuma tana mai murmushi can tayi breaking silent din tace "Ka bari seya kare seka cire" juywa yayi ya kalla jinin saura kadan ya kare For how long have i been here? Abunda ya fara tambayan kanshi kenan seta katseshi by saying "And the man that is trying to kill  you thinks you are dead" Da sauri ya kalleta "Yes! So na gama settleing maku komai for now zaku zauna anan gidan it has everything you will need to survive for two months and idan kuna bukatan wani abu you can inform me so babu inda zakuje anan zaku zauna harse abu ya kwanta na rigada na gama maku komai after two months zaku tafi New york ku gama karatunku seku kuma zaman can har abada cus is more saver for you guyx...." "Who are you?" Ya katseta Seda tayi murmushi sannan tace "A guardian. Idan kuna bukatan wani abu ga remote din can you can contact me..." "Abbah fa shima ya mutu?" Ya kuma katseta yana magana a hankali. Seda tayi ajiyan zuciya sannan tace "For now yana raye so metion dinmu kenan mu taimakeshi kafin ya kasheshi" "How do you know about what was happing to us?" Ya kuma aika mata da wata tambaga "Lets just say my life is dedicated to your family so duk abunda kuke ciki a family ku ina sane dashi..... For some reasons.. don't ask!" Ta dakatar dashi danta ga alaman yana son ya kuma mata wani tambayan. "In time zaka sani" bata kuma wani maganan ba tayi offing computer. Maida kanshi yayi kan pillo kawai se yaji wasu zafafan hawaye suna zubu mai wanda se'a lokacin suka zo mai. 'Yanxin shi kenan ya kashe Mammi? Shikenan? Habah! Habah! Wannan abun yayi yawa. Yayi yawa fisabillilah. Yayi yawa!! Ya Allah laifin me na maka da zaka jarrabani da wannan? Yanxin shikenan Mammi ta tafi ta barmu. Ta tafi? Na shiga uku! Ya Allah ka dauka rai na yanxin! Ya Allah banson duniyan! Na gaji! What did she did to deserve this? An horrable death which besan ma ko zasu mutunta gawanta ba. Ohh Allah. Ohh Mammi dan Allah ki dawo! Ki dawo naji dumin jikinki once more. Ki dawo and hug me one last time this life is zero with out you! Mammi please come back and stay with us' ya karashe in a low tone. Kawai se hawayen suka cigaba da zubu mai kaman fanfo. Manal ce ta bude ido a hankali tana addu'a. Tou addu'an ta yaji tanayi ne ya sashi saurin kulle ido yana baccin karya cus besan meze ce mata ba. Tana gama bude idon ta karema dakin kallo tukun seta juya ta hango Marwan yana bacci a lokacin dukka abunda ya faru ya fara dawo mata. Kawai seta kurma uban kara tana "Mammii!!" Shi kawai take maimaitawa "Na shiga uku! Mammi karki tafi dan Allah karki tafi ki barmu a haka! Mammi" seta sake sakin wani irin kuka wanda bata taba yin irinta ba. Duk abunda take Marwan yana jinta amma yana danna zuciyanshi akan karya kulata har se taji sanyi kadan tukun. *** Sanda aka fitar da Mammi daga dakin da suke tareda Abbah seda aka daureshi kaman kare. Yana zaune a daure kawai yaji harbin bindiga wani wawan shock ya sameshi ya kasama komai. Yana zaune a haka ko motsi ya kasayi cus he don't want to beleive Miat dinshi aka kashe (mammi). Kawai seyaga an fito da ita cikin jini. Yana daga kai ga kallesu kawai se zuciyanshi ta buga a take a wajan Allah ya dauka abunshi. On 29th August Allah yayiwa Alhaji Mansoor da Hajiya Miat rasuwa! 