Tuesday, 15 August 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA -CHAPTER 9 Tun lokacin bata sake fitowa daga dakinta ba har seda taji shigowan Abbu kana ta fito a library ta sameshi da medicated shades dinshi yana wasu rubuce-rubuce tana shiga ya cire shades din yana kallonta "Swthrt what's with the face?" Wani fuskan shagwaba tayi sannan ta karaso cikin library din gunshi ta nufa ta zauna kan cinyanshi "Ah ahh zaki ballama dan tsoho kafa, ke bakisan kina girma bane?" "Habah Abbu mana na kawo maka kara amma kana wani cewa ina girma" ta karasa maganan kaman zatayi kuka "Aww kinfison ace baki girma?" Ya tambayeta da mamaki "Niba haka nake nufi ba" "Tou yanxin dauko kujeran can ki zauna akai seki fadan min karan wa kika kawo" Noke kai tayi kaman karamar yarinya wai ita bazata dauko ba Mikewa yayi ya dauko mata kujeran ko kunya babu ta amsa ta zauna sannan yace "Ina jinki babyn Abbu" "Yawwa Abbu ba kace zan fara attending Kung fu class ba?" Daga mata kai yayi alaman hakane sannan ta cigaba "Wai dazin Ummu kuma zan fara zuwa catering school again" "A hakane we made the decision together" "Habah Abbu fisabillilah me kukeson ku maidani ne? Am just 17 amma kunason in ringa zuwa school sannan naje Kunfu class idan na dawo na tafi catering school ae bazan gane komai ba" "Zafa ki gane and your brain is still young dan haka Monday-Firday idan kika dawo daga school 3:30pm zaki kung fu class Weekends kuma bayan malaminki ya tafi karfe1pm ki tafi catering class din zuwa 4pm ba shikenan ba?" "Aa wlh ba shikenan ba wlh ruda kwal-kwalwana kukeson yi nifa Abbu gaskiya ban yarda ba kawai a barni nayi zamana a haka girki koma zan iya koya online" "Online? Chab ban yarda ba na tabbata indomie da kika dafa dakin online kika duba ko ba haka bane?" "Hakane Abbu amma wlh ba haka suka nuna min ba nice kawai na kara....." "Saboda kar yayi dadi ace ki sake wani koh?" Ya katseta Shiru tayi bata sake magana ba Seya mike yaje gun kujeran da take "Meelarh hun wannan abun da mukeyi we are not doing it to hurt you or someting no!! Is for your own good yanxin idan kinyi aure ya zakiyi?" "Ga maids nan kuma ni ba yanxin zanyi aure bama" "Ba ko wannan namiji keson maids na mashi girki ba. Khameelarh kibi UMARNIN IYAYENki kiyi abunda muka zaban maki i know someday you will thank us. Kinji Babyna" "Tou shikenan Abbu but nima zakamin wani abu" "Mention it" ya gaya yana komawa kan kujeran da yake "Abbu you know i love you guyx and ina bin abunda kuka sakani (am i dreaming?) Well nabi abunda kuka sakani" Tayi saurin gyara kanta seda Abbu yayi murmushi sannan yace "Ina jinki" "Yawwa Abbu why not a sayan min motan yanxin plxxx" "Mota! Chab kema kinsan baze yuwu ba dole se kinada drivers liences dinki and baki kai age dinba" "Abbu mutane dayawa suna 16 fa aka masu drivers liences and ni ko bandashi babu me kamani" "Aa baze yuwu ba we are the gorvement dole mutane suga example a wajan mu dan haka na maki wannan alkawarin on your 18th birthday zan baki komai hadda dream car dinki kin yarda?" "A na yarda aradu ae yama kusa thank you" Seta mike tayi pecking kumatunshi sannan ta fice kallonta kawai yakeyi yana murmushi yadda yake jinta sosai a zuciyanshi. --Vice president office-- Vice president ne da senate president(Mustapha Anas) a office dinshi suna hira "Am telling you don't worry about this nima bakasan yadda na kosa na hau mulkin nan ba wlh" "Bari kawai kaika kusa koni? Har mafarki nake gani na zama vice naka" Dariya sukayi duka tafa (Kunsan idan President ya rasu vice nashi ke hawa tou idan ya hau Senate president ke zama Vice nashi. Nasan most of you know gaya nake for does of you that don't) "Amma yanxin ya maganan yaron nan da kake ban labari ya ganka kowa?" "Wlh ya ganni fah ido hudu mukayi dashi amma karka damu inada wanda na saka aiki zasu nemo minshi sena tabbata na goge video sannan a mashi yankan rago a gabana" ya gaya irin babu sauran imani a zuciyanshi (Innalillahi kaga yankan rago a wandonka wlh dan babu me yanka Marwan na tsaya ina kallonshi๐น๐น) Suna cikin wannan maganan ne sega wa'an nan mazan biyu sun shigo da sauri Vice President ya mike yayi