Tuesday, 15 August 2017

RASHIN MAHAIFA- CHAPTER 11 Dede kunnenshi yace "Take care of yourself" ya riko hannunshi ya saka mai wani silver gun Sakinshi Marwan yayi yana kokarin kallon me ya saka mai kawai seyaga bindiga jikinshi ya fara rawa kaman wanda ke cikin ice tana kokarin sakin bindigan Abbah ya daura hannunshi akan na Marwan sannan yace "Ka kwantar da hankalinka. This gun is for protection i want you to have it take care of yourself" Dagowa yayi ya ciro wayanshi ya mika ma Marwan "Keep this" amma har'a lokacin wayan Marwan yana hannun Abbah Kallon Manal yayi wanda ta kwantar sa kanta a jikin Mammi sunata kuka yace "You guyx have to go now before is too late" yadda yayi magana kowa idan ya kalleshi yasan karfin hali kawai yakeyi dan muryanshi har wani rawa yakeyi Manal ce tazo ta rungumeshi tareda sakin wani sabon kuka "Abbah you guyx don't have to do this dan Allah kuyi hakuri karku tafi ku barmu. Karku barmu mu kadai Abbah bazamu iya rayuwa babu ko ba and you guyx know that we can use the video against them they can't hurt us. Mammi please kiyi mai magana karku tafi ku barmu mu kadai" Ta karashe maganan tana kuma sakin wani kuka, tuni har idon Abbah ya kuma ja cus kukan mata na mugun karya mai zuciya Dagota yayi daga jikinshi yana dakewa kuma yana kawarda fuskanshi gefe guda "Marwan kubi ta kofan kusada basement na tabbata su biyu ne kawai don't let them catch you" Ya kalla Mammi wanda se kuka take ya riko mata hannu Marwan kam duk ya gana karaya dayaga de da gaske tafiya zasuyi su barsu seya saki kukanshi a lokacin yana riko hannun Manal wanda ke ihu sosai Abbah da Mammi suka sauko kasa zuwa parlon har'a lokacin gayun na kokarin bude kofan Su Marwan suma suka sauko Abbah ya juyo ya kallesu yaga sun nufa hanyan da zasu fita ita kowa Mammi tama kasa kallonsu se kuka take a hankali tana rike da hannun Abbah Seda Marwan sukayi nisa dan suna dabda basement din seya juyo yace "Abbah, Mammi" a hankali. a tare suka kalleshi "I promise" kawai yace ya juya yaja hannun Manal wanda daga ita se duguwan riga da dankwali akanta Takalma suka saka irin wanda ake ajiyewa a bakin kofa suka bude karamar kofan daze fitar dasu ta baya Manal ta kallesu batayi magana ba ta share hawayenta ta fara fita se Marwan ya fito shima Kafin su tafi suka sake kallon Mahaifansu a tare suka daga ma juna hannu se suka wuce Fashewa Mammi ta sakeyi da kuka ta durkusa a wajan kaman ranta ze fita Abbah ya dagota ya zaunar da ita akan couch sannan yace "Am begging you badan niba for the sake of your children kibisu please" "No!! No!! I have made my decision" Ta karashe maganan tana goge hawayenta tana wani ajiyan zuciya abun tausayi (Is not easy to loose both your children in one day likewise your parent.) Zama sukayi sosai akan kujeran bayan Abbah ya kunna T.v parlon Mammi na jikinshi se ajiyan zuciya sukayi dukka su biyun Su Marwan kowa suna zuwa bakin bangon gidan ta baya ya saka ma Manal hannunshi ta taka ta dane bangon seta dira ta waje "Are you okey?" Ta tambayeta "Sure" ta amsa mashi. Wulla mata jakan bayanshi yayi Sannan ya matsa baya a guje ya dawo ya dane bangon seya dira Jakan ya dauka ya goya ya rike mata hannu suka fara gudu a daren nan Allah ya taimakesu akwai security light na gidansu so yana dan haska wajan cus ta bayan gidansu suka fita so dajine wajan. Gudu suke sosai seda sukayi nisa sosai sannan Manal ta tsaya tana maida numfashi shima tsayawa yayi "Ya'Marwan mu kira sojoji mana tunda yanxin bamu gidan dan Allah karsu masu wani abu kaji?" Beyi magana ba ya