😭😭😭😭 The day Marwan and Manal will never forget in there live!. Wani gaye ne a cikin yaran Acting president ya leko dakin yaganshi. Ya duba nunfashin shi yaji shiru ya duba bugun zuciyanshi shima shiru. Da sauri ya fito ya dama Acting President ya gayan mai aka kira doctor yana dubawa yace Allah ya mashi cikawa. "Easy!" Kawai yace yayi ficewanshi. Amma abunda yayi wanda ban taba tsammanin yanada raguwan imanin nan ba shine. Ya saka a suturtasu a kaisu makwancinsu na gaskiya. Aekowa haka akayi se gashi ma anyi rasuwa kusa dasu saboda haka gawawwaki uku aka hada akayi masu sallah kuma gashi sunyi mutane sosai daga nan aka kaisu makwancinsu na gaskiya 😭😭😭😭 (Mehn!! I can't take dis aswr!) *** Tayi kukanta ma'ishi da Marwan yaji baze iya yin shiru ba seya kira sunanta a hankali "Manal" Shiru tayi dukda tajishi "Addu'a kawai zaki mata" yayi magana a hankali. Batayi magana ba se shirun datayi. Shima be kuma magana ba, Suna kwance a wajan can se Manal tace "Waya kawo mu nan?" "Wata matace" ya amsata ba tareda ya kalleta ba "Why?" "Nima ban sani ba" "When are we living?" "Bazamu bar gidan nan ba!" Da sauri ta kalleshi da mamaki "Why?" "Cus nan yafi mana and it's saver" "I see! You do trust her right?" "Yeah" "Hmmm" kawai tace dan ita haushin shi takeji gabadaya cus laifinshi take gani. --Hours afterward-- Lokacin jinin da ake karama Marwan da ruwan da ake karama Manal ya kare dan haka Marwan ya cire masu ya lura da kallon da Manal kemai amma ya basar.kafan wani azaba yake mai, kawai a gefan gadon seyaga wani sanda dan haka seya dauka amma still yana dingishi. Bag-pack nashi ya dauka ya fito daga dakin itama ta biyoshi. Wani parlo suka gani babban gaske ga T.v, A.c, fridge da sauransu ya hadu karshen haduwa. Wani kofa ya gani ya shiga se yaga Kitchen ne ba wani babba bane amma duk abunda za'a bukata yana ciki sega wani kofa a cikin kitchen din store ne! Kayan abinci ne kala-kala daban-daban bayan sun fito akwai wani bed-rooms guda biyu dukka akwai closet a ciki tanan ne kowa ya gane dakinshi saboda kayan ciki sannan akwai toilet a ku wanne seya fito waje tsakar gidan empty babu komai se flowers amma bangon gidan dogune sosai ga gate din a kulle yake gadaya yadda babu wanda zece akwai mutum a gidan sannan akwai generator da solar a gidan. Kai gidan de babu abunda babu a ciki wanda mutum zeyi rayuwa dashi na tsawan 4 months. Duk zaga gidan da yakeyi Manal na binshi a baya. Juyowa yayi ze kuma se yaga wata kofa karama a kusa da inda aka ajiye Generator yana lekawa kawai yaga wata karamar Gym ne. Kullewa kawai yayi ya fito. Manal tuni ta shige parlon ta fashe da wani kuka. Shi kowa zama yayi a jikin wajan flower kawai ya saka kanshi a gwiwanshi kawai. * ** Khameelarh take waya da Ummu se zabga mata shagwaba takeyi wai yaushe zasu dawo "Meelarh na gayan maki yana sabon sauki sosai xako ganmu For now mungode ma Allah" "Tou Ummu. Why not na biyo ku kawai" "Aa Meelarh you have to stay and take care of the house okey?" "Okey" ta amsa idon nan ya cika da kwalla she really do missed them alot gashi kullum tana gida makarantan ma ta ajiyeshi a gefe harse Abbu ya dawo zata kuma itama. Ko sallama bata mata ba tayi hanging up ta kwantar da kanta akan pillo ta tana facing poster data manna a dakinta kawai seta mike ta baroshi. gaban mirror ta tsaya ta mannashi ajiki se tayi wani murmushi. --The nxt day-- Wuraren karfe 2:24pm El_Armeen yazo gun Khameelarh ya dade yana parlo yana jiranta bata sauko ba kuma wayanta is off. Dan haka seya mike ya nufa saman, dakinta ya shiga ya tarar da ita tana shakar baccinta girgiza kai yayi kawai ya juyo ze fito kawai seyaga hotan data manna a jikin mirror ta. Barowa yayi seya kuma girgiza kai, gun gadon ya nufa yana bubbuga kafanta da karfi. A furgice ga tashi tana neman hanya goduwa dantasan ita kadaice a gidan se kawai taga El_Armeen a tsaye akanta da sauri ta jawo bargonta ta kulle kirjinta dashi cus vest ne a jikinta "Excuse you!" Ta gaya tana mai wani kallo. "What is this?" Ya daga poster. Mikewa tayi da sauri ta kwace a hannunshi seta nufa gaban mirror ta akan kujeran jiki ta dauka Kimono dinda ta saka jiya ta saka sannan ta juya ta kalla El_Armeen wanda ke binta da ita tace. "First. Be kamata kana shiga dakin mace