Tuesday, 15 August 2017
Home »
» RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 14 Gudu yake police din na ganin haka yayi wulli da donut din hannunshi ya ciro bundiganshi ya kwallama partnershi kira ya fara bin Marwan Waigawa Marwan yayi yaga dukkunsu ukun suna binshi ga daya a cikin police din yana pointing mai bindiga. Gudu kawai yayi duk ihun da suke mai ya tsaya kosu harbeshi be sakashi tsayawa ba. Daga nesa ya hango Manal zaune a bench dinda yace ta zauna da ledoji a gefanta sannan ta saya wani dan karamin veil ta saka a kanta batama ganshi ba dan tana kallon gefe can ne. Harya bude baki ze kwalla mata kira seyaga wani mutum yayi parking din motanshi kofan a bude yana deban kaya a cikin trunk din. Kafin kace me ya isa gun motan ya shige tareda kulle kofan ya fizga motan yabar mutum da kaya a hannunshi, sakin kayan yayi ya fara ihu yana binshi shime Gudu Marwan keyi sosai a cikin 406 din nan jikinshi kyarma yakeyi Isowa gun Manal yayi ya tsaya ya bude mata kofan da sauri "Get in!!" Ya gayan mata da karfi Kallonshi tayi ta bude baki zatayi magana seta ga mutanen dake bin bayanshi har uku Rungumo ledojin tayi guda biyu ta tashi da sauri ta shiga motan batama kulle kofan ba ya fuzga motan ya ringa gudu kawai se jin harbin bindiga sukayi ya tarwatsa glass din baya Ihu ta sake tana rike da kunnenta ta toshe da hannunta biyu kanta a durkushe "Durkusa a kasa" Marwan ya gaya yana danne mata kai, haka ta durkusa a wajan tana kuka jikinta kowa kaman tana cikin kankara se rawa yakeyi dan tsaban tsoro wai abunda take gani a T.v yaushi yake faruwa dasu Se harba bindigan sukeyi duk sun cire side mirrors din da glass din baya tuni ya fashe. Sunyi nisa har sun dena ganin mutanan sannan ya rage speed din motan ya kalla Manal duk ta gama tsurewa "Manal" ya kira sunanta a hankali se yaji shiru "Manal!" Wannan karan da karfi ya kirata still no answer. A inda yake yaja burki ya tsaya. Tabata yayi kawai seta biyo hannunshi alaman ta sume. Saketa yayi ya fito a gigice ya bude kofan da take daurata yayi kan kujeran ya kwantar da kujeran seya fara duba jikinta ko an sameta ne amma bega jini ba ajiyan zuciya yayi seya bude ledan data shigo dashi ya ringa tarwatsar da kayan ciki sega ruwan sanyi na gora ya fito dashi budewa yayi ya yayyafa mata Seda ta sauke ajiyan zuciya sannan ya bude ido tana kallonshi seta fashe da kuka. Shafa gefan fuskanta yayi yace "It's okeyy mun wuce su" "Ya'Marwan mu haka rayuwan mu ze kasance what did we did to deserve this? Yanxin wata kila Abbah sun koma ga mahaliccin mu and Vice president yace kayi kisan kai na tabbata yanxin kowa nemanka yake, neman mu. Me mukayi? Me mukayi da akeson rabamu? Bayan rabamun da yayi yanason yaga bayanmu. Ya Allah ka dauka raina nima dan nabi iyayena Ya Allah am freaking tired of this(you hv'nt seen anything yet swthrt) Ya' Marwan meze hana mu saki video yanxin muce kuma iyayenmu suna hanunshi. Dan Allah a saki video Ya'Marwan" seta cigaba da kukanta Shiru yayi yana kallonta na kusan 10mins sannan ya rike mata hannu "Manal" ya kira sunnanta in a peaceful manner. Kallonshi tayi amma bata amsa ba se shan majina take "Remember i made a promise to Abbah that bazan saki video ba yanxin? I made that promise to him and no matter what i most full fill it, you have no idea what am going through but let me promise you this if the right time comes wlh am going to avenge for what they did to us harse da bakinshi ya rokeni and no matter what am promising you this bazasu taba maki komai ba am gonna protect you. Your big bro is gonna protect his little baby sister and zamuyi yadda su Abbah sukace zamuje mu cigaba da karatun mu insha Allah but before then we have to face whatever is coming to us, before then we have to be strong by god grace we are still going to be one big happy family once more that is if everything is over. So promise me this, promise me you are gonna stay strong cus everthing that is happing right now jarabawace daga Allah so we have to be strong to pass it. Promise me" Ya karashe maganan yana rike fuskanta da hannunshi biyu a lokacin hawaye ne kawai yake zubu mata shima idon ya cika da hawaye kuma yayi jajir "I promise" ta fada atlast then ta sake fashewa da kuka Huging nata yayi very tight