ciro wayan da Abbah ya bashi. Se'a lokacin ya lura ashe ba asalin phone dinda Abbah ke using bane a rude ya duba ko akwai sim card amma babu sede M-card din Abbah ne a ciki At that very time ji yayi kaman ya dauke numfashin shi ya mutu Ihu kawai ya saki da karfin gaske yayi wulli da wayan gefe guda Manal wani mugun tsorata tayi shi kowa durkusawa yayi a wajan ya saki kuka cus yasan shine kawai ze taimakeshi a lokacin Kuka yake kaman karamin yaron da aka yaye Manal taje ta rungumeshi itama ta saki kuka riketa yayi sosai shima kaman yan biyun da aka haifesu a tare se suka koma abun tausayi At that time duk kudin da suke dashi a cikin bag-pack din nan is of no use cus basusan ta yadda zasuyi su taimake iyayensu ba balle kansu. Basuda wani gata se Allah a lokacin basuma san ko iyayen sunada rai ba ko an rigada an kashesu A yanxin ne yayi dana sanin zuwa wani beach party cus shine silan duk abunda yake faruwa dasu a yanzin Sun dade rungume da junansu daga bisani suka cigaba da tafiya bayan Manal ta dauko mashi phone din, har lokacin Manal bata dena kuka ba shi kowa se shara hawaye kawai yakeyi cus ga gane idan yana kuka yana karama Manal tsoro "Ya'Marwan let's go back please gara mu mutu tareda su Abbah" "Manal nayima Abbah alkwarin am going to keep you safe so am gonna keep that promise let's keep going" yayi magana da karfin hali Jan hannunta yayi suka cigaba da tafiya tanata kuka. --Khameelarh-- Tana cikin bacci kawai kaman an tasheta seta tashi a furgice ta kunna bed side lamp na dakin ta kalla lokacin 2:35am Mikewa tayi da sauri ta fito daga dakinta ta nufa dakin su Abbu tanata knocking da karfi tana kuma kwalla masu kira "Abbu!! Ummu!!" A firgice suka tashi a tare suka nufo kofan amma Abbu ne ya bude "Meya faru Meelarh?" Turo kai tayi ta shiga dakin ba tareda ta amsa shi ba Ido hudu tayi da Ummu seta sauke ajiyan zuciya "What's wrong swthrt?" Ummu ta tambayeta tana taba temperature jikinta "Ji nayi kaman someone is sick or in trouble. Seda safe" Tayi waje abunta Kallon juna sukayi se Abbu ya girgiza kai kawai suka koma suka kwanta Ita kowa dakinta ta koma ta dade a kwance da taga de ba baccin zatayi ba kawai seta kunna laptop dinta ta fara kallon 'Wish upon' (the best film of the year damn!!) Tanata kallonta hartaji kiran sallah ta mike tayi sallah ta haye gado se bacci ya dauketa *** Da karfi aka bugo kofan kawai seya koma gefe guda A furgice Mammi ta mike se Abbah shima ya tashi Bindiga dukkansu suka ciro suna pointing masu "Ina Marwan yake?!" Eagle ya tambaya yana nunama Abbah bindigan hannunshi "Baya nan" kawai yace "Where is your f*cking son!?"ya maimaita da karfi "I told you baya nan and bazaku taba samunshi ba" Bayan bindigan ya buga ma Abbah a bayan kai kawai ya zube sumamme Salati Mammi ta farayi tana kuka tana ihu duk ita daya "Rufe mana baki!" Dayan ya daka mata tswa. Babu shiri tayi shiru "Ina danki yake?" Ya tambayeta "Nima bansan inda yake ba" tana magana tana kuka tana kokarin rike mijinta. Seya sake daka mata tsawa wani burgicewa tayi dan ba karamin razana tayi ba "Nace maku bansan inda suke ba" "Suke? Su biyu kenan suka fita?" Shiru tayi bata amsa shiba "Magana nake maki koh?" "Am telling you the truth bansan inda suke ba" inda take magana abun tausayi "Eagle jeka ka duba gidan gabadaya" Itade Mammi kuka kawai takeyi Sama ya haura kafa yake sakawa ya buga kofa seya budu seya shiga har toilet da closet seya leka amma babu kowa haka ya gama garara dakunan nan guda hudu be sama kowa ba ya sauko kasa ya leka kitchen,store loko-loko