ba haka kawai and Second this.." seta daga poster "Is my privacy you are not allowed to look at it!!" Ta karashe maganan tana dan daga muryanta shi kawai kallonta yakeyi can yace "He's a criminal you know" "And i don't believe it" tayi magana tana dawowa gun gadon still poster yana hannunta "Don't tell me you have falling in-love with him" "Ohh noh! Am crushing on him there are differnce you know" Seta kalla hotan tayi wani ajiyan zuciya tana murmushi "Loser!" Yace mata yana zama a kujeran mirron ta "Dick-head" ta rama "Biatch" "Bitch" "Ass hole" "Moda- f*cker" ya kuma mata seta kalleshi ta mike har gabanshi taxo tace "Screw you! Banda lokacinka you ruined my romantic dream with my prince charming" sannan ta jawo wayanta ta sauko kasa. Shima mikewa yayi ya biyota "Amma kinsan kisan kai yayi koh?" "And that's what i like about him beside i don't believe someone cute like him will kill an innocent soul so go F*ck yourself!" Be kuma mata magana ba ya sama waje ya zauna yana chanja channel da remote. Itama wayanta take dannawa daguwa tayi ta kalleshi tace "Kasan wanda yayi liking post dina yanxin a insta?" Banza yayi da ita dan haka se tace "Kai wlh banza ne da wani katon kanka a wajan kaman katon Rock! Freaking loser!" Still ko kallonta beyiba ya kwantar da kanshi jikin kujeran. Abun ya kuma kuna mata rai batasan sanda ta wullu mai da wayan hannunta ba kawai seya buge wani flower vase (Na maman Ummu ne wanda dashi aka kaita dakinta lokacin data aura Babban Ummu so Ummu na masifan jidashi cus shine kadai memory Mamanta da take dashi ko maids din gidan basu tabawa kullum dakanta zata goge kayanta) Faduwa yayi kasa ya tarwatse into pieces ga wayanta shima ya bare. Da sauri El_Armeen ya mike zaune yana kallon abunda tayi ita kowa hannu kawai ta saka a baki dukka biyun tana kallon vase din cus tasan se ran Ummu ya baci. Kallanta yayi ya kuma kallon abunda tayi cus shima yasan vase din Ummu na sonshi. "Kwatama! Kin bani aradu. Bari kiga na wuce gida i wasn't here when it happend" ya karashe yana mikewa Tagade da gaske yake guduwa zeyi seta fara rokanshi dan Allah ya tsaya suyi gluing dinshi dakyar ya tsaya. Sun dade suna abu daya amma yaki tsayawa se El_Armeen yake tou su duba store ko za'a sama irinshi. "Hmmm! Kaima kasan baza'a sama ba. Wlh it's all your fault!" "My fault?" Ya tambayeta yana nuna kirjinshi "Lol! You are welcome" He added trying to exit the room. Da sauri ta riko hannunshi se kuma ta sake. "Habah please naa.. you can't just work away am sorry okey?" (Lol daman Khameelarh tana bada hakuri? Am in shock) Dakyar ta shawo kanshi ya dawo se suka tattarashi suka saka a wani abu akaje store aka boye a ciki se suka dauko wani vase a bakin stairs sukayi replacing nashi! Se'a lokacin ta tuna da wayanta a wajan ta dauka ta hada screen din ya danyi craking kadan kashewa kawai tayi ta ajiye a karkashin pillo couch din. ♡♡♡

Share:

Monday, 28 August 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 18 Khameelarh ce ta fito daga wanka daga ita se towel a jikinta ta nade gashin ta a cikin wani towel din. Zama tayi akan kujeran mirror ta kawai se phone nata dake kan study table nata ya fara ringing mikewa tayi taje ta dauka se taga Bwestie ta. Dagawa tayi ta kara a kunne ta rike wayan da shoulder ta tana cire towel din kanta "Sup" Kawai tace. "Yo. Gani fa a parlon kasa" El_Armeen yayi magana ta daya ban garan "Kay. Yanxin na fito daga wanka barin shirya abeg" "ASHAP" Kawai yace a tare sukayi hanging up. Drying gashinta tayi shap-shap ta saka hair oil sannan ta shafa mai jikin nan yasha turare after then she start with her make-up which is eyelining,giranta and then Kylie's lipstick which is maroon Seta mike ta shige closet nata. After 34mins