se shima ya fara hawaye He want to be strong for her but he knows he can't make it, he can't take it. Allah kadai yasan yadda yakeji a zuciyanshi ji yake kaman a yanxin yayi hunting Vice President down cus he is the cause of all this shine sanadin abunda ke faruwa dasu right now. Sun dan dade a haka daga baya they pulled back "So can we keep going?" Ya tambayeta yana kokarin saka smile a face nashi amma ya kasa cus he knows cute smile nashi is forever gone Nodding mashi kawai tayi harya mike setayi saurin cewa "Wait" tsayawa yayi yana kallonta "Ina ka sama motan nan?" Kallon motan yayi se'a lokacin yaga wacce motace "Long story" kawai yace mata ya wuce ya zagaya ya zauna a drivers sit. Ita kowa ledan data shigo dashi ta bude ta ciro cup cakes din ciki guda biyu ta mikama Marwan wanda se yanxin yaji yanajin yunwa Amsa kawai yayi ya ajiye a gefan sit din ya tada motan suka fara tafiya Manal kan cin Cup cake din take kaman wanda ta shekara bataga abinci ba se turawa take tana kurawa da ruwa shi kowa se kallonta yake ta mirror gaba wanda yayi setinshi daidai ita. Tausayinta ne kawai ya kamashi. Yana kallonta taci Cup cake dinnan har guda hudu sannan tayi ajiyan zuciya. Shi kowa ruwa ya dauka ya sanye baki daya yana driving ajiye goran da zeyi se yaga waya akan Dash-Board din motan da sauri yakai hannu ya dauka Wayan Samsung ce yana dubawa yaga akwai kudi a ciki besan sanda yaja motan ya tsaya ba kallonshi Manal tayi. Dialing number Abbah ya farayi it was not reachable yayi na Mammi a kashe Manal data gane me yakeyi se tace "Ka gwada kiran naka ba yana hannun Abbah ba?" Be mata magana ba yayi dialing numbershi ya saka a speaker yana ringing. *** Vice President ne akan Mammi yana tsaye yana tambayenta ta gayan mai inda yaranta suke tayi shiru tana kallonshi kawai Daga hannu yayi ya kalla mata wani mari amma still bata kulashi ba "Why won't you face me and not her!" Abbah ya fada daga can gefe a tsawace yana kokarin cire kachan hannunshi Juyowa yayi yana murmushi ya iso wajan shi "Haka kace koh?" Ya tambayeshi with a wired smirk on his wicked face "Dove,Eagle!" Ya kwallamasu kira Su da suke bakin kofan suka amsa "Yes Boss" sannan suka shigo "Ku daga min wannan trash din" yayi magana yana pointing Abbah. Zuwa sukayi suka dagashi ya tsaya a tsaye shi kowa kokarin kwacewa yake amma ya kasa Vice president tuxedo shi ya cire ya nannade hannun rigan "Face me like a man huh?" kawai ya kaimai punch a ciki kafin ace me ya sake aika mai da wani "Kanada yaro kanada mata" Mammi ta katseshi yana kokarin kaimai na ukun. Tsayawa yayi amma be juyo ba "Why are you doing this? Saboda son duniya? Barin tuna maka idan ka manta zaka mutu kuma duk wannan abunda kake kokarin tarawa duk zaka tafi ka barshi a duniyan ba tare zaka tafi dasu ba. Kanada iyali idan sune ake masu wannan abun how would you feel? If you were in our shoes how would you feel? Duk abun nan saboda video da Marwan ya dauka and yana wajan ka, gamu ma a wajan ka why won't you just kill us and get over it? Kill me and leave my family the hell alone. Mr President is doing his best to see change in the country what did he done wrong da kuke kokarin kasheshi? Saboda kawai kudin da akace akwai a kasa? You are better than this i know i don't know you that well but you are better than this karka bar shaitan yaci ganaba akanka karka bar duk tarbiyan da iyayen ka suka dauraka akai ya tashi a banza akan son abunda zaka tafi kaima ka barshi. Am begging you let my family go, let my kids have a good future kaman inda kakeson yaronka ya sama. You already have what you want what else do you need?" "Your son!" Ya fara da karfi finally yana juyowa yayo gunta "I want to kill your son with my two hands dan nan gaba ko'a a lahira bazeyi labe ba. I won't stop till i hunt him down and then na dawo kanku na kasheku cus you guyx know my secret and let me warn you never mention my parent again" Ya karasa magana yana pointing mata finger "Why won't i mention them? Cus you know they will be disappointed on you? Am begging you kayi amfani da abunda ka karanta kai bakada imani ne ko yaya a zuciyanka?" "Na gasa na cinye. and barin fadan maki duk abunda zakice ko meye shi will never change my plans on your family cus i won't stop senaga