Tuesday, 15 August 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 7 Copying number motanshi sukayi sannan suka juya suka koma gun Vice president A burkice yake gabadayanshi karasowa gunsu yayi da sauri "Yaya? Kun kamashi?" "Yallabai wlh ya gudun mana. Amma ka kwantar da hankalinka mun copa number motanshi" "Toh naji inason ku ganu min information nashi baki daya sannan ku kamu minshi kar ku bari video da yayi ya fita duniya" Yana gama fadin haka ya kada riganshi ya bar wajan. By now yan party kowa ya watse dan lokacin da sukaji harbin bundiga gabaki dayansu kowa ya tarwatse daga gun party kowa ta kanshi yake Faisal (frnd din Marwan) ya ciro wayanshi yana dialing number Marwan amma se ace number busy dan bega motanshi ba se kuma jikinshi ya fara bashi Allah sa ba abunda ya sameshi *** Driving yake kaman (Baby driver )Lol gabanshu se fadi yakeyi gashi ya kira Abbah ya kirashi amma be daga ba Da haka ya nufa gida amma seda ya tabbatar babu me binshi tukun Yana isa gida ya shiga ya bude gate sannan ya shigo da motanshi ya kuma ya rufe gate din Shigowa gida yayi aguje har a lokacin a rude yake Kiran sunan Abbah kawai yakeyi dan yaga motanshi a waje and yau Saturday yasan beje aiki ba A parlon kasa ya tsaya yana kwallama Mammi da Abbah kira "Abbah!! Abbah!! Mammi!!!" Kawai yake maimaitawa. Manal dake kitchen ta fito aguje tana tambayanshi lafiya "Ina Abbah yake" ya tambayeta yadda yake maganan ma seya sake tada mata hankali "Suna sama. Ya' Marwan meyafaru wai?" Nufan wajan stair case din yayi ba tareda ya amsa taba "Abbah!! Abbah!!" "Wai lafiya Marwan? Lafiya kake kwalla mana kira haka?" Abbah yake fada yana saukowa daga sama da alaman bacci yakeyi Karasawa Marwan yayi gunshi aguje "Abbah we have to leave like right now! We have to leave" Ya gaya yana rike da hannun Abbah dukka biyun Mammi itama ta sauko kallonshi take da mamaki yadda yake magana da kuma yadda ya kuma dan tasan ba haka ya fita ba Rikoshi tayi suka sauko kasa kujera taja ya zauna akai sannan ta deba ruwa a glass cup ta saal mashi a baki ba musu ya amsa. Seda ya shanye dukka sannan ta cire cup din a bakinshi a hankali tace "Tell me meya sameka" "Mammi. Abbah we have to leave like right now wlh kasheni zasuyi!! Kashe mu zasuyi gabadaya" Mekewa yayi sannan ya cigaba "Abbah mu hada kayan mu mubar garin nan dan wallahi kashemu zasuyi gabada" ya gaya yana son wucewa Kallonshi suke baki daya hankali tashe dan duk ya gama rudar dasu ga kuma hawayen da yakeyi itama tuni Manal ta fara hawaye "Kai!!!" Abbah ya daka mashi tsawa Dakatawa yayi sannan ya juyo "Calm down and tell us what the F is happening" he added in an annoyed tone Juyowa Marwan yayi yana kallonshi sannan ya maida view nashi gun Mammi da itama ta gama burgicewa seya sake kallon Abbah Kaman Abbah ya gane abunda yake kokarin gayan mai seya nufa gun Marwan ya rike mashi hannu suka fito waje gun garden Gun wasu kujeru suka zauna sannan Abbah yace "Am all ears" Seda yayi wata ajiyar zuciya wanda be taba irinta ba sannan yace "Abbah muna cikin party Mammi ta kirani a waya na kuma gefe guda na daga bayan mun gama magana sena maida wayan harna fara tafiya naji mryan mutane suna magana a hankali sena kuma ina dubawa se naga Vice president suna wata magana. Sena ciro wayana ina video kawai se aka kirani" tsayawa yayi yana kokarin ciro wayan a aljihunshi Gun video yakai sannan ya mika ma Abbah wayan Kallon video Abbah yayi kawai seya fara "Innalillahi wainna ilaihir'raji'un" a hankali seya kalla Marwan wanda har yanxin a tsore yake "Marwan what have you got yourself into? Oh my Goodness the vice president was behind this all of it. I knew it, i totally knew it. Innalillahi kuma sunga fuskan ka?" "Abbah sun gani fa and am pretty sure sunga number motana dan harsun harba glass din baya. Abbah ya zanyi na janyo mana bala'i muna zaune lafiya tunda yakeda niyan kashe president am sure kasheni bazeyi mai wahala ba, Am so sorry Abbah" Yana