ta fito da wani milk crop top a jikinta da milk pants ta daura blue vintage looking Kimono akai seta dauka blue veil ta daurashi kaman dankwali tasa hills black seta sake fashe jikin nan da turare ta suntuma phone nata da black shade ta sauko kasa. Akan couch ta tarar dashi yana danna waya as usual. "Phone addict" tace tana saukowa Dagowa yayi da sauri ya kalla ta inda yaji muryan Khameelarh. Besan sanda ya cire shades din idonshi ba. Ita kuma smiling tayi tana unlocking screen din wayanta ready to take selfies Harta karashe saukowa be dena kallonta ba. Ita kowa se dauka hotuna take abunta. "What!!?" Tace taba cigaba da daukan selfie ta ashe ta lura da kallon da yake mata. Gyara murya yayi ya mike "You ready right?" Daga mai kai kawai tayi yace "After you" murmushi ta sake tace "You are such a gentlemen" tana fitowa Beyi magana ba ya maida shades nashi shima ya fito. Khameelarh na fitowa se guard dinda Ummu ta saka ya ringa kula da ita wanda ita kanta batasan da zancan ba yayi saurin tare mata gaba. "Excuse me ma'am sorry to ask but were are you heading to" Kallonshi tayi irin kallon 'Are you kidding me?'  Din nan "And who are you to ask me!?" Ta tambayeshi tana dan daga murya kadan. "Ma'am am sorry but the first lady herself orderd me to look after you before she comes back" ya gaya in a respectful way Cire shades din idonta tayi ta saka kunne daya a lips dinta tana wani smiling "First stop calling me ma'am and secound da badan you are cute ba i would have fired you right now. And i can take care of myself" tana kaiwa nan ta maida shades din ta wuce shide El_Armeen beyi magana se bayan ta wuce yace ma guard din "Karka damu ba wani gu zamu ba, we are just going for a work" daga mai kai yayi se shima ya wuce Khameelarh kam har'an bude mata kofa ta fice abunta Tafiya suke kowa na danna wayanshi dukkansu akwai shades a disonsu. Suna cikin tafiya se  Khameelarh taga an manna wani poster a jikin kofan wani gida ae seda ta karasa wajan El_Armeen yana kiranta ina seda taje wajan saka hannu tayi ta baro poster. "Me zakiyi da wanna da kike cirowa" El_Armeen yake tambayanta yana karasowa inda take tsaya duk ta maida hankalinta kan hotan gayen data gani "Khameelarh!!" Yadan saga murya. Dago kanta tayi ta kalleshi da sauri "What?" Ta tambayeshi a rude "What are you gonna do with the poster?" yayi magana yana poiting dinshi a hannunta "Ask me one more time" ta bashi amsa tana wucewa daga wajan while folding the poster "Khameeelarh!!" Ya kuma kiranta yana yana sauri so that he could catch up with her. "Don't disturb me okey?" Ta saka paper a aljihun wandonta. "Mind your business" she added. Shiru yayi be kuma mata magana ba haka sukeje yawo a kafa suka ringa zaga garin mutane se kallonta suke wasu teenagers age-mate na Khameelarh har hoto suka dauka dukkansu hadda El_Armeen. Bayan sun dawo gida shi kuma ya wuce gida ta fito da poster ta mannashi a dakinta tanata kallonshi tana wani smiling kaman tababbiya. (Guess who was on that poster) *** Fitowa sukayi suka cigaba da tafiya Marwan ya bama Manal shades dinda ya sayo shima ya saka haka suke tafiya duk sun daka holan rigan sanyin Marwan yana goye da jakan a bayanshi wani yunwa sukeji kaman mene Sega wani cake store a tare suka kalla juna se suka saki murmushi (God!) Marwan yayi niyan shiga se Manal ta hanashi tace "Kaga a poster fuskanka ne a ciki ni babu wanda ya sanni so kawo naje na sayo and i will meet you here". Babu musu ya ciro kudi ya bata cus sun gane yanxin da sukayi using credit card dinne Acting president ya gano inda suke so seya dena using nashi tunda sunada kudi cash dayawa. Amsa tayi ta shiga wajan irin a store din ana iya sayan babban cake akwai kuma wanda ake yankawa tou irinshi ta