Tuesday, 8 August 2017

RASHIN MAHAIFA-CHAPTER 5 Ummu ce ke zaune a dakinta tana waya da Abbu tana bashi labarin yadda sukayi a school yau Shi shiru kawai yayi se daga baya yace "Allah ka shiryan mana wannan baiwar taka" "Amiin" Ummu ta fada "So yaushe zaka dawo?" "Anjima kadan dan yanxin na gama break-fast" "Break-fast?!" Ummu ta tambaya dadan karfi "Yeah. Meyafaru?" "A ina ka sauka nema" ta gefo mashi tambaya "Hotel ofcourse" "Amma sunsan zakazo dama?" "A mana. Why the questions?" "Habah dear! Habah dear! Fisabilillah kasan sau nawa ake kawo maka hari amma baka daddara ba yanxin hadda zama kaci abinci kuma kace sunsan da zuwanka fisabillilah" ta karashe maganan wane zata fashe da kuka Murmushi yayi yace "Honey da wake kareni?" "Allah" ta amsa a sanyaye "Tou insha Allah shize cigaba da kareni. Shi ze cigaba da karemu, kinji?" Daga kai tayi kaman yana gabanta "So calm down. Yanxin ina Meelarh take?" "Tana cikin dakinta tun da muka dawo ko breakfast batayi ba" "Okey yanxin kije ki bata hakuri ta fito ta karya" "What!? Ae baze yuwuba yarinya tayi mistake ae dole a nuna mata tayi and even though it hurts me na ganta a haka baxan bata hakuri ba sede idan ka kawo ka bata bani ba" "Tou shikenan idan na dawi za'a san yadda za'ayi insha Allah" "Tou shikenan Allah cigaba da kare mu daga makiya" "Amiin"ya amsa dakyar danji yake kaman ana murda mai hanjin cikinshi A haka suka cigaba da hiransu amma Abbu shi karfin hali kawai yakeyi maybe seya dan zaga 😹 *** Khameelarh ce kwance a dakinta idonta sun kara manya kuma sunyi jajir wane volcano ga sketch-pad nata a gabanta tanata zane duk ta batashi da hawaye amma dukda hakan bata dena drawing dinda takeyi ba Can taji phone nata na vibirating tana dubawa taga Abbu mayar da wayan tayi ta cigaba da zanenta Seda ya kira na hudu sannan ta daga ta saka a kunnenta amma batayi magana ba "Baby" ya kira sunanta a hankali Shiru tayi bata amsa shi ba "Meelarh are you there?" "Uhm" kawai tace dan tasan tana bude baki tou kuka ne zezo mata "Meelarh are you okeyy?" "Uhmm" "Talk to me abeg" "Abbuu" seta fashe da wani wawan kuka daman abunda take gudu kenan "Meelarh it's okeyy, everthing is alright okeyyy?" "Abbu yaushe zaka dawo" ta fadi dakyar saboda kukan da takeyi "Insha Allah a yau dinnan zan dawo amma probably da yamma" "Come back soon" "Insha Allah" se tayi hanging up --hrs later-- Har'a lokacin Khameelarh na bedroom nata bata fito ba popcorn ne kawai da malt a cikinta Ummu kowa ta gama dinner ta jera akan dinning lokacin 8pm yayi seta kuma dakinta dan tayi alkawari bazata ba Khameelarh hakuri kaman yadda suka saba mata seta san tayi kuskure tukun Kafin takai dakinta se taji wayanta na ringing da sauri ta karasa ta dauka tana dubawa se taga MY KING (wato Abbu see LOVE😹) Smiling tayi sannan ta daga "Hell....."bata karasa ba taji wata murya wanda ta tabbata bana mijinta bane ya katseta da "Mrs lawwan?" "Yes... ss that..'s mee..e" ta fadi duk muryanta na mugun rawa cus yadda taji mutumin kaman ba'a natse yake magana ba "Am so sorry to say yanxin aka tafi da Mr. President saudiyya.." "Saudiyy.. yya!!" Ta maimata da karfi sannan ta cigaba "wh..attt. tt happened.. to..him" ta karasa idonta ya ciko da kwalla "I have no idea. But all i