magana a hankali hawaye yana kwaranyo mai Kallonshi Abbah yayi se yaga ya bashi tausayi hannunshi ya daura a bayansi se yace "Habah big boy men up abeg. Calm down they can't do anything to us we have the video against them idan sukayi threating dinmu semu saka video online duniya ta gani anyi 1-1 kenan" "But Abbah what about the president? I know by now they have a plan yadda zasuyi su kasheshi" "Karka damu sunsan kanada video nan right?" daga mai kai Marwan yayi "Perfect!! so tunda sunsan kanadashi they won't do anything stupid" Hug Marwan ya kaima Abbah "I have no idea what to do without you guyx by my side" Murmushi kawai yayi shima yayi huging nashi back "One more thing karka gayan ma Mammi cus you know how koko she is about His Excellency i will find a perfect time dazan fadan mata abunda ake ciki" "Gorrit" a tare suka saki murmushi Amsan wayan ya sakeyi ya tura video a wayanshi sannan ya mika ma Marwan nashi wayan "Ka cire M-card din wnd find somewhere save da zaka ajiye" Daga mai kai kawai yayi Dawowa parlour sukayi anan suka tarar da Mammi da Manal suna zaune sunyi gungum-gunmun Tana ganin shigowansu seta mike tayo kansu "Marwan are you okey? Meyasameka ne? Faisal called yana tambayana wai kana gida? Wai sunji harbin bindiga. Tell me meyafaru a wajan!" Murmushi yayi sannan yace "Mammi nothing serious fah harbin da akayi ne yaban tsoro shiyasa" "Tou su waye sukayi harbin?" "I have no idea" "Then meyasa motanka babu glass din baya?" Kallon Abbah yayi shima yana kallonshi seya fara shafa gashin kanshi "Uhm...glass..abunda......" "Garin gudu ne" Abbah yayi saurin amsawa "Gudu kuma. How comes glass dinne ya fashe kawai?" "Lets forget about all this okeyy. He's okey right? Then mubar zance. Marwan je kayi wanka ka huta" Daga mai kai yayi ya nufa dakinshi se Abbah ya rufa mai baya shima ya wuce nashi dakin Kallonsu Mammi da Manal sukeyi da suka gaji se suka rufa masu baya *** "Abbu gani" Khameelarh ce da night gown nata tazo parlo "Come and sit next to me princess" Zuwa tayi ta zauna "Kina jina koh?" "Yep" ta fadi tana poppong P din "Perfect zan sakaki a karate class" Mikewa zaune tayi da sauri "Karate wetin?! Ohh God no please. Abbu karana aka kawo maka a school hala? but this not fair i've been a good girl banma teachers rashin kunya wlh am doing my best you can ask El_Armeen" Ta karasa maganan kaman zatayi kuka dan har idonta sun ciko da hawaye Kallonta yayi kana yace "Babu wanda ya kawo karanki the Kung fu class is for protection a matsayinki na mace" "Abbah i can protect myself you know no need of Karate class. Wlh jikina ze murde na kuma na maza" "And who told you that? You are attending Kung fu class and that's final" Seya mike yabarta a wajan. Binshi tayi da kallo yana barin parlon tace " 'You are attending kung gu class and that's final' da wani bakinshi kaman Kun fu msteww i hate this life sometimes" seta mike ta wuce dakinta(ohh Allah Khameelarh) Marwan ne ke wance a dakinshi gabadaya ya gaza bacci se juyi yakeyi akan makeken gadonshi Wayanshi ya dauka yaje gun video yayi playing ya ringa kalla yakai sau hudu kaman yana neman wani abu Can se yayi coping video akan phone din seya bude wayan ya cire M-card din Wani dan kit din agogo dake kan mirror a ciki ya saka seya kulle ya kuma ya kwanta yana kokarin kiran Faisal dan tun dazin yaga missed call nashi Ringing daya ya daga "Dude wai lafiyanka? Ina ka shiga? Tun dazin se kiranka nake" "Wlh ina gida" "Meyafaru? Did you heard the gun shot?" "Gunshot! Waht gunshot?" Yayi acting kaman besan da wani harbi ba "Hmm bari kawai i had that girl what was her name?" "Symarh?" "Right ita wlh i had her kawai se mukaji harbin bindiga kumafa ba wajan mu bane ae kowa seya kama gabanshi ni seda nayi nisa sannan na tuna dakai wlh a lokacin ne na ringa kiran number ka wai busy harna kira Mammi" Dariya yayi yace "Party was boring ne shiyasa nabar wajan" Hira suka danyi daga bisani sukayi sallama lokacin 