lungu-lungu haka ya garare gidan bega kowa ba. Ya dawo ya tarar har'a lokacin Abbah na sume. Mammi kowa tana gefe se kuka take tana kalon mijinta amma an hanata tabashi "Babu kowa fa a gidan nan" "Ka duba ko ina kowa?" "Ba inda ban duba ba" Kafanshi ya daga ya bugama Mammi a kugunta. Wani irin ihu ta saki dan azaba "Idan baki gayan mana inda suke ba zan harbe kan mijinki wallahi" Shiru tayi bata kulashi ba seda taga yayi pointing bindigan a kan Abbah ready to blow up his brain setayi saurin cewa "Dan Allah kuyi hakuri ni ku kasheni. Habah bakuda imani ne? Kaman ba mutane ba ni ku kasheni amma ku sani idan har kuka kashe His Excellency wallahi karshen ku bazeyi kyau ba dan bawan Allah nan babu abunda ya maku.." Badan ta shirya ba tayi shiru saboda bindigan da suka buga mata a kai itama ta sume. "Yanxin ya za'ayi wai? Kasan munyi ma boss alkawarin yau zamu kaishi gidan gobe yana zuwa kawai ya tarar dashi" Eagle ne ke wannan maganan "Why not mu tafi dasu idan mukayi blackmailing din Marwan din dasu na tabbata ze dawo duk inda ya tafi" "Tou amma gidan fa?" "Do i look like i care?" Yayi wucewarshi --20mins later-- Haka suka debesu kaman kayan wanki bayan sun gama satan da zasuyi a gidan. Suka sakasu a bayan motansu suka nufa guest house din Vice A wasu kujerun karfe suka zaunar dasu suka dauresu da igiya akayi taping bakinsu yadda ko sun tashi bazasu iya magana ba. Sun bama juna baya. Su kowa su Eagle kwanciyansu sukayi abunsu hankali kwance. *** Su Marwan gudu kawai sukeyi wanda na tabbata ko wuka za'a saka masu a wuya akace su gaya inda suke bazasu iya ba dan wajan wani mugun duhu ne basu ganin kowa kuma ba'a ganinsu. Yana rike da hannun Manal. Ita kowa a hankali take gudu dan ji take kaman ranta ze fita(what a wired feeling). "We have to keep going" yana gayan haka ya ja hannunta ko taku uku basuyi ba kawai sukaji sun zurma a wani waje more like a big hole Ihu Manal ta kurma basusan lokacin da suka saki hannunsu ba Marwan ya bige kanshi a kan wani katon rock ko 3sec be karayi ba ya dauke wuta Manal kam ba abunda ya faru da ita dan furgicin da tayi ne ta sume itama. --The nxt day-- Wuraren 6:45am su Abbah suka bude ido. Shine ma ya fara budewa salati ya farayi saboda yadda yaji kanshi yake wani sarawa dago hannunshi yakeyi amma yaji be motsawa se yayi saurin bude ido ya ganshi a daure kicin-kicin ya farayi yana kokarin budewa shine ya tayarda Mammi itama Salati ta farayi ita. "Miat!" Abbah ya kira sunanta a furgice cus he never expected ze ganta a wajan "Na'am" seta fashe da kuka Rudewa ya sakeyi gashi babu daman ya kalle fuskanta "Ki kwantar da hankalinki Allah na tare damu and insha Allah bazasu kamasu ba" Shuru tayi batayi magana ba se kukan da takeyi. "Ku wanna irin jahilai ne fisabilillah? How would you let them escape? I've never met an ass holes like you two" Vice ne ke wannan bala'in cus shi ya rigada ya iso amma Senate president be iso ba. Suna zaune ne a parlo suna bashi labarin abunda ya faru "Boss ka kwantar da hankalinka zamu kamusu insha Allah kafin su bar garin nan amma kafin nan gashi" Eagle ke maganan ya mika mashi phone din Marwan Amsa yayi yana kallon wayan da alaman tambaya "A jikin babanshi muka sama so na tabbatar wayan sistershu na hannunta and kaga zamu iya using din iyayensu su kawo kansu" He added Shiru yayi da alaman tunani yakeyi Can se yayi unlocking screen din ya shiga gallery ya shiga camera sega video seda ya kalla sannan ya maida wayan cikin aljihunshi ya kallesu "Wanna daki suke?" Fuskan nan a daure Gayan mashi dakin