saya choculate cake Aka mata packaging nashi guda biyu se drinks me sanyi shima guda biyu ta biyasu ta fito. A wajan data bar Marwan ta sameshi yana kokarin dialing wata number. Sakawa yayi a kunne yana ringing, tsayawa tayi inda yake zaune tana kallonshi. Ana dagawa yace "Faisal" irin he didn't expected that number daya saka was correct cus beyi tunanin ya rike number Faisal ba (best-frnd nashi) "Na'am" ya amsa a hankali kaman yana cikin wani hali "Faisal. Marwan ne" "Ohh. Myy god!! Marwan! Kana nan daman? I thought you were dead also" he said excited "Dead?" Ya tambayeshi "Yes saboda abunda ya faru da gidanku" yace a hankali A rude Marwan yace "Meyafaru dashi?" He asked a bit shocked "Uhn with the fire na..." "What fire Faisal?" "Marwan were are you? Gobaran da akayi a gidanku. Wait, baku cikin gidan ne?" "Gobara? Innalillahi..." Se Marwan yayi cutting line din nan da nan ya kashe wayan cus kar Faisal ya kira. Manal da taketa kallonshi se tace "Ya'Marwan wetin happen again?" Shiru yayi wane baze amsa mata ba se can yace "Faisal yace gidan mu anyi gobara. More like the beast is behind his, am freaking feild up with this asshole!" Ya karashe maganan da karfi. Fashewa Manal tayi da kuka kawai cus shine kadai solution nata a lokacin. Shiru yayi beyi mata magana ba seda taci kukanta sosai sannan ya lallasheta suka cigaba da tafiya ga cakes din a hannunta. Wata mota suka gani ta haya Golf se Marwan ya tara yace ya kaisu inda ake hawa mota idan za'a bar garin. A baya suka zauna abunsu se'a lokacin suka sama cin cake din, mutumin dake gabansu se kallonsu yake yana latsa waya tou shima Marwan daya lura da hakan se hankalinshi ya kasa kwantawa. --15mins later-- Suna cikin tafiya Manal se gyan-gyadi take a motan Marwan kowa yanata kallon mutumin kawai se yaji karan motan sojoji a nesa da sauri ya tada Manal yace ma driver motan "Mallan dan tsaya xanyi pitsari" "Tou bari mu sama wajan tsayawa" ya gaya yana duduba irin toilet dinda akeyi a hanya "Tsaya anan kawai!" Marwan yadan daga murya. Mutumin ya kalleshi seya kalla Driver "Mallan karka tsaya cigaba da tafiya." Manal da bata gane abunda ke faruwa ba amma ta gane Marwan so yake ya fita. "Mallan ka tsaya mana dan Allah nalura bakeda" Manal ta gaya da fuskan tausayi. Marwan ya juyo ya kalleta. "Karka tsaya Mallan" Mutumin ya sake fada duk suka rudar da driver. Kawai seya tsayar da motan da sauri suka fice Marwan ya mikam Driver 1k. Mutumin yace "Mallan wannan fa shine wanda yayi kisa da Acting president dakanshi ke nemanshi" duk yan motan suka juya suka kallesu. Juyawa sukayi zasu gudu kuma wajan dukka dajine se wani a motan yace "Kai tsaya babu inda zaka wlh" Wata mata dake motan tace "Haba! Kaman bakuda imani kuna kallon yaran nan kunsan taimako suke nema amma kana cewa ya dawo. Dan nan ku gudu dan wannan mugun ya kira sojoji" wata tsohuwa tayi magana tana nuna mutumin "Wlh basu isa ba se'an kamasu" ya gaya yana kokarin fitowa daga motan Tuni su marwan sun fara gudu suka shige dajin ba'a dade ba sega sojojin suka iso wajan aka gayan masu sun shige dajin. Haka suka bisu cikin doran dajin nan --2hrs later-- Sun tsiran ma sojojin amma abunda basu sani ba shine suna kumawa cikin Abuja ne dansun bata a cikin dajin. Suka shiga cikin mutane se wayan dake hannun Marwan din ya fara wani aleart dayake ya kunna fito dashi yayi daga aljihunshi se yaga wata number tana requesting video chat da Marwan. Nunama Manal yayi tace mai yayi accepting, aekowa yayi kawai fuskan daze fara gani se yaga fuskan Acting president yana wani murmushi a tskorace dukka su biyun ke kallon fuskanshi. "Don't be surprice kids. No dogan turanci am gonna ask you this last time zaka kawo min kanka?" "F*ck yourself!" Marwan yace "Good" se