Tuesday, 15 August 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 13 Kallonshi take da mugun mamaki shima haka ita yake kallo da hanunshi ya daura akai Bayan kusan 15mins tana kallonshi kawai seta mike a hankakali ta fashe da wani irin kuka me mugun tsuma rai Ta zama abun tausayi kawai kuka take can Marwan shi ta gaba bashi tausayi seya mike dakyar kanshi na juyawa ya nufa inda take Huging nata yayi ta baya yace "Hey! Am sorry i was just kidding ke kadai kika rage min taya zan manta dake" a hankali yake maganan cus yadda kanshi kemai zafi sosai Juyowa tayi ta fara dukan kirjinshi da karfi tana cigaba da kukan tana cewa "This not a joke i hate you" Rungumeta yayi sosai "Am so sorry and ina tare dake a ko yaushe I love you so much" Shiru tayi tana saukar da ajiyan zuciya "And i love you more" ta fada daga baya a zuciyanta kowa gode ma Allah take sosai danya taimaketa cus tasan idan Marwan yayi losing memory shi itama ta gama. Shi kowa tausayinta ya kamashi *** "So barin ware gida ni yanxin" El_Armeen yake magana yana mikewa daga kan kujeran da suke zaune tareda Khameelarh Kallonshi tayi kaman zatayi kuka tace "Habah ni kadai zaka bari a wannan gidan dan Allah?" Kallonta yayi da mamaki karara a fuskanshi sannan yace "Duk securities din gidan nan kike cewa ke kadai? Kede kika sani ni na tafi" "Dan Allah ka kwana anan mana" "Wait! Hala Malt dinda kika sha yayi expire ne ko mene. Meelarh naga alaman kin gaji da ganina a duniya dan ko Mr. President be yankani ba Daddy ze yankani. And seriously i need a shower dan na fara tsami banyi wanka ba na fito" "Babu komai dan kaga kaine kawai frnd dina shiyasa kake min wulakanci lokacina yana zuwa nima" tayi magana irin abun tausayin nan Murmushi yayi yace "Nina hanaki yin frnds din girman kanki ne ya ja maki" Harara ta galla mai tace "Ae wlh da inada girman kai ko kai bazan kula ba dan rainin wayo ka tafi mana dama can waya kiraka" Ko in kula yayi da ita ya kama hanyan fita seya juyo yayi mata gwalo pillon hannunta ta wulla mai ya fita yana mata dariya. Abun ya shakar da ita da karfi tace "Moda f**cker" yadda zeji shi kowa seyace "Thank you" Tsaki taja ta mike ta shiga dakinta tana tunanin yadda zataji muryan Abbunta da Ummunta. *** Anyi aiki an gama but har'a lokacin be tashi ba. Ba kaman na farkon bane wanda da aka gama ko 30mins be kara ba ya tashi amma yanzin har 2hrs 30mins be ko motsa ba heart bit nashi kawai ake gani a hankali. Ummu tana kusa dashi tana rike da hannanshi wanda babu karin ruwan a jiki ta daura kanta a gefan gadon tanadan gyan-gyadi a hankali kawai seta mike lokaci daya dan Khameelarh ta ta fado mata. Waje ta leka taga daya daga cikin securites dinda sukazo dashi tace mai bari taje ta dawo karya bar kowa ya shifa hadda Nurses din. "Yes Ma'am" Sannan ta wuce. A Hospital din akwai inda ake call Telephone kenan nan taje tayi dialing number Khameelarh ta saka a kunne yana ringing. Ita kowa tayi zurfi cikin tunani kawai se taji Despacito a parlon kasa mikewa tayi a guje cus tasan ringing tone natane. Tsalle tayi akan Couch sannan ta dauka wayan number ta gani wanda ta tabbata Ummu ce cus bana kasan nan bane Dagawa tayi tasa a kunne tareda cewa "Ummu" a hankali seta fashe mata da kuka Nan da nan Ummu taji zuciyanta ya karye "Baby ya isa haka please ya sama sauki fah" "Then bashi mu gaida dashi please" Shiru tayi tana tunanin me zata ce mata can tace "Now is not a good time cus an mashi alluran bacci ne danya sama hutu but as soon as he weaks up i will contact