gawanku baki daya am telling you sena gansu sannan zan dena se nayi focusing akan mayen President dinku" Yana kaiwa nan ya fice abinshi kafin yakai kofan se wayan aljihunshi ya fara ringing Jan burki yayi ya tsaya sannan ya ciro wayan se yaga wayan Marwan ne da mamaki ya daga kai ya kallesu na kusan 3secs daga baya ya daga call din amma beyi magana ba "Abbah. Kaine?" Marwan asked in an excitment Kallonsu ya karayi seya ciro wayan a kunnenshi ya saka a speaker "Marwan?" ya kira sunanshi alaman tambaya Dumm! Kirgin Marwan ya buga ya daga kai ya kalla Manal data zare idonta waje "Marwan bazaka amsani ba? Na tabbata kanajina..." Mammi najin haka se wani kukan dadi yazo mata dan ta cire hope suna raye da karfi tace "Marwan Baby karkazo komeze ce maka! Karka kuskura kazo.." "Shut the f*cking up!" Ya gayan mata a tsawace "Marwan we love you guyx so much take care of your sister..!" Ta sake fada da karfi Daga bayan hannunshi yayi ya kwasa mata mari "i said shut up" Ihu kawai ta saki amma be hanata shiru ba "Mammi! Mammi!!" Suka fara kiran sunanta da sukaji ihunta "Baby am here karku kuskura kuzo!" Tsaki Vice president yaja ya fice "Marwan i know you are hearing me so listen carefully. Iyayenka suna hannuna both babanka da mamanka if you want them back and be a family once more you have to come here and bring me the other video and am gonna let you go all of you." "Meyasa kake haka? It's my mistake why will you include my parent on it? And Video yana cikin wayana what else do you want?" Wani dariyan mugunta ya sake se yace "Karku maidani yaro mana i know you most have copyed it somewhere else so if you really do love your parent bring the damn video in 24hrs or else am going to kill your precious Mother and i promise to send you a video on how i turtored her before i kill her. Tomorrow by the trains at 2pm come with your sister. And mind you i have people watching you every move naka idan bakazo ba zasu kawo min kai" Ding! Call din ya yanke. "Mun shiga uku! Mun shiga uku!! Ya'Marwan kazo yanxin mu kai mashi please. Kaji muryan Mammi she needs our help Ya'Marwan am begging you please for the sake of our family ka kaimashi Video..." Ta gayabtaba wani kuka "Shut up and lemme think!" Ya daka mata tsawa in an annoyyance "Keda kunnenki kinji muryan Mammi. Kinji da kunnenki abunda take cewa! Baki tunanin it's a set up? baki.." "I don't care what the f*ck it is!" Ta katseshi a tsawace "I just want my family back" She added dispirately "I don't care no matter what it takes i want my parent my life is useless without them. Me zanyi da yaruwa babusu? Babu iyayena. So idan kai bazaka kaiba i don't care am gonna find help and am going to take the Video to them. MYSELF i don't need you nomore am tired of things your way. I love my parent i don't care what am gonna get myself into" Ta karashe maganan a hankali "Manal am not doing this because i don't love them no! You were there when i made the promise to them. Manal mu bari when the right time comes se mu saki video. Kin ji abunda Mami ke cewa da kunnenki so am sorry but am not going to take the video to them" *** Kwance Ummu ke a jikin hannun Abbu wanda har'a yanxin be tashi ba, idonta biyu tana kallonshi kawai tana hawaye ita this time around she wants him to give up and ya sauka kawai daga kan mulkin ta gaji ta gaji. Anata abu daya ga wancan da yayi masu aikin anyi bincike an rasa wanda ya kasheshi and tasan dalilin kisan da aka mashi. Ji tayi computer da ake mashi using nashi yayi wani kara wanda bashi ta saba ji ba. Mikewa zaune tayi da sauri ta kalleshi kawai se taga ya motsa. Tabashi tayi kawai seya fara wani motsi da saurin kaman irin an saka mashi shocking kaman ze mutu Jijigashi ta farayi tana kiran sunanshi da karfi amma hakan be dakashi jinta ba. Batasan sanda ta saka kafa ta fice a guje ba tayi waje. Guards din dake bakin kofan guda hudu suka tsaya suna kallonta da mamaki suna tambayan lafiya amma ko sauraransu batayi ba. Wata doctor ta gani a guje ta karasa gunta tana kuka ta riketa "Ki taimaka min help me please ze mutu" ta gaya tana kuka muryanta yana wani rawa Kama hanyan dakin tayi da sauri harda gudu take hadawa. Ummu ma tana binta a baya a guje tana share hawaye. πππ






0 comments:
Post a Comment