sukayi ya shiga hadda jawo kofa Abbah ne ya fara ganinshi cus shine me kallon kofa Wani murmushin mugunta Vice ya saki wanda yayi fitting fuskanshi irin sosai "Well! Well!! Well!!! What do we have here?" Wani kallo Abbah kemai irin am so sorry for the woman that gave birth to you Motsowa kusa dashi yayi yana cigaba da murmushi "Ga kaman ni nan kowa" Seya kuma gefan Mammi se kuka take abunta dan idan batayi kuka ba ciwo ne ze kamata "Awwn ki dena kuka idan yaronki yazo da kafanku zaku tafi" Dede fusanta yazo yana mata wannan maganan Miyau ta tofa mai a fuska ba shiri yaja baya yana goge fuskanshi dan ita fuskanta babu komai a bakinta Abbah kawai suka saka ma Saukan mari kawai taji a fuskanta ya kwada mata mari Ae marin nan har'a zuciyan Abbah seda yajishi a zuciye ya mike a kujeran kawai se igiyan ya tsinke na hannunshi furgan dayan ma yayi shima ya tsinke Bare abun bakinshi yayi yayi kan Vice (duk wannan abun a 3secs ta faru) Hadashi yayi da bangon dakin ya shakure mai wuya da dukka hannunshi Fuskanshi harya koma ja a lokaci daya (an taba mai Queen dinshi😹) Su Dove ne suka shigo a guje ihu Mammi ta farayi dan yasan sun shigo amma kafin ya ankara sun buga mai wanu abu ya baje Ihu ta cigaba dayi tana kuka tana kokarin kunce hannunta amma babu hali "Ku sama wani abu me karfi ku daureshi dashi" Vice yayi magana yana maida nunfashi Haka suka daukeshi suka sama wani karfe a dakin a jiki suka daurashi *** Abbu,Ummu da Khameelarh ke kan Dining suna breakfast hankalinsu kwance su abunsu As usual Khameelarh na gefan Abbu sunacin plate daya "Abbu kasa a bani nayi managing traffic light na cikin gari mana na kwana daya" Dagowa sukayi suka kalleta a tare da mamaki dan meyakaita wannan tunanin bayan dukka sana'oin garin nan "Meyasa kikesonyi?" Abbu ya daure ya tambayeta Wani dariyan mugunta ta saki kafin ta gyara zama tace "Inason ko sena tabbatar motoci sunzo from all sides sena tsayar dasu idan sun taru dayawa sena fara video a lokaci daya zan saka GO!! Gabadaya suzo a tare aradu kowa ya mutu" Seta fashe da dariya Kallonta sukeyi duk sun kasa magana na kusan 10mins can se Ummu tace "Meelarh your heart is full of darkness" Kallonta kawai tayi batayi magana ba Abbu ya bude baki zeyi magana kenan kawai seya fara tari kaman ya kware Gabadaya hankalinsu ya kuma kanshi da sauri Ummu ta mika mashi ruwa a glass cup amma ya kasa amsa da sukagane ba na wasa bane se Khameelarh ta mike da sauri tana shafa bayanshi tana dan bubbugawa a hankali Ummu itama tayo kanshi Abu de kaman wasa seda yakai Abbu har kasa se kunfa ya fara fitowa a bakinshi Ko 2secs be karayi ba ya fita daga hayyacinshi ya sume a wajan Tashin hankali da ba'a mata rana Kuka suke baki dayansu suna jijjigashi amma kaman gawa Ihu Khameelarh take tana cewa "Ku kira Ambulance!! Ku kira Ambulance!!" Kawai take cewa Ummu kuwa durkushe kawai take a wajan tana kuka bata iya cewa komai Daya daga cikin maids din gidan ne tayi kokarin kiran Ambulance. πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Share:

5 comments:

  1. antibrowserspy-pro-crack is designing to provide users safe surfing information? The Hex gives the web a gift through their better opportunities to access personal computer systems.
    new crack

    ReplyDelete
  2. I am very thankful for the effort put on by you, to help us, Thank you so much for the post it is very helpful, keep posting such type of Article.
    CyberLink ColorDirector Ultra Crack
    UC Browser Mod APK Crack

    ReplyDelete

Contact Form

Name

Email *

Message *