you okey?" Gyada mata kai tayi kaman tana gabanta. Abunka da yarta tasan bazata amsa ba seta cigaba "Meelarh don't let anyone in the Mansion karki fita kinji? Kiyi zamanki a ciki hatta Securities karsu shigo duk abunda kike so ki tambaya Maids. Kinji Swthrt?" "Tohm Ummu. Yaushe zaku dawo?" "For now ban sani ba amma ana sallaman mu zaki ganmu anjima zan sake kiranki kinji? Take care love you" "Love you more" A tare sukayi hanging up Kwantawa tayi akan kujeran kawai tana tunanin yadda rayuwansu yake 'Wancan ciwon da yayi ance guba yaci yanxin fa? And waya saka mai? Wait. Waye ma keson kasheshi? Allah ka rabamu da makiya Allah kasa wannan mulkin idan ba alkairi bane Abbu ya sauka' Haka ta ringa sake-sake ita kadai har daga baya sarkin sata ya saceta (bacci). *** Su Abbah a yanxin sun gala baita sosai balle ma Mammi wanda bata saba da wahala ba garama Abbah Namiji ne amma a gaskiya ita tana shan wahala ga zama waje daya ga kujeran babu laushi ga babu daman motsawa dole tana waje daya. Ajiyan zuciya kawai takeyi babu daman magana dan gala baita. Abbah kallonta yakeyi tun dazin yaga bata bude ido ba. "Mammi" a hankali ya kira sunanta "Uhmm" kawai ta amsa mashi dashi idonta were still closed "Don't give up okey? Allah na tare damu kuma nasan ko me zasuyi Allah baze barsu su kamasu marwan ba mu cigaba da Addu'an kariya" Ya karashe maganan a hankali. Batayi magana ba se hawayen daya fara bin fuskanta kaman ruwa, at that very moment ji yayi kaman ya mike yayi huging matanshi cus only God knows how she most be feeling right now after loosing both her kids this is the worst nightmare every 'Allah kana ganin masifan da muke cika Allah ka yaye mana Allah ka kubutar da iyali na ka karemin yarana Allah ka tuzarta wannan azzalamin ka kaskantashi ka ruguza mashi rayuwanshi ka ruguza abunda yake kokarin shiryawa' Shiru yayi kawai yana cigaba da kallonta ta kuma kaman ba ita ba Ohh Allah. Tafiya su Marwan keyi ya goya jakan yana rike da hannun Manal suna neman kemist dan wanke mashi ciwo amma ko kyallin mutum basa gani balle wani shago, ita duk ta gaji shima ya gaji ga kanshi yana mai wani radadi amma a haka yake daurewa dukda jirin da yakeji. After like 1hr of walking ga yunwan da sukeji kawai can nesa suka hango wani town "Ya'Marwan kalla kaman mun iso wani gari" da sauri ya daga kai a lokaci daya yaji wani dadi ya ziyarci zuciyanshi duk gajiyan da yayi seya manta dashi ya fara sauri itama haka Manal sauri suke sosai suka shiga garin kana ganin garin kasan ba kauye bane yan birni ne. Haka suka fara wuce mutane se kallonsu ake amma ba wanda yayi masu magana kallo kawai ake binsu dashi can suka hango wani store karami nan suka shiga kayan provision ne a ciki gefe suka sama ya bude jakan bayanshi ya fito da 2k ya mikama Manal. "Saman mana abunda zamuci barin duba ko akwai kemist a kusa, karfa ki fita daga nan idan kin gama ga bench nan a waje ki zauna a kai kawai kinji?" Daga mashi kai tayi seta juya ta shiga cikin store din sosai shi kuma ya juya ya fita. Ashe Vice President ya bada order an hada meeting da dukkan sojojin Nigeria da Police da Army hadda Nevy dukkansu de akan duk wanda ya kamusu ze kara mashi matsayi bayan ya cika mashi aljihu kenan. Marwan ya fita yanata tafiya can daga sama ya hango wani karamin shago daya tabbatar kemist ne hamdala yayi ya shiga bayan ya sake bude jakan ya dauka 1k kenan ya saka a ajihunshi ya shiga. Da sallama ya shiga babu kowa a shagon seme kemist din kawai. Gaisawa sukayi dashi ya gayan mashi abunda