can say is i think yaci wani abune which is probably not good for him am not sure,amma muna wajen kofanshi mukaji yana nunfashi sama-sama muna shigowa muka ganshi yana aman jini" "Jini!! Wait who are you?" "Sunana Musa am one of his guards da mukazo tare" Jikinta rawa kawai yakeyi tama rasa me zatayi, ta rasa me zata tambayeshi, ta rasa inda zata saka kanta. Why does this keep happening to them? Why? Shine abunda take tambayan kanta kuma har'a lokacin phone din yana kunnenta "Hello? Ma'am you still there?" "Yeah. Thanks am hanging up" "My pleasure" Fadawa kan kujera tayi na dakinta tareda ajiye wayan ta gefanta "Ya Allah. Ya Allah ka kareminshi ka dawomin dashi gida lafiya he has people to take care of, he has the whole Nigeria to take care of Allah ka dawo mana dashi kusa damu. How i wish am right next to you, how i wish ina tareda kai. Allah ko waye da wannan aikin cutan ya kuma kanshi, Allah ka kaskantashi" Seta share hawayen dake zubu mata ta mike ta shiga toilet nata alwala ta dauro tana alwala tana share hawaye haka harta gama sannan ta fito Sallah ta ringayi tana ma mijinta addu'a tana kuka sosai *** Khameelarh ce da wayanta a hannu tana duba latest update na BBC kawai se taga wani video a kasan aka saka "The president of Nigeria was rushed to saudiyya 2hrs ago..." bata gama karantawa ba ta mike zaune tana kunna video Ae kowa gashi aana kokarin sakashi a ambulance kaman beda rai ga jini duk ya bata mashi farar shaddanshi Wani wawan ihu ta saki "Abuu!!!" Ta kira sunanshi da iya karfinta sannan wani banzan kurfi yazo mata, fitowa aguje tayi daga dakinta ta nufa dakin Ummu aguje Akan dadduma ta sameta tanata share hawaye "Ummu kinga abunda ya faru da Abbu?" Ta tambayeta cikin kuka tana daga bakin kofan dakin daga mata kai kawai Ummu ta iyayi idonta harsun kunbyra sunyi jawur ga hancinta shima yayi ja kaman me mura, abunka da farar mace Karasawa cikin dakin tayi ta fada jikin Ummu tareda sakin wani kuka itama a lokacin wani sabon kuka yazo mata haka suka hada kai sunata kuka "Ummu i told him, i told him karyaje, karyaje amma seda yaje.... Ummu dan Allah i beg of you ki fadan mashi ya sauka daga kan mulkin nan. Am begging you wlh a future dina banda plan din zama marainiya(you wish)" ta karasa da kuka Tapping bayanta kawai Ummu keyi tama kasa magana se hawaye takeyi Haka suka kari kukansu daga baya Khameelarh ta mike itama ta dauro alwala suka ringa mashi addu'a suna kaima Allah kukansu SAUDIYYA Dayake a private jet nashi aka kaishi(Lawiza private jet) basu wani dade ba suka isa akayi rushing nashi hospital din ana bashi taimakon gaggawa. Kwance yake kaman gawa danko nunfashi bayayi gashi lokaci daya ya fara ramewa(bawan Allah) --3hrs later-- Bayan kwakkwaran bincike aka gano cewa guba yaci and yanada karfi sosai sannan yana saurin ramar da mutum dan jini yake tsutsewa Wani kwararran Doctor wato Dr. Abubakar Babban doctor a saudiya gabaki daya dan ya kware irin sosai Dr. Abubakar yace yadda za'ayi shine za'a wanke mashi intestine nashi ta inda yaci abun kafin ya zagaye jikin nashi baki daya. But it's under probability ne cus they are 30% sure akan abun cus basu tabayi ba but zasuyi possible best nasu suga sunyi nasara akai A haka suka shiga surgery