12 yayi da yagade ba bacci zeyi ba seya mike ya dauro alwala ya ringa gera nifiloli yayi-yayi harya gaji seya dawo gadonshi ya kunna laptop dinshi yana kallon Teen Wolf har wajajan karfe 5pm yaji kiraye-kirayen sallah seya sake alwala ya fito sukaci karo da Abbah tare suka nufa masallaci Suna dawowa ya dawo dakinshi ya kwanta ya tufa addu'oin shi amma har'a lokacin seya kasa bacci tunani daya yake sanda daya daga cikin mazan nan sukaci "Yanxin meze hana kawai aje gidanshi a mashi yankan rago shiyafi komai sauki" Abunda kemai yawo akai kenan ji yake kawai kaman zasu biyoshi suyi mashi yankan ragon mikewa yayi da sauri kaman an mintsineshi ya leka window dake kallon gate ya dade yana kallo bega kowa ba daga bisani ya kuma ya cigaba da kallonshi har 7:58am idonshi biyu Karfe 8:42am ya mike dagashi se boxers da riga ya fito ko brush beyi ba balle yayi brushing kanshi haka ya sauko kasa ya tarar da Mammi da Manal suna gera break-fast a dininng kallonsu yakeyi kaman be taba ganinsu ba seya sama waje ya zauna a parlo yayi setinsu _Ya Allah what did i got myself into? Allah kasa karsu gane koni waje Allah karka basu daman rabani da family na cus i know ni kwaro ne a gabansu am pretty sure idan suka ganoni bazan masu wahala ba. What took me there in the first place?_ Haka ya ringa gero ma kanshi tambayoyi kala-kala bema san Mammi namai magana ba kuma su yake kalla seda tazo ta tabashi sannan yadan furgita kadan Zama tayi kusa dashi "Marwan swthrt tell me meke damunka tun dazin nake maka magana amma baka sani ba" Wani murmushi ya kwakulo wanda idan mutum yayi shi zakaji kaman yana maka zafi a fuska sannan yace "Mammi am fine kawai lissafi nakeyi akaina" "Lissafin mene Marwan?" "Na kudin da Abbah ya bani naga yayi saurin karewa ne" Girgiza kai kawai tayi bawai danta yarda ba ta kuma gun dining din "Toh tasu muyi break-fast" Tana tufe baki sega Abbah ya sauko daga sama yana kallon Marwan har idonshi sun kara manya ga gashinshi was a mess se yaji ya bashi tausayi danya tabbata be samu bacci ishesshe ba Karasowa yayi ya zauna a dininng Manal ta gaidashi "Marwan bazakaiyi break-fast ba?" "Uhm Mammi na koshi" "Meyasa bazaka karya ba?" "Abbah am not hungry" "Atleast ko coffe kasha mana" shiru yayi beyi magana ba "Manal tashi ki hadama Ya'Marwan coffe yasha" Ba musu ta mike taje kitchen ta hadu mai bata dadeba ta kawo mai Mika mai tayi ya amsa "thank you" Seta juya ta kuma tayi break-fast nata Kafa kai yayi dukda zafinshi haka ya shanye yanayi yana ajuyewa haka ya kurbe dukka Remote ya dauka sannan ya saka pillo ya kwanta akan couch din parlon yana kallon The flash Ko 20mins ba'ayi ba wani bacci ya daukeshi Su Abbah suna gama break-fast nasu ya mike yana cewa "Marwan tasu i need to talk to you" Se yaji shiru dan haka ya leka ciki parlon ya ganshi ya fara bacci wani mugun tausayinshi yaji ya kamashi "Manal dauko min blanket" Mikewa tayi ta dauko a dakin Marwan ta kawo mai Abbah ya amsa sannan ya lullubamai ya kunna mai Ac sannan ya kashe wutan dede parlon Yana juyawa kawai se yaga Mammi tana kallonshi alaman tambaya "I need to talk to you like right now!" Tana gama fada ta juya ta haye sama... *** "Khameelarh!! Khameelarh!!!" "Na'am Ummu gani nan zuwa" she yelled from upstairs "Sauko yau ke zaki mana lunch!" "Wtf!! Are you serious?" "Yes! So hurry up am waiting for you" "Buru uba an kasheni. Ni wlh bacci nakeji" ta gaya a hankali tana saukowa daga kan gadonta Dama shorts ne kawai da vest a jikinta seta daura wata crop top ta sauko kasa da earpiece a kunnenta. "Ummu dagaske kike wai?" "Yes a age dinki ya kamata ace kin iya komai amma a yanxin baki iya komai ba kwata-kwwta wata nawa ya rage maki ki shiga 18 amma ace ko indomie baki iya dafawa ba. Yau dole sekin dafa mana wani abu" "Ko menene?" "Yes" "Ae shikenan basekin tada jijiyan wuyanki ba" tana gama fadin haka ta shiga kitchen din

Share:

0 comments:

Post a Comment

Contact Form

Name

Email *

Message *