kawai Marwan yaga fuskan Mammi duk ta kuma wani iri "Mammi" a tare Manal da Marwan suka kira sunanta "Marwan. Manal" Mammi ta kira sunansu dakyar "Zaka kawo min kanka?" Acting president ya kuma tambayanshi yana pointing ma Mammi bindiga akanta "Tsaya! Tsaya! Zanzo..." Marwan ke magana a tsoarace Manal kowa duk ta kidime "Idan kazo ban yafe maka ba" Mammi ta katse shi besan lokacin da yayi shiru ba. "Idan ka kuskura kazo bazan taba yafe maka ba" ta sake maimaitawa "Shut up" Ya buga mata tsawa. Marwan ya rasa abunda zeyi "Mammi" ya kira sunanta a hankali muryan nan har wani rawa yakeyi "Na rigada na gayan maka" duk maganan da tayi bata kallesu ba "Zaka zo ko bazaka zo ba?" Ya kuma tambayanshi Shiru Marwan yayi ya rasa abunda zece yasan ze iya kasheta kuma gashi tace 'bata yafe ba' Kawai seya fara girgiza kai "Bazaka zo ba kenan?" Ya dade be amsa se ya kuma tambayanshi Da karfi Marwan yace "Noh!!" Da sauri Manal da Acting president suka kalleshi. "No! No! No please" Manal tayi magana tana fashewa da kuka dan tasan ending din "Marwan, Manal i love you guyx so much Allah maku albarka yasa ku gama da duniya lafiya. Lailahaillallah muhammadan rasulillah sallallahu alaihi wasallama" shi taketa maimaitawa idonta a kulle "Kace bazaka zo ba?" Ya kuma tambayanshi Hawaye ke zubu ma Marwan ya cigaba da girgiza kai "Good!" Kawai yace Ji kake dushhh!!! An harba bindiga. Dan tsananin tsoro ya saki wayan baki daya Manal kowa sumewa tayi kawai a wajan. 💋💋💋

Share:

Sunday, 27 August 2017

RASHIN MAHAIFA-CHAPTER 17 Suna hawowa saman gabadaya sojojin suka bazo a bakin kofan se Acting president yazo yayi knocking kofan kaman abun arziki "Marwan just open the door there is no way out" Ko kulashi beyiba ya nufa Window yana dubawa idan zasu iya fita tanan se yaga ba wani kwari gare window ba cus kaman wani katako aka buga shi da net aka makala a wajan kawai. Cireshi yayi baki daya ya ajiye a gefe ya juya ya kalla Manal wanda take kallonshi kawai da bindigan a hannunta. Alama yayi mata datazo, babu musu tazo ta tsaya gabanshi. "Ta window nan zaki sauka, kina sauka karki tsaya ki tafi stregth kawai i will catch up kin gane?" Girgiza kai ta fara tana leka wajan da tsoro. Ta bude baki zatayi magana kenan suka sake buga kofan ana kiran sunan Marwan da karfin gaske "Manal now!" Ya gayan mata adan tsawace. Batada wani option dinne kawai shiyasa ta fara fitar da kafanta hankali "Karki kalla kasa" ya gayan mata yana rike hannunta, daga mai kai kawai tayi babu wani magana "Ya'Marwan i don't want to" Tayi magana jikinta na mugun rawa "Manal" ya kira sunanta in a soft tone bata kalleshi ba balle ta amsa ba, be damu ba ya cigaba. "Idan baki sauka ba there is no way out kamamu zasuyi, ni zan iya yarda su kamani but not you beside babu abunda ze sameki insha Allah cus babu nisa kina fita akwai ladder shi kawai zaki hau ki sauka" Kallon wajan ladder tayi seta kalla Marwan "You promise kana baya na?" "Cross my heart" Ya gaya yana crossing heart nashi Gyada mai kai tayi sannan ta fara sauka da sauri-da sauri tana kaiwa na karshen ta kalla Marwan wanda ita yake kalla seta mashi alama daya sauko. "Ki tafi am right behind you" ya gayan mata more like wispering mata, girgiza kai tayi "Nop! You promised" "Manal go!!" Yadan daga mata murya Raising middle fingerta tamai ta fara gudu. Juyowan dazeyi yaji Acting President yana cewa "Break the freaking door!!" A tsawace Da sauri ya fice ta window kafin ya fara sauka suka bude kofan ido hudu sukayi da Acting President. Raising middle fingershi yayi mai kafin kace me har Marwan ya dira but he really hurt his left leg. Da sauri Acting President ya fizga bindigan dake hannun ogan sojojin yayo gun window ya fara harbi kawai. A guje Marwan