gunsu a zuciye "Ku bakuda hankali ne bana hanaku shigo min office ba? Akwai fa inda muke haduwa daku meyasa bazaku kirani nazo ba? Kuma ko zuwa nan zakuyi ku ringa shirin mutanen arziki mana" Ya karasa maganan kaman ze kwada masu mari "Habah zanka ya dade our soon to be president informatuon dinda muke dashi baze jira ace harseka zo bane shiyasa muka biyo ka" Tunda yaji ance 'soon to be president' seya sauko Senate president ne yace "Meyafaru ko gayan mana!" "Yawwa! The news is mun gano information na yaron. Mun gano gidansu,ga phone numbershi. Yana zaune da iyayenshi da kanwarshi ne,babu abunda bamu sani ba nashi har birthday shi mun sani" "Bravo!!! Bravo!!! Kun gama mun komai wlh and kunada kaso me yawo akan wannan news dinda kuka kawo. Yanxin yaushi zakuje ku dauko minshi danda hannu na zan kasheshi kuma na kashe banza wlh" "Mu ko'a yanxin nema bamuda matsala" dayan ya amsa shi Wani wawan dariya Vice president yayi irin na mugunta wanda yayi fitting fuskanshi irin sosai bayan kaman 2mins yana dariyan seyace "Ku bari se cikin dare amma a yau din nan ku daukominshi amma ku tabbatar kun taho da video da yayi kun gane koh? Guest house dina zaku kaishi babu wanda yasan nawane da sassafe zanzo i will be the one to kill him.with my own hands daga yau babu wanda se sake ma wani labe idan yana zance" "Hakam yayi ranka ya dade. Ya maganan President din kuma?" "Wanan zancen ku barshi se an gama da useless yaron nan semuyi focusing a kanshi" Senate president ne ke maganan nan "Nifa ina tunani kaman akwai abunda gayen nan ya kama ace wai wannan fa na hudu kenan muna kokarin aikashi amma yaki aikowa a gaskiya wannan karan a samu yadda baze kubuta ba idan son samune hadda family shi ya aikaso can baki daya d wannan jarababiyar yar tashi ni dazan samuma kafin a aikashi ya aura min ita dan shegiyn ba karamin kyau gareta ba kuma kudi gareta fa" He added Dariya Vice yayi "Hakane fa kuma zaka samu kudi dan ba karamin gado zata samu ba yar iskan amma kaima kasan baze yuwu ba dan yadda His Excellency keji da yarinyan nan kaman kwai mara bawo" "Hmm bari kawai amma harna hangoni da ita ba" Tafawa suka sakeyi suna dariya "Zaka dauka sabon jini. Dove(sunan daya daga cikin gayun ne amma asalin sunanshi Muhammad) yanzin i will be expecting your call dan Allah kar ayi kuskure ka gane koh?" "Insha Allah sir. Karka samu damuwa, Eagle taho muje"(sunan dayan kenan shi koma asalin sunanshi Abubakar amma dan iskanci sun chanja sunansu zuwa birds Lol) Fita sukayi suna planning yadda zasu shiga gidan a yau din nan Vice presisent da Senate President kowa tafawa sukayi sannan Vice yace "Kaga abu yazo mana da sauki gobe kawai mu hadu a guest house dina by 10am" "Insha Allah ni maybe acan 9 zemin" Dariya dukayi aka sake kashewa (ALLAH SA MU GANE) *** Marwan kowa ya dade yana bacci a wajan itama Mammi se gyan-gyade take akan kujeran da take harta fara bacci ta daura kanta kan kirjinshi Abbah kowa dakinshi ya koma tunani baja-baja akan nan nashi ya rasa ta yadda ze bullu ma alamarin gashi danshi yana cikin damuwa sosai and yasan idan yayi releasing video za'a kama Vice President amma suma fa bazasu tsira ba cus he is 100% sure he is gonna hunt them down Haka shima har bacci yayi awon gaba dashi Manal kowa tayi kuka harta gaji (Baki fara kuka ba babe) Seta kunna T.v dakinta tana kallon Screen Queens. Wajajan 2pm Marwa ya bude ido tareda karanto addu'an tashi daga bacci Kafin yakai karshe se yaji alaman kan mutum a kirjinshi yana gama karantawa ya bude ido sosai seyaga Mammi a kirjinshi murmushi yayi seya kuma ya kwanta yana kallon ceiling yana kokarin tuno meyasa yake bacci a parlo a hankali abunda ta faru ya fara zuwa mashibl har mafarkin da yayi ayatul kursiyu ya kara karantowa sannan ya karanta addu'oin kariya A hankali yace "Mammi are you awake?" Kaman jira take seta bude ido da sauri "Marwan baby how are you feeling?" Ta tambayeshi tana taba tempreture jikinshi "C'mon Mammi it was just a bad dream." Ya gayan mata yana wani murmushi which am pretty sure is totally fake "The worst bad dream" He added yana kallon ceiling "Marwan tell me mafarkin me kayi?" "Mammi