room dashi rai a hannun Allah aka fara aiki. (Allah ya taimaka) **** "Mammi!! Mammi" Marwan ya fito daga dakinshi aguje yana kiran sunanta "Yane wai kake kirana kama zaka bani abu" ta fadi tana fitowa daga kitchen "Mammi kinsan abunda ya faru ynxin?" "Ya za'ayi na sani ina kitchen?" Mika mata wayanshi yayi sannan yace "Yanxin nan aka tafi da His excellency saudiyya wai yaci gubu" Bata kaiga kallon wayan ba ta sakeshi a kasa ya tarwatse "Innalillahi wai inna'ilaihir raji'un, innalillahi wa inna'ilaihir raji'un" shine kawai abunda take fadi tana ja da baya kaman zata zube a kasa Rikota yayi saurinyi a rude ya ja mata kujeran dining ta zauna sannan ya zuba mata ruwa ya mika mata Kasa amsa tayi cus yadda jikinta ke rawa shim duk ya gama rudewa Abbah ne ya shigo yana ganin halinda ake ciki ya karaso da sauri yana tambayan abunda ya faru "Abbah daga gayan mata abunda ya farune fa kawai shine ta rude haka" Marwan ya fadi kaman zeyi kuka "Meyafaru?" Abbah ya tambaya yana rike da hannunta "Akan fa Mr. President" "Mteww. Kaima kasan yadda take akan His Excellency nasan kuni batamin sonda take mai shine zaka gayan mata?" Ruwa Marwan ya sake mika mata ba tareda ya amsa tambayan Abbah bah. Wannan karan seta amsa ahankali take sha (Ita haka take irin sonda take ma Mr. President she can give away her life for his cus tasan idan babu shi tou suma babu so dan Allah kadai yasan inda zasu kare. Allah de ya cigaba da rufa mana asiri, Amiin) Dagata sukayi aka kaita daki ta kwanta ji take kaman batada lafiya "Wai fisabillillah Miat yaushi zaki chanja? Zaki kashe kanki akan mutumin da besan kinayi ba, na tabbata ko iyalinshi basuyi yadda kikayi ba ae wannan aikin banza ne. Kuma Allah ne ke karemu kuma shize cigaba da karemu" Abbah ne keta zazzaga mata piece of his mind amma ko kulashi batayi ba harya gama yayi ficewarshi Marwan yana parlo duk ya gama rudewa dan idan ta mutu he knows shine sanadi Abbah na fitowa ya shiga da sauri a kwance ya sameta karasawa bakin gadon yayi a hankali sannan ya zauna "Mammi am so sorry na matane wlh" Murmushi kawai tamai "In dauko maki magani" Kafin ta amsa sega Manal ta shigo aguje tana kuka "Mammi, Ya' Marwan!! Mr. President ya mutu" Mikewa Mammi tayi zune tana dafe da kirjinta tana wani nishi sama-sama kaman ze dauke "Ke bakida hn...." Marwan bekai ga karasawa ba Abbah ya shigo ji kake kawwwww!!! Ya kwadawa Manal mari ta gefan fuska "Ko bakuda hankali ne? So kuke ku kasheta ko mene? Tou duk dan da ya sake maganan His Excellency anan gidan wlh zega bacin raina plus be mutu ba" Ya karasa yana kallon Mammi dan inda ta sake rudewa Karasawa yayi gunta ya mika mata wani tablet guda biyu da ruwa a glass cup ba musu ta amsa tasha Marwan ya mike yaja hannun Manal wanda har'a lokacin take tsaye tana hawaye Suna fita ta fashe da kuka "Ya' Marwan me nayi? Kawai daga fadan maku abunda ya faru shine nayi laifi?" Ta karashe tana kuka sosai Beyi mata magana ba seda suka isa bakin dining sannan yaja mata kujera ta zauna sannan ya durkusa ya deba wayanshi da Mammi ta tarwatsar kana ya kalla Manal Bata labarin abunda ya faru yayi sannan ya karasa da cewa "Jin gayen nan take kaman kanin babanta wlh" Murmushi Manal kawai tayi Hannu ya daga ya share mata hawayen