ya mike dukda yadda yakejin zafin be hanashi gudu ba. "Ya'Marwan!!" Yaji an kirashi ta bayanshi. Da sauri ya juya kawai seyaga Manal a jikin wasu flowers tana boye seta fito ta nufo wajanshi. Ae batama kai ga gama karasowa ba yakai mata wani mari abunda be taba mataba kenan a rayuwanta. Ko daga mata murya bayayi se ya zama dole. "I thought i told you to run?!" Ya tambayeta a tsawace Ita kasa yarda tayi marinta yayi rike wajan kawai tayi tana kallonshi "Tambayanki nake!" Ya sake daka mata tsawa "Nika mara?" Ta tambaya unbelievable "I wish you were the one they caught not my parent. Everything that is happening is all your freaking fault, I hate you" she added hawaye na kwaranyo mata. Kawai se sukaji harbin bindiga kaman daga sama ihu Manal ta saki tana kare fuskanta. Besan sanda ya fuzga hannunta ba suka fara gudu suna shigewa cikin flowers cus idan suka tsaya a titin definately se'an samesu gashi titin wayam babu kowa cus dare yayi. Acting President ne da bindigan a hannunshi yanata harbi gashi harsun bace mai. Kallon sojojin yayi wanda basa komai idan ba kallonsu ba. "What are y'all doing? Follow them!" Ya buga masu tsawa, kowa ya daga bindiganshi sannan suka fara binsu. Ogan sojojin ne ya kallashi yace "Sir. Why do you want those kids so badly?" Da kaman baze amsashi ba se daga baya yace "They have something that belong to me" Ya karashe maganan yana kallon fuskanshi "Then why won't.." wani mugun kallo ya buga mai wanda ya sashi dan dole yayi shiru. Suna cikin gudun suka hango wata kofa Manal na taba handle din kawai seya bude da sauri suka shige. Inda suka shiga kaman feild din sport ne na yara cus ga basketball dan karami ga kuma feild din football ga footballs din a gefe dayawa. Marwan ne yayi locking kofan suka shiga cikin wajan sosai. Manal ta zauna a kan wani bench har'a lokacin hawaye kawai ke kwaranyo mata shi kowa Marwan zagawa ya farayi dan dubawa idan akwai mutane a wajan amma babu kowa dan haka duk kofan daya gani seya tabbatar a kulle take. Ya dade yana gayewa can seya dawo gunda Manal ke zauna ya daura hannunshi akan kafadanta yana kallon fuskanta kawai sega shedan hannunshi a fuskanta wajan yayi pink ji yayi ta bashi wani tausayi. Bude baki yayi zeyi magana setayi saurin cire mai hannunshi daga kafadanta "Habah Baby sis am sorry okey?" Banza dashi tayi kaman bata jishi ba. "Manal" still no respond "I couldn't go without you" tayi magana a hankali. Ji yayi he feels guilty sosai "Then am so sorry" batayi magana ba har yanzin. Amma kana kallon fuskanta kasan ta sauko. Sun dade a area wajan suna dube-dube amma basuga alaman mutane ba da haka suka dawo suka gayan mai 'They lost them' Wani irin wulli yayi da bindigan hannunshi cike da jin haushi. "You are all useless!! All of you!" He roar like an angry lion. Kallonshi kurum sukeyi dukka babu wanda yayi magana. A zuciye ya nufa inda motanshi yake wanda drivershi yana ciki. Kafin ya bude kofan seda ya laushe motan da karfin gaske kaman yayi hauka ya shige ciki. Driver kam beyi magana ba yaja motan suka fara tafiya. Sojojin suma suka shige nasu. Marwan ya saka kunnenshi a jikin kofan yaji shiru ya tabbatar sun tafi seya dawo ya nufa wajan kwallayan dake dakin yana duba abunda ze sunfidama Manal. Kawai seya hango wani flag kaman na wani team ne, dauko mata yayi ya mika mata babu musu ta amsa. "Shinfida ki kwanta it's already late" "Anan zamu kwana? Bazasu dawo ba?" "Kusun dawo am here to keep you safe so chop-chop and get some sleep" Gyada mai kai tayi ta shinfida ta kwanta da hannunta cikin aljihun rigan ko takalmin kafanta bata cire ba. Shi kowa kan beanch din ya zauna bayan ya ciro bag-pack din ya ajiye a kusa dashi ya ciro phone din kawai yana kallonshi ba tareda yayi komai