it was nothing abeg" "Marwan look at me" "Mammi please not now please" "I know what you are going through so tell me mafarkin me kayi" She said in a serious tone "No no you have no idea what am going through so please leave me alone please" ya gaya yana mikewa Jawo hannunshi tayi ta maidashi ya zauna "Dawo ka zauna Abbah told us everthing that happened so Marwan my son tell me what's the dream about please" ta karashe maganan kama zatayi kuka "Everything?" He asked "Yes everything" Ajiyan zuciya yayi sannan ya bata labarin mafarkin da yayi da kuma kasa baccin da yayi jiya Ta tausaya mai matuka haka ta ringa kwantar mashi da hankali daga baya ta mike danyin azahar "Taso kayi sallah ni kuma barin daura lunch" Daga mata kai kawai yayi ya nufa dakinshi Itama nata dakin ta nufa tayi sallah sannan ta shiga dakin Abbah sallah ta sameshi yanayi dan yanxin ya tashi shima Saukowa kitchen tayi ta daura lunch din Marwan kam daya shiga dakinshi shower ya sakan mankanshi ya kusan 40mins yana abu daya daga bisani ya kashe ya fito bayan yayi brush kenan ya dauro alwala jallabiya ya saka Sallah yayi ya dade yana masu addu'oi baki daya daga baya ya tashi ya shafa mai yayi brushing gashin shi ya shafa mai se sheki yakeyi sannan ya sauko kasa Anan ya samu Manal tana gera plates alaman yanxin aka sauke lunch kenan kallonshi ta tsaya yi Duk suka juyo suna kallonshi karasowa wajan yayi yace "Yane anga dan beauty anata kallonshi" Dariya Manal tayi tace "Beauty my foot" "A yar bukulu. Mammi me akayi ne?" Ya kuma kaman bashi bane keda damuwa dazin hakan ba karamin kwantar masu da hankali yayi ba "Your favorite" ta amsa mai tana wani murmushi wanda ya bayyana hakurin Makkah tah "Cocunut rice?" He asked in an excitement "Nope" "Waina?" "Nope" "Yam balls?" "Nop" "Fate?" "Noh" "Is it tuwo" "Guess again" "Shinkafa?"(god wai yana cikin favorite nashi) "Nah" "Pancake din hausawa?"(kunsan meshi? Kalallaba A.K.A Wainar flower๐น) "Yes!!" Ta gaya da karfi irin ya cinka din nan Tsalle yayi kaman yaro sannan ya karaso a guje yana jan kujera "Zanso inga sanda wani ze girma wai wainar flower shine favorite nashi" Manal ta gaya tana neman tsokanan shi "Help me ask" Abbah ya tayata "Jealous much?" Mammi ta tambayeshi "Yawwa that's my tsohuwa" ya gaya yana kallonta Begeshi tayi tana dariya shima dariya yakeyi Mikewa tayi ta zuba mashi a plate tareda egg sauce se lashe baki yakeyi Su kuma dan-wake sukaci abunsu ana cin abincin nan se tsokanan juna sukeyi shida Manal "Mehn you guyx missed alot" Marwan ya fadi yana lashe hannu "Gross" Manal tace tana yamutse fuska Shareta yayi yana cewa "Barin kira Faisal yazo muje mu buga ball" "Meyasa bazakayi a gida ba?" Mammi tayi saurin tambayanshi "God Mammi!!! Taya zan zauna a gida nayi football ni kadai kina maidani kaman yaro wlh" "Muba mutane bane?" Dariya yayi yace "Ambulance are busy yanxin" Bigeshi Abbah yayi yace"meka maidamu tsofaffi kome? Muma fa munyi yayin football" Dariya Manal da Marwan suka saki "Aww baku yarda ba? Yanxin idan zamuyi cinku zamuyi nida Mammi" "Ohh. Hell yeah" Mammi ta fadi se suka tafa da Abbah Hakan suka ringa musu har daga baya akace aje a buga kowa ya saka riga da wando Marwan yana ganin Mammi da wando seya fashe da dariya wai kalla tsohowa da wando (ko 40 fa Mammi bata kaiba amma duk ya rainata kuma ba kiba gareta ba) Zama a kanshi tayi ta ringa jubganshi shi kowa se dariya yake mata Haka suka fara ball din nan Manal da Marwan se Abbah da Mammi idan Marwan ya kalla Mammi da Abbah seya fashe da dariya haka akayi rabin kwallon nan da dariya Sun kusan 1hrs daga baya kowa yaci 1-1 haka su Abbah suka gudu daki se huci sukeyi wanka sukayi daga nan bacci ya daukesu Manal kowa seda suka gama selfie da Marwan sannan sukayi wanka suma(Never do they know that was there last happy moment together with there parent as in all the family) Parlo Marwan ya dawo yana kallo abinshi hankali kwance duk ya manta abunda ya sameshi jiya amma gabanshi se fadi yakeyi --Karfe 12am na dare-- The M family were all sleeping hadda Marwan kowa bacci yakeyi Dove da Eagle suke iso gidan. (Ohh noh) ๐๐๐






0 comments:
Post a Comment