dake idonta yace "Taso ki rakani Mool Abbah ya ban kudin" "Habah? Nawa ya baka?" "35k ofcoure" "Kwatt nima barinje ya ban nawa kason" "Chab so kike ya kara maki mari ta daya gefan hala" Shiru tayi idonta yayi rau-rau "Tasu zan baki 5k a ciki idan kinaso?" "A mana inso. Waiitt, kowa fa kulle shagonshi yakeyi rumos akeyi wai ya mutu kaga inda ake kuka mata da maza a cikin gari? chabb" "Ohh Allah. Allah ka bashi lafiya" "Amiin" ta amsa dashi --3days later-- An gama aiki and it was a huge succes ya dawo da kibanshi kaman bashi yayi ciwo ba Dr. Abubakar kowa ya sama rewards sosai Abbu ya kira family shi ya gayan masu ya sama sauki baze dade ba ze dawo cus seya zauna ya ringa amsan magunguna Sunyi murna sannan sunyi kuka sosai which am not sure na dadi ne ko na menene i have no idea Mammi kowa da taga video da Mr. President yayi da kanshi akan cewa ya sama lafiya koma yana ma mutane gidiya da sashi a addu'an da sukayi Tayi rawa harta gaji dan dadi. abun ma dariya ya fara ba Abbah --2weeks later-- Ummu da Khameelarh suna parlo suna kallo (an shirya😹) se Khameelarh takai Aljazeera Ummu ta kalleta "Meelarh yaushe kika fara kolon News?" Murmushi tayi sannan ta bude baki zatayi magana kawai se taga Abbu ya sauko daga jirgi Wani ihu ta saki tana tsalle a parlo Ummu itama murna ta farayi dan duk basusan yauze dawo ba Tafiya yake cikin takama se murmushi yake ga camera ta ko'ina se gaisawa dashi ake ana mai sannu da zuwa ga haske daya kara ga kuma wani tunbi da yayi Seda Ummu tayi hawaye dan dadi Sannan suka durkusa a wajan nan suna ma Allah godiya Sun dade sosai sanna sukaji a News din ana cewa "His Excellency President Lawwan Abdul-kareem just came back from Saudiyya and he's surgery was a success so he's gonna go back to he's family today" Rungume juna sukayi dan dadi sannan Ummu ta wuce kitchen san daurawa King nata abinci duk dadi ya gama cinyeta Khameelarh kowa se rawa take sha --2hrs later-- Gari ya hargitse anata murnan dawowan President ta ko wannan gefe na garin Wani me kudi shanu biyu ya fito dashi ya gasa aka rabawa mutane Abbu na sauka a gidanshi dayan rakiya Ummu har waje suka biyoshi suka rungumeshi dan dadi a tare kuma suka fashe da kuka Murmushi karfin hali yayi yace "Tou mena kuka Allah zamuma godiya gani na dawo lafiyana lau murna ya kamata muyi ae" Rungume juna sukayi Khameelarh se kuka take Yan rakiya se video ake masu akeyi ana posting online Shiga cikin gidan sukayi dukka cikin guest parlo ga wani katon dining wanda ze dauka mutane 50 an cika da abinci kala-kala Zama kowa yayi dan mutanen zasuyi 20 Abbu suka shiga ciki da iyalenshi Tsalle Meelarh ta sakeyi ta rungumeshi Wanka yayi ya fito da wata blue shadda yayi kyau sosai Ummu itana ta shiya cikin wata maroon atanfa tayi daurinta kaman budurwa tayi kwalliyanta sannan ta yafa wata babban veil a kanta Khameelarh itama Maroon atanfa ta saka wanda style din yayi fitting nata sosai tayi heavy makeup abunta ga dankwalin nan anci lokaci wajan daurawa Haka ta fito babu veil cus jikinta duk a kulle yake se selfie sukeyi wai ta sama na posting su kuwa suka biye mata suka ringa dauka har suka gaji sukayi wucewarsu.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Contact Form

Name

Email *

Message *