dashi ba taba ciwon kanshi yayi kawai seya girgiza kanshi. Yana zaune a haka yaji Manal harta fara bacci ba'a wani dade ba wani wahalallan bacci yayi awon gaba dashi a yadda yaje a zaunan. After a long drive Acting president ya isa Mansion dinshi cike da bakin ciki. Yana shiga parlon sega El_Armeen yana zaune gaban T.v da wayanshi a hannu, sukayi ido hudu da juna seyace "Daddy ina kaje haka?" "Inda ka aekeni. Meya hanaka bacci?" Seda ya girgiza kai sannan yace "Khameelarh ce wai bata jin bacci so am keeping her company tunda babu kowa a gidan" Yayi magana yana cigaba da danna waya. "Msteww. Whatever" ya gaya tareda hayewa sama yana tunanin 'Meze hana kawai ya saka a kashe Khameelarh. Msteww aebashi ze saukar da mayen babanta ba' Haka ya shige dakinshi ya tarar da matanshi akan dadduma tana sallah. Tana ganinshi ta tashi da sauri. "Alhamdulillah. Alhamdulillah ina kajene wai? I thought something bad had happend to you" tayi magana tana huging nashi dan dadi. Tsayawa yayi a wajan kaman statue seta dago ta kalleshi "Wai meke damunkane kwana biyun nan ka chanja gabadaya?" "Work" kawai yace mata seya janye jikinshi ya shige toilet. Zama tayi a bakin gadon kawai ta fashe da wani irin kuka abun tausayi ta kasa gane kan mijinta kwana biyun nan but she want to believe aiki ne ya maidashi haka amma wani gefe a jikinta yana sata tunani kala-kala. Ta dan dade a haka daga bisani ta kwanta sosai akan gadon ba'a dade ba bacci yayi awon gaba da ita. Wanka yayi a toilet din bayan ya gama ya dauro alwala yana fitowa ya saka wata jallabiya yayi sallah seya haye gadon tareda janyo matanshi ba'a dadeba shima bacci ya daukeshi *** A yanxin ko yaji tausayinsu ne oho amma ya kwancesu but ya chanja masu daki ya maidasu wani daki akwai toilet a ciki amma window dakin babu yadda za'ayi a fita babbane dan girma amma kuma yadda aka kulleshi babu daman budewa. Kuma ana kawo masu abinci kullum sau uku (Da alama imani ya fara shiga zuciyanshi Lol) Mammi ce kwance a kafadan Abbah duk ta wani rame kaman tayi ciwon shekaru rabi bacci take amma rabi idonta biyu ta kuma wani irin abun tausayi ga kuma wani baki da saukayi dukka su biyun Rabin Hours dinda suke speeding sallah sukeyi na rokan Allah yasa kar azzalamin nan ya kamasu Marwan. *** Abbu yanxin ya tashi amma be iya komai yana daga kwancan nan sanda ya tashi Ummu hadda hawaye dan dadi ta gudu ma Allah kaman ba gobe hadda rungume Abbu seda tayi. Shi kowa kallonta kawai yake yana murmushi. Be iya komai idan zeci abinci se'a dago mai gadon a bashi abinci ko sallah ne daga gadon yakeyi. Ya wani rame kaman ba Mr. President ba ga baki kuma da yayi. (Kai duniya!! Wlh karshen wasu baza tayi kyau ba. Allah sa mu dace. Amiiin) Sanda Ummu da gayan ma Khameelarh, Abbu tashi sega Khameelarh na cewa 'Alhamdulillah! Alhamdulillah' Har gaisawa da Abbu seda sukayi. --The nxt day-- Marwan ya fara tashi ya kalla Manal tana bacci kana kallonta kasan baccin nan badan dadi akeyinshi ba mikewa yayi. Yayi wata mika dan jikinshi wani azaban ciwon da yakeyi saboda kwana da yayi a zaune. Duk jikin nan yayi tsami. Ya dade a tsaye yana streching jikinshi daga nan ya dauka jakanshi ya goya. Ya fara neman toilet a wajan, kaman daga sama seya sama wani shiga yayi da addu'a yayi alwala ya fito. Besha wuyan gane gabasba, yayi sallanshi bayan ya shinfida wani kyalle kenan. Ya dade akai yana ta addu'oi daga nan ya mike. Yana mikewa ita ma Manal ta mike zaune tana mika tareda addu'a itama jikinta sedayayi tsami. Tana zaune se susa hannu kawai take tana binshi da ido kaman T.v "Ga toilet can idan zakiyi alwala" Marwan ya gaya yana nuna mata. Gyada mai kai kawai tayi seta mike ta nufa inda yake nuna mata. 💋💋💋

Share:

Contact Form

Name

Email *

Message *