ya kawoshi nuna mashi wajan zama yayi ya zauna seya debo kayan wanke mashi ciwon ya zauna shi kowa Marwan ya cire gyalen Manal wanda ya barta babu komai akanta ga gyalen duk ya baci da jini. Me shagon ya kalla goshin Marwan seya kalla fuskanshi da mamaki koma besan dalili ba dan yana mai kamada wanda ya sani "Ya akayi ka sama wannan ciwon haka" Seda gaban Marwan ya fadi ya amsa shida " Fadi nayi wajan ball, danyi sauri ana jirana dan Allah" Daga mai kai kawai yayi ya fara kwankewa daurewa kawai yakeyi seya tuna da Mammi ce ke wanke mai da yanxin ta saka Abbah da Manal sun danneshi dan ihu ze ringa mata. Allah sarki wani sa'in iyayenka kawai kake ma iskanci balle ma mahaifiyarka. Besan sanda hawaye ya kwaranyo mashi ba cus yasan probably by now sun koma ga mahalicinsu. Me kemist ya tsaya kallon Marwan da mamaki yace "bro kuka kakeyi?" Firgita ya danyi kadan alaman yayi zurfi cikin tunani. Girgizamai kai kawai yayi yana share hawayen fuskanshi Cigaba da dinke mashi yayi yana gamawa ya bashi maganin daze sha ya biyashi kudinshi tareda mai godiya ya meke ze fita. Kawai ya hango poster fuskanshi ansaka katon Wanted a sama a firgice ya tsaya yana sake kallo. Mutumin kemist din kowa yana kwashe kayanshi daga wajan seya daga kai ya kalla Marwan danya aza ya fitane. Mikewa yayi yana son kallon abunda ya tsaya kalla se yaga poster karasawa yayi gunshi tareda dafa bayanshi "Yade?" A dan firgice ya kalleshi seya cigaba da kallon hotan yana kare fuskanshi "Ka ganshi karami dashi koh? Wai kisa yayi seya fito daga gida shida kanwarshi Vice president da kanshi ya saka ana nemanshi kaga kowa ba karamin masifa yaja ma kanshi ba" Yayi magana yana kallon hotan shima amma be gane Marwan ba cus poster is Black and White so ba dole bane ya ganeshi. Shiru Marwan yayi kirjinshi yana dukan uku-uku 'He really got the nerve to say i killed someone' So yake ya fita kafin mutumin ya ganeshi. Beyi magana ba ya ganje jikinshi ya kama hanyan fita. "Tsaya!" Yaji mutumin ya fada da karfi. Dumm!! Kirjinshi ya buga a lokacin ya tsaya amma be juyoba,karasowa gunshi gayen yayi ya mika mai leda "Gashi ka manta da magungunan" ya gaya yana mika mashi wata leda. Juyowa yayi a hankali ya amsa tare da cewa "Thank you" Kallon fuskanshi mutumin yayi ya kalla poster se a lokacin ya ganeshi. Hannun Marwan mutumin ya rike da karfi. Nan da nan jikin Marwan ya fara rawa dan tsoro "Kaine! Wallahi kaine" "Mallan wlh banyi kisan kaiba. Wlh ban kashe kowa ba kayi hakuri ka rufa min asiri dan Allah" Duk a tsorace yake "In rufa ma asiri?" Mutumin ya maimaita se yayi wata dariyan keta "Kasan nawa yace ze bada?" Jawo hannun Marwan yayi zuwa poster ya nuna mai amount din "Kalla ae tausaya min zakayi kawai na kira number dan idsman na sama kudin nan na gama da shagon nan kuma..." be karasa ba Marwan ya kaimai wani wawan punch a hanci. Ba shiri mutumin ya sakeshi nan da nan jini ya farabin hancin. Marwan na ganin haka yayi waje a guje bayan ya dauka ledan maganin Yana fita se yaga wani police da donut a hannunshi yana tafiya se ya dena gudun yana tafiya a hankali yana kare fuskanshi "Sir gashi nan. Shine wanda ake nema!!" Mutumin kemist din ya gaya da karfi daga shagonshi yana nuna Marwan sannan yana kokarin biyoshi shima hannunshi a hanci yana kare jinin Police din ya kalla mutumin ya juyo ya kalla Marwan yaga yana zabga sauri se yace "Hey! Stop!" Yanajin haka ya saka kafa ya fara